← Book details Mugun Albishir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 21

Sashe 11

Mugun Albishir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da na saurara da kyau naji kukan tsuntsaye da tantabaru a cikin daren, sai na fahimci ko shakka babu sune suka zo min a matsayin dararrakun da mutane ke yi min a cikin mafarki. Sannan kuma qaton mayafin da ya taushenni shi ya shiga hana ni in iya motsawa in taka rawa a gaban tsofaffin matan dake buga min amada ba ji ba gani. . Na ji an ci gaba da buga min qofar . . Lp=17Mugun albishir Page 17 . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . Na ji an ci gaba da dukan qofar, nan da nan nayi sauri na ture mayafin dake lulli6e da ni na sauke daga kan gadon, na lalubi makunnin wutar lantarkin dakin dake jikin bango na kunna, haske ya gauraye dakin. Na duba agogon bango naga qarfe daya da minti bakwai na dare. Na ji tsoro ya sake kama ni. Wane ne yake tashi na a cikin wannan uban daren? Na tambayi kaina, a daidai lkcn ne na isa bakin qofar na sa hannu na dafa ta, aka sake bugawa da qarfi. . "wane ne?" . Na tambaya a tsorace. A daidai lkcn ne naji zazzaqar muryarta Zubaida ta keto daga cikin daren ta yada zango a kunnena. . "bude min mansur, ni ce...." . Shiru ban iya motsawa ba da na fahimci ko wace ce...." Me ya kawo Zubaida dakina cikin wannan talatainin daren? . Ta sake bubbuga qofar cikin qosawa ta ce...." . "ya sauri ka bude min mansur, ni ce Zubaida." . Na bushe a jikin qofar ina xullumin budeta. Don kuwa na san in har mijin ta ya san cewar ta xo dakina a cikin wannan uban daren, to babu abin da zai hana shi ya harbeni a washe gari. Dama daxun ya gama gargadina cewar kada ya sake ganin nayi kuka don naga yana dukan matarsa. . To a qalla dai bai gano cewar masoyiya ta ba ce, sai dai Kuma a halin ynx idan ya ji maganarta a dakina abin da zai yi min ya wuce gargadi. . "mansur ka bude min qofar mana, ni ce Zubaida, Kada ka ji tsoro." . Zubaida ta sake rero min muryarta daga can waje, nayi sauri jikina yana tsima sbd razana na bude mata qofar a rikice. A daidai lkcn da qofar ta bude ne, hasken wutar lantarkin dake a cikin dakina ya sauka akan kyakkawar fuskarta, Kuma a lkcn ne ta saki wani tattausan murmushi a lkcn da muka hada ido ta ganni a tsorace kamar an koro zamo daga rami. Tana sanye da doguwar riga mai ruwan ciyawa, ta lullu6a wani qaramin gyale mai shara-shara a saman wadataccen gashin kanta, Wanda ke motsawa kadan a sakamakon wata qaramar iska da ake yi a waje. . Ganin cewar na bushe a tsaye ina kallon ta, sai ta sawo kai ta shigo kai tsaye bata daina murmushi ba, ta ce min..." . "ba ni wuri in shigo, ina ta faman bubbuga maka qofar kana ji na ko mansur?" . Na kauce na bata wuri ban ce da ita komai ba, na bi ta da kallo a lkcn da naga ta za6i wurin zama a gefen gadon da na tashi Babu dadewa. Nayi qarfin halin tambayaRta. . "Zubaida lfy kika zo dakina a cikin wannan daren? Kuma ba kika jin Tsoron kada ya jiyo muryarki kike daga murya kina surutu?" . Ta ce da ni ba tare da ta sake kallon razananniyar fuska ta ba." . "Babu damuwa mansur." . Ban gane manufarta ba." ganin cewar ban saki jiki da ita ba, sai ta dago kai ta sake kallona ta yi min murmushi ta ce...." . "don allah ka saki ranka mansur, ka cika tsoro, sai ka ce ba namiji ba." tun da na ce maka ba matsala. Ya yi barci, ba zai farka ba sai gobe da safe." . Nayi ajiyar xuciya sannan na dan ji sanyi a raina, don kuwa na gama tsorata da wannan mijin nata. Ina kyautata zaton yafi ni son Zubaida dari bisa dari. Ta sake cewa da ni. . "yau tun da wuri ya buge ni mansur, shi yasa yayi barci tun daxun, Kullum sai ya zane ni da bulala. Haka rayuwata take kasancewa, Babu yadda zan yi sai dai haquri." . Na ji tausayinta ya kamani a lkcn da naji tayi wannan maganar, musamman ma da naga tayi shiru tana tunani. na bi ta da kallo tsawon wani lkc, ban san abin da take tunani ba." ni Kuma ban tambayeta ba." xuwa can Kuma sai ta yi ajiyar xuciya ta ce da ni. . "zauna mansur, Akwai maganar da nake son muyi ni da kai, shi yasa Kaga na zo wurinka a daidai wannan lkc. Kada ka zargeni, ba wani abu yasa ka ga naxo dakinka ba." . Na samu wuri a gefen katifar dake kan gadon na zauna, nesa kadan daga inda Zubaida take zaune. To amma Kuma tazarar