Sashe 17
Mugun Albishir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
. Fursunonin sun bani labarai da dama na surqulle Wanda ya sa suka kauracewa soyayya, to amma Kuma ni duk wannan baiwa tsorata ni ba." ina nan da soyayyarki Zubaida a raina, Kuma ina fatan duk lkcn da na fito daga gidan yari zata zama mata ta...." . Sai dai kuma na fara shan jinin jikina. Don kuwa tun da na zo gidan yarin ko Sau daya Zubaida bata kawo min ziyara ba, sannan Kuma bata aiko min da wani saqo ba, Wanda zai sa in kwantar da hankalina, in san cewar tana nan tana jira na. Kwanci tashi gashi har an yi shekara goma. . Baqin cikin rashin ganin Zubaida masoyiyata, da Kuma tsananinn wahala da muke sha a gidan yarin, ya sa duk na kode na lalace. Nayi baqi wuluk, sannan Kuma gasusuwa sun firfito min a fuska duguzum, na zama abin tsoro a wurin yara qanana da ace zan fito duniyarsu su ganni. . Sau da yawa na kan rabat dare ina kukan baqin ciki idan na tuna cewar duk sbd soyayyar Zubaida na tsinci kaina a wannan wuri. Amma Kuma gashi ko sau daya ba ta zo ta ganni ba." . . Lp=26 Mugun albishir Page 26 . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . Sau da yawa na kan raba dare ina kukan baqin cikI idan na tuna cewar duk sbd soyayyar da nake yiwa Zubaida na tsinci kaina a wannan wuri. Amma Kuma gashi ko sau daya ba ta xo ta ganni ba." to amma babu mamaki Kuma wani abu ne ya faru da ita a lkcn da zan zo gidan yarin. Ban san ynx a wane halin take ba." . Don haka nan take sai naji tausayin Zubaida ya kama ni. Ina xullumin ko wani abu ne ya same ta, gashi Kuma bani a tare da ita ballantana in sake taimakonta. Kullum sai na tuno bankwanan da muka yi a lkcn da aka yanke min hukuncin a kotu. A lkcn da take kallona fuskarta sharkaf da hawaye. . Kafin mu tashi mu fita daga dan tsukukin dakin mai kama da akurkin tantabaru ni da Sauran abokaina biyar sai aka turo qofar dakin ta bude. Wani gandiroban ya shigo, to amma shi ba da bulalar ya shigo ba, ya shigo ne da wata doguwar takarda a hannunshi, da shigowarshi ya ce da mu. . "wane ne mansur a cikin Ku?" . Na ce dashi. . "ni ne....! . Gandiroban ya dube ni cikin farin ciki ya ce. . "to mansur sai ka yi bankwana da abokanka. Yau ne ranar da za a sallameka daga wannan gida. Yau ka cika shekara goma. Yi sauri ka zo mu je ofishin kwantirola." . Na ji farin ciki ya ishi xuciyata. Na dubi abokan kwanana su Bangis da Gambo, na ji tausayinsu ya kama ni, don kuwa su hukuncin daurin rai da rai aka yanke musu. Bangis ya ce da ni. . "mansur shi kenan Kuma zaka tafi ka barmu, Fatan nan gaba zaka kiyaye wajen yin soyayya . Sauran fursunan suka fashe da dariya. . Dumfama ya ce. . "muna Fatan wata rana zaka zo mana da Zubaida don mu ganta." . Nayi masu alqawarin zan zo da ita idan na aureta. Sannan na bi gandiroban muka fice muka bar dakin. Na ji iskar safiya mai sanyaya xuciya ta bugi fuskata sannan Kuma annashuwa da murna suka mamaye min xuciyata. Don kuwa rayuwata ta dawo sabuwa. Lkc ya yi da zan fita in ga Zubaida, na ce a xuciya ta...." gani nan xuwa, ina Fatan baki mance da ni ba." ni ne mansur Tsohon masoyinki, tun na shekaru goma da suka wuce." . . ** . . Lkcn da aka sallame ni na fito daga gidan yari, ban zame ko ina ba sai unguwarsu da nake tsammanin zan ganta. Gidan Alh.Bashir yana nan kamar yadda na bar shi tun shekara goma da suka wuce. Sa6anin wancan lkcn, ynx ba dan tsoho Falalu mai kwari da baka ke gadin qofar gidan ba, a wannan karon wani baqin soja ne a zaune rungume da doguwar bindigarshhi Wanda nake kyautata tsammanin rabonshi da ya yi fara'a, Babu mamaki wataqila tun yana yaro qarami, lkcn da ake Bashir kudin tara. . Na qarisa inda yake nayi mashi sallama, kafin ya amsa sai da ya kalle ni sama da qasa, da ganina ko mutum bai tambaya ba ya san ceewar daga gidan yari na fito. Don kuwa Bayan kodaddun kayana masu kama da ragowar kura, duk jikina tabon duka ne kamar dokin suga. Da yaga na tsaya a gabnshi ina nemo abin da yafi dacewa in tambaye shi. Sai shi ya dakatar min tsawa. . "wa ka zo nema?" . Na ce dashi . "na zo neman Zubaida ne.l" . Sojan ya ce da ni. . "Babu wata Zubaida a gidan. Ya ce da ni gidan na wani kanal din soja ne." . nayi mashi gdy, sannan na fice cikin rashin sanin inda zan je on ga Zubaida. A halin ynx na fahimci cewar sayar da gidan aka yi Bayan rasuwar mijinta. . Don haka kai tsaye sai na wuce gidan Kawuna Wanda ya fara yi min hanyar xuwana gidan marigayi mijin Zubaida. . . Lp=27Mugun albishir Page 27 . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . Don haka sai na wuce kai tsaye gidan Kawuna Wanda ya fara yi min hanyar xuwana gidan marigayi mijin Zubaida a matsayin direba. Daga shi har iyayena da Sauran 'yan uwana, na san cewar ynx tuni sun haqura da ni. Don kuwa har na je gidan yari nayi shekaru goma babu wanda ya waiwaye ni. Su a 6angarensu Suna tsammanin ni ke da laifi, tunda dai ni na kashe wa Zubaida miji. . Da na je gidan Kawuna nan din ma ban yi katarin samun shi ba, don kuwa gidan a kulle yake da kwado. Da na tambaya ne ake ce min ya tashi ya bar kaduna tun shekaru biyu da suka wuce babu kowa a gidan. . Na rasa inda zan sa kaina in ji dadi, don kuwa a halin ynx ban san kowa ba." nima Kuma Babu wanda ya sanni. Zubaida ce kadai zata ganni ta tuna ni, gashi Kuma ita ma na neme ta sama ko qasa na rasa inda ta shiga a duniya. Shin anya kuwa Zubaida tana a raye? Wannan ita ce tambayar da na riqa nanatawa a xuciyata har nayi kwana daya ina neman ta, amma Kuma ko labarin ta ban samu ba." . Wasa-wasa har aka yi mako guda ina ta cigiyar inda masoyiyata Zubaida ta ke. Haka nake wuni tun safe har dare ina shige da fice a cikin garin. Duk wani wuri da na san cewar ta ta6a bani labarin ta je, sai da na je nayi tambaya a wurin, amma Kuma ban samu sa'a, wani ya ce min ya san inda take ba." . Aka yi wata daya Babu labarin Zubaida Babu labarin Wanda ya san inda take. Da naga cewar an yi wata uku ban ganta ba, sai na cire rai da Kuma tsammanin ganinta. Don kuwa nayi duk wani qoqari da ya kamata ace masoyi ya yi wajen neman masoyiya amma Kuma ban gano Zubaida ba." . Ganin yadda rayuwata ta zama a dalilin son wata mace daya a duniya, ina ta faman wahala akanta gashi har girma ya zo min ban sani ba." na kusa shekara arba'in amma Kuma ban samu nasarar mallakar wacce nake so ba, Kuma ban san inda take ba, wataqila tana raye a can wani garin, Babu mamaki Kuma ta dade da rasuwa. . Ba a jima ba da naga cewar ba ni da wata qwaqqwarar sana'a, tun fitowata daga gidan yari, sai na nemi aikin leburanci a wani reshen hukumar ruwa. Aikin mu shi ne xuwa haqa ramukan fanfuna da Kuma sauran aikace-aikace na leburanci. Wanda mutum zai yi ya samu abin da zai ci kada ya mutum da yuNwa. . Wata rana muna zaune ni da Sauran leburori 'yan uwana a hukumar. Sai wani mutum ya silalo motarshi mai qyalqyali da ganinta an san an mori inuwar sili, mutumin ya fito wani dan gajere mai fadin fuska yana sanye da kayan alfarma wadanda suka taimaka wajen rage masa muni. Ya shiga xuwa ofishin shugaban hukumar. Xuwa can suka fito tare, suka xo inda muke a Zazzaune muna jiran aiki. Shugaban hukumar ya ce. . "mansur zata ka je gidan wannan mutumin, sunan shi Alh. Rufa'i. zaka haqa mashi sabon rami, yana so ne a canza mashi hanyar ruwa. Ya ce ya baiwa iyalinshi sallahun cewar zata a je, don haka an san da xuwanka." . Alh. Rufa'i ya miqo min wani qaramin kati mai dauke da adireshin gidan nashi da Kuma lambar wayarsa. Na amshi katin, sannan na dauki kayan aiki shebur da Kuma diga. Na hau dan acha6a nayi masa kwatancen adireshin gidan ya dauke ni a cikin mintI bakwai muka isa unguwar, sannan muka je har qofar gidan. . in ban da na tabbatar cewar shi ne gidan da yaxo daidai da adireshin dake a jikin katin ba, da babu abin da zai sa in amince in shiga gidan. Don kuwa a tsarin ginin da aka yiwa gidan da wasu irin furanni dogaye da aka qawata gidan dasu, ya sa ni tsammanin ko shugaban qasa yake zaune a ciki ya ca6a.m. . Na sallami dan acha6a ya tafi, na isa bakin tangamemiyar qofar gidan riqe da kayan ginin a hannu na, sai ka ce mai xuwa ginin kabari, duk kayana, sun yayyage. A qalla dai na ci sa'a Akwai masu gadi a qofar gidan, don ina jinjinawa Tsoron in shiga Babu izini mutanen gidan su yi min ihun mahaukaci. . Na qarisa wajen masu gadin su uku ne sanye da kayan buzaye, kowannensu yana riqe da zabgegiyar bulala sannan Kuma sun bar gashin baki a fuskokinsu zaro-zaro. . Nayi masu sallama sannan na nuna masu katin shaidar aikina na leburanci, suka gani. Nayi masu bayanin abin da na zo yi da Kuma katin adireshin