← Book details Mugun Albishir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 21

Sashe 10

Mugun Albishir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun taska) "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . . To amma ni kuma ban yi murmushi ba, don kuwa tsoro ne cike da xuciyata. Dole ne in ji tsoron wannan labarin da na samu, don kuwa ni ina son in aureta . Gashi kuuma tun ba a je ko ina ba na samu wannan labarin wai mazan da take aura mutuwa suke yi. . Na sa hannu na share xufar dake a goshina. Alh.Bashir ya ci gaba da bani labarin . "wani lkcn mu maza muna da matsala mansur.ba mu san halin mata ba amma Kuma su sun san halin mu. Mu maza har Kullum mukan dauki kanmu ne a matsayin mutane wayayyu, don haka ba mu da tsayawa mu yi bincike ba akan mace idan zamu aureta. . Lkcn da na auri Zubaida na rainata mansur, don kuwa ni din nan da kake gani Dakta ne, ita Kuma yarinya ce qarama, ba wani karatun kirki tayi na azo a gani ba, don kuwa ko digiri ba ta yi ba." to amma Kuma sbd tsananinn wayau da makirci, duk da tarin ilimin nawa, wannan bai hana Zubaida ta shirga min maqarqashiya ba." . Ya yi saurin sauya akalar hirar . "bari in baka labarin abin da ya faru a tsakanina da matata Zubaida a lkcn da take so ta kashe ni. . "Alh. Ya kawar da idanunshi daga kaina ya qurawa wani qwan lantarki na gwal ido, sannan ya ce da ni. . "bana kusan shekara uku kenan da yin aurenmu ni da ita. Na fara haduwa da ita ne a wajen wani biki a zariya, duk cikin daruruwan 'yanmatan dake a otel din da aka yi shagalin bikin Babu wacce ta kai Zubaida kyau. Nan da nan na tuntu6eta muka fara hira. Abu kamar wasa tun a ranar farko ta yi min alqawarin zata aure ni, sbd ta san cewar ni ba qaramin attajiri bane. To amma Kuma kafin Zubaida ta yi alqawarin zata aure ni, sai da gindaya min sharudanta, cewar bata zama da kishiya, a lkcn ina da matata mai Suna fiddausi, dawowa ta gida keda wuya na sake ta, muka rabu. Bayan mun rabu sai na kwashe yaranmu biyu na kaisu legas wajen wata qanwata dake zaune a can. Don kuwa Zubaida ta ce min bata son hayaniyar yara a gidanta. Ni Kuma bana son in yi abin da zai 6ata mata rai a rayuwata. Ba a jima ba na aurota mansur, muka zauna kamar da gaske." . Ya ci gaba da kallon bango kafin ya ci gaba. . "bayan an yi wata uku da yin aurenmu, wata rana kwatsam sai Zubaida ta ce min wai zamu yi wata tafiya. Zamu je wani qauye can gariin kakanninta zamu gaishe su." muka shirya tun da sassafe muka shiga mota. A lkcn ne Zubaida ta ce min ita zata tuqa motar wai a cewarta bata so taga ina shan wahala. Ban yi mata musu ba mansur, na bata kan motar, ni Kuma na zauna a gefenta tana tuqa motar ina kallonta, muna hira a haka har barci ya kwashe ni ban sanI ba, don kuwa tafiya ce mai nisa, kuma gashi hanyar qauye ce akwai muka da kwazazzabai." . Alh.Bashir ya yi shiru na dan wani lkc sannan ya ci gaba. . "ina a cikin motar ina barci ban sanin ba mansur, sai Zubaida ta tsayar da motar akan wani tsauni mai bisa, Kuma a gefen tsaunin Akwai wasu manyan ramuka masu girma. Shi ne sai ta fito ta barni a a ciki. Motar ta fara gangarowa baya ita kadai, ba a jima ba ta saki hanya ta fada a cikin qaton ramin dake a gefen tsaunin. . Motar ta tarwatse a cikin ramin, ni dai ban farka ba sai akan gadon asibiti an yanked min qafafuwa. Ita Kuma Zubaida tana can a hannun 'yan sanda Suna tuhumarta a yadda aka yi ta bar wannan hadarin ya faru bata a cikin motar." . Lanqwasasshen mutumin ya dan saki ransa kadan ya dube ni. . "ka san abin da Zubaida ta fadiwa 'yan sanda da suka tambayeta mansur?" . Na girgiza kai a tsorace, xufa na wanke min fuska." . "cewa ta yi wai tana cikin tuqa motar ne sai ta ji fitsari ya kamata, shi ne a cewarta wai sbd tsabar matsuwa ta tsayar da motar ta fito bata kashe ta ba, Kuma bata sa waigi ba har motar ta fara gangarowa da baya. Ita Kuma wai sai sautin fadowarta kawai ta ji cikin rami. "yan sanda basu amince da wannan labarin da ta bayar ba, don kuw duk wanda ya ji wannan labarin ya san na qanzon kurege ne, ta shirya wata hanya ne kawai da zata kashe ni ta kaucewa zargi. To amma Kuma da yake ina matuqar qaunarta ni da kaina na dauki lauyoyi na tura su na ce su kareta, Bayan an gama shari"a an yafe mata, sai na dawo da mata ta Zubaida muka ci gaba da zama a matsayin mata da miji." . Na ji xuciyata tana harbawa fas! Fas! Don kuwa na gama tsorace. Da qyar nake shaqar numfashi. . "anya kuwa masoyiyata Zubaida ita ce take da irin wannan mummunan hali? Me yasa to take son ta kashe mijinta? . Kamar Alh.Bashir ya san tunanin da nake yi sai ya ci gaba. . "ba wani dalili ya sa Zubaida take son ta kashe ni ba mansur, sai don kawai tana so ta mallaki dukiyata ita kadai. Don kuwa ta san sirrin komai na dukiyata. Daga baya na sa an yi min bincike sosai akanta. Duk mazajen da ta aura a baya ita ce ta kashe su." tun tana yarinya matashiya take aure tana kashe mazajen ta. Wani abin takaici a game da munanan halayenta shi ne, Zubaida ta kan yi aure biyu ko uku a lkc daya. Don kuwa mazajen da take aure yawancinsu ba a zaune suke ba 'yan kasuwa ne dake yin kasuwanci tsakanin qasashen qetare. Sannan da na yi bincike akanta ya nuna cewar iyayenta na bogI ne ba na gsky ba ne....! Wasu "yan damfara ne kawai ta samu suke zama matsayinn iyayenta idan zata yi aure, wurin su ake xuwa a daura mata aure. . . Lp=16 Mugun albishir page 16 . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak . . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . Idan zata yi aure wurin su ake zuwa su daura mata aure." . Wannan labarin dole ne ya tayar min da hankali, don kuwa idan har wadannan halaye sune halayen masoyiya ta Zubaida to tabbas rayuwata tