Sashe 14
Mugun Albishir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
qoqarin tuno wata addu'a ce da ya dade da mancewa, Zubaida ta sake ce mashi a fusace. . "ka yiwa 'yansanda waya su zo ko baka ji ba ne?" . Dan tsohon ya dan murmure yana inda-inda, yayi sauri ya fice daga falon yana mis-mis da baki. Nayi ajiyar xuciya sannan na durquusa kusa da Zubaida, ina kallon gawar Alh.Bashir yana kwance kamar yadda na barshi jiya da dare. Na ce da Zubaida . "ya kamata kina daina kukan haka nan, don kuwa kowanne mai rai mamaci ne, ki daina kukan, addu'a ya kamata ki yi masa.' . Zubaida ta sassauta kukan da take yi, sannan ta kawar da kai cikin damuwa, tana sanya da doguwar rigarta ta daren jiya, amma Kuma a wannan karon ba gyale ta yaro ba, dankwalin rigar ta daura Wanda aka qawata shi da adon wasu dinkakkun furanni a saman goshinta. Ban san me yasa take jin kunyar hada idanu da ni ba." Babu mamaki Kuma me yiwuwa tana zargin ni na zo na kashe shi cikin daren. To koma dai me zata yi tunani aikin gama ya riga ya gama. Shekaru talatin sun zo qarshe. . Ta ce min ba zai mutu ba sai ya qara shekara talatin a duniya, shi ya sa ni Kuma na dan rage yawansu suka qare a cikin dare daya. Don kuwa na qosa in aureta, na qosa ta zama mata ta. . Tsawon lkc muna a durqushe ni da Zubaida mun tana gawar gabanmu, ita Kuma tana shassheqar kuka. Xuwa can sai muka jiyo sautin jiniyar motar 'yansanda ta shigo cikin gidan. Nayi mamaki da naga har ynx Zubaida bata daina kuka ba, sai ka ce tana baqin ciki da mutuwarshi, sai ka ce ba shi ne yake jera mata bulala hamsin ba Kullum a gadon bayanta kafin ta kwanta barci. . 'Yansanda hudu suka shigo cikin falon sanya da baqaqen kaya, Babu alamar wata damuwa a fuskokinsu. Muka jiya muka dube su. A lkc ne na miqe tsaye na basu wuri, suka kalle ni a lkc guda sannan suka mayar da hankalinsu akan gawar Alh.B. Wani a cikinsu ya tambaya. . "muna Fatan dai Babu Wanda ya ta6a gawar a cikin Ku?" . . Lp=22mugun albishir Page 22 . daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . "muna Fatan dai babu Wanda ya ta6a gawar a cikin Ku?" . Zubaida ta girgiza kai tana shassheqar kuk, ni ne samu damar yi musu magana. . "Babu wanda ya ta6a gawar shi, a haka muka same . Wanda ya yi tambaya da farko ya sake cewa. . "shi kenan, kuna iya tafiya, amma kada Kuma yi nisa domin bayan mun gama binciken akwai tambayoyi da zamu yi maku." . Nayi sauri na fice daga falon, don kuwa xufa nake yi, duk iskar safiyar da ake busawa. Na san cewar idan har 'yan sanda suka yi la'akari da yadda na rude, me yiwuwa asirina ya tonu su gane ni na kashe mijin Zubaida . Na fita waje naga tuni gari ya waye. Na hango Falalu mai gadi raku6e a jikin falwayar da ta shigo katafaren gidan inda mai gadi yake zama. . Da gani na ya yi sauri ya tarbeni ni kamar Akwai wata magana da yake so ya sanar da ni. Muka hadu ni dashi har ynxn baiwa daina karma ba, Kuma Akwai alamar hawaye a cikin busassun idanunshi. . "Mansur." . Ya kira suna na. Ban yi tsammanin ya riqe suna na haka ba, don kuwa kwana na biyu kawai a gidan, Kuma tun xuwa na ban fito mun yi hira ba." Me zai sa in fito, tunda dai muna tare a ciki ni da masoyiya ta? . na amsa kiran da ya yi min, na ce dashi. . "Baba sai haquri ka daina kuka, shi dama rai baqon duniya ne, idan lkc ya yi sai tafiya. . Tsohon ya share hawaye ya ce da ni. . "wannan gsky ne mansur, to amma dole ne in yi jima da wannan rasuwa ta alhaji. A ce abu cikin dare daya ba ko ciwon kai ba na qafa.." . Ya sake rikicewa yana qoqarin gyara tsayuwa, don kuwa duk ya birkice, kamar Wanda aka dora shi akan bishiyar macizai. Na ce dashi. . "idan kwana ya qare ko babu ciwo sai an je baba. Sai dai a yi mashi addu'a" . Akwai alamar zargi a xuciyar Tsohon, na gane haka ne da naga ya yi saurin waigawa duk wani 6angare na gidan. Da ya tabbatar Babu Wanda yake saurarenmu sai ya yi qasa-qasa da muryarshi ya ce da ni. . "Mansur ina zargin hajiya. Da wahala idan ba ita ce ta kashe alhaji ba, don kuwa dama ana zarginta ta ta6a yunqurin kashe a lkcn baya. Domin kuwa ta ta6a jefa shi cikin rami a mota, a dalilin haka ne ma ya zama gurgu. Dama can tana son ta kashe shi." . Daqyar na kawar da fushin dake xuciyata, don kuwa Tsohon ya gama qule ni. Bai san irin son da nake yi wa Zubaida ba, shi ya sa yake gulmarta a gaba na, amma don Kada ya yi zargin wani abu sai na ce dashi. . "Babu mamaki Kuma ba ita din ba ce, don kuwa idan kwana ya qare ko ba a kashe mutum ba, shi da kan shi ma zai iya faduwa ko Babu ciwon kai ba na qafa." . Da dan Tsohon ya ji na kare Zubaida sai ya yi gum da bakin sa, yayi shiru yana girgiza kai, muka yi tsaye mu biyu kowa yana tunanin da ya dame shi. Na san shi tunanin mutuwar mai gidan sa yake yi, ni Kuma lissafin kwanakin da Zubaida zata yi kafin ta gama takaba nake yi. . Bayan wani lkc sai na hangi Zubaida ta fito daga cikin gidan ranta a 6ace, ga alama ni take nema. Don kuwa da fitowarta ta tsaya tana dube-dube, da ta hango ni tare da mai gadin a tsaye bakin qofa sai ta yafito nI da hannunta. Na bar dan Tsohon na nufi inda take cikin sauri. Da xuwa na ji ta ce da ni a sanyaye. . "ka shiga ciki. 'yansanda ne suke son ganin ka, ni na gama amsa nawa tambayoyin." . Na dubi Zubaida sosai, tana nan a cikin damuwa, Kuma da alama kamar tana fushi da ni, sai ka ce nayi mata laifi . Sai ka ce ba mijinta kawai na murde wa wuya ya mutu ba." . Na shiga cikin gidan kai tsaye na cire duk wata alama da zata san 'yan sanda su gane bani da gsky a fuskata. Na saki 'yan sanda su hudu a falon suna jira na kamar kuraye sun samu tunkiya. . Sun yi min tambayoyin da ban san iyaka ba." har da tambayar yadda aka yi aka haifeni? To Amma Kuma amsa daya na tsaya mawa. Ni baqo ne a gidan, ban san abin da ya faru ba." na kwanta barci da wuri, Kuma na farka da safe naji matar gidan tana 6uurari waigo mijinta ya mutu. Dole akan haka suka rabu da ni, tunda dai ko maqure ni zasu yi ba zan tonawa kaina asiri ba in ce ni na kashe shi. Na bar su a cikin falon suna gwaje-gwajen su na al'ada, a lkc da na fita waje ne naga wata doguwar farar motar asibiti ta daukar gawa ta shigo gidan. Ta yi fakin , wani likita ya fito dan sirri sanye da farar riga da Kuma farin tabarau, wasu qananan likitoci biyu Kuma suka biyo bayan shi suka fito da wata makarar asibiti ta qarfe. . . a lkcn da na wuce cikin faffadar farfajiyar gidan ne na hango Zubaida a cikin mota daya daga cikin motoci biyar din dake qyalqyali a cikin hasken safiyar. . Zubaida ta tayar da motar, sannan ta tuqo ta cikin sauri, ta zo daidai inda nake tsaye ina kallonta. Ta dube ni sannan ta ce. . "shigo mu tafi." , Na tsaya sororo ina kallonta... . . Lp=23Mugun albishir Page 23 . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak Madugun taska . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . Na tsaya sororo ina kallon ta, ganin bata son ta yi min dogon sharhi sai na fasa tambayarta inda zamu je a daidai wannan lkcn da ake tsaka da bincike a gidan. Na zagaya 6angaren damar na bude motar na shiga baya na zauna, ita Kuma ta tuqa ta nufi qofar shiga da fita ta gidan, wacce ke a bude fayau! Shi kansa mai gadin ya rude, ya mance bai rufe ba." . Zubaida ta fice da mu, muka bar gidan. Ta hau kan titin layin gidan, muka doshi yamma. Bayan mun yi nisa mun daina hangen gidan, sai tayi fakin da motar a bakin titi, a wani waje da ke da qarancin mutane. Har xuwa lkcn ban ce da ita komai ba, ban tambayeta dalilin da yasa ta daukoni muka fito ba, har xuwa lkcn da ta kashe motar ta juyo ta dube ni. To amma Kuma na san cewar wata magana ne mai muhimmanci take son mu yi, wacce take buqatar sirri. . "mansur" . Zubaida ta ambaci Suna na a cikin damuwa da Kuma shiga6a. . "na qura mata ido ban amsa ba, na ci gaba da sauraren abin da take son ta fada min..." . "ina so ne muyi wata magana mansur." . Ta ce da ni. . "ina so ne ka fada min gsky bana son ka yi min qarya. Me ka sani a game da rasuwar mijina?" . Ta qarishe maganar a cikin kuka, hawaye ya xubo mata cikin sauri. Ta share hawayen sannan ta tsayar da ganinta a kaina. . "ka yi min magana mansur." . Ta sake cewa da nni cikin damuwa. . "me ka sani game da wannan mutuwar?" . Na yi ajiyar xuciya sannan na ce da ita. . "ni na kashe shi." . Tsawon lkc muna kallon juna Babu wanda ya sake cewa wani abu. Na sake tabbatar mata. . "tabbas ni na kashe mijinki Zubaida. Na san cewar ke kanki kina zargin