dake a tsakaninmu bata hana ni shaqar qamshin dake a jikinta ba, Wanda na rasa gane ko qamshin mene ne a tsakanin turare da man shafawa. To amma Kuma ko ma dai mene ne, ni dai ya burgeni. Don kuwa duk ya cika dakin kamar qamshin dakin amarya a qasarmu ta hausa. Na tuno zamanin da ta zo wurina ta zauna. . "....ga alama kaima irina ce...." . Zubaida ta katse min tunanin da na fara ta juyo ta dube ni da fararen idanunta, hannunta daya na dafe da gyalen da ta yafa akanta. Ta ce da ni. . "naxo wajen ka ne akan wata magana da naji mijina ya sanar da kai daxun da safe. Ina raku6e ina jin ku, ina jin duk abubuwan da ya fada maka mansur....na san cewar ynx fahimci kai duk ka amince da wannan sharrin da yayi min ko mansur? ta ci gaba da kallona don jin abin da zan ce...." . Nayi saurin girgiza kaina, da naga bata dauke idanunta akaina ba." . "ko kusa ban amince da wannan labarin ba Zubaida. Don kuwa tun muna makaranta na san cewar ke macece mai kyawawan halaye da mutunci. Ba zai ta6a zama gsky ba ace ke ce ke da irin wannan halin, tun daxun da ya bani labarin ni tunic na mance da maganar, in dai wannan shi ne abin dake damunki kika kwantar da hankalinki, har abada Babu wani mahaluqi da zai tunkare ni da irin wannan mmaganar a game da ke in amince." . Zubaida ta dan saki ranta a lkcn da na kai qarshe. Ban sanin ba ko don ta ji dadi na yabeta shi ya san ta mance ta saki dan figigin mayafin dake lulli6e da kanta. Ta yi sauri ta sake jawo shi ta dora a saman gashinta, Wanda yake ta sheqi a cikin hasken dake dakin aduk lkcn da ta motsa. . "na gode sosai mansur." . Ta ce da ni. . "naji dadi da ban same ka a cikin mutanen da suke dora min zargi akan abin da ban aikata ba." Sau da yawa ina mamakin halin wannan mijin nawa mansur....ba ya kyautata min, baya gani na da mutunci, shi a tunanin sa waigo Kullum kashe shi nake so in yi. To akan me zan kashe mijina ina da hankali mansur? . . Lp=18mugun albishir Page 18 . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . To akan me zan kashe mijina ina da hannkali mansur? Wannan hadarin da ya baka labari, ba laifina ba ne tsautsayi ne....! Amma Kuma ya qi ya gane . Akan haka ne yake min irin wannan cin mutuncin, Kullum sai ya buge ni kafin in kwanta barci. Wai shi ba zai barni in zauna haka ba, tunda dai na jawo mishi ya zama gurgu babu abin da zai iya yi, a Maimakon haka yake yi min bulala hamsin a kowacce rana kafin in yi barci, sbd tsabar zalunci." . Zubaida ta saurara tana qoqarin mayar da numfashi, don kuwa Akwai alamar bata son tuno da al"amarin. Na gane haka ne da naga tana fadin maganar cikin fushi da Kuma sauri. Nayi sauri na kwantar mata da xuciyarta na ce da ita. . "ku yi haquri Zubaida matsalar zaman aure kenan sai haquri. Kin san wasu maxan haka suke yiwa matansu irin wannan wulaqancin da Kuma cin zarafin. Gsky bai kyauta ba, amma Kuma idan baki da alhakinshi wata rana zaki ga sakayya, in allah ya so zaki rabu dashi ki samu wani dan arziqi da sanin ya kamata ki aura." . Na fada mata haka ne don tun ynx in gyara tawa gwamnatin. Ina son in nuna mata kuskurenta ne da ta auri wannan Tsohon mai kudin ta bar yaro dan zamani irina. (amma Kuma talauci kamar 6eran maSallaci). . A cikin sa"a Kuma sai Zubaida tayi tsaki ta ce da ni cikin damuwa. . "na gama tsorata da halin maza mansur.ni ynx Babu wani abu da namiji zai fada min in yardda dashi. Don kuwa na sha wahalar aure ba Sau daya ko sau biyu ba." duk maza haka kuke mansur, halinku daya." . Na ji tsoro ya kama ni na ce da ita . "ba haka ba ne Zubaida. Wlh ba halinmu daya ba." Akwai masu hankali. Ke dai kawai ba ki yi dace bane. Amma ki qara jarraba ko da mutum daya ne ki gani a nan gaba." . Na qura mata ido ina qoqarin karantar abin dake kan fuskarta. To amma Kuma da naga ta fara sakin ranta, sai naji dadi a raina. Don kuwa ina so ne in riqa kushe mijinta don ta yi qoqari su rabu, daga baya Kuma ni in zagaya in aureta. . Ta sake yin ajiyar xuciya, sannan ta yi tagumi tana kallon dardumar dake a malale a tsakar dakin, sannan ta ci gaba da cewa. . "wannan hadarin da ya faru kamar inda ya sanar da kai, ba a fi wata uku ba dayin aurenmu, sai naga cewar ya kamata mu je wani garin kakannina don na gaishesu Kuma su ga mijina. A ranar da zamu
Chapter 11 · 0% Book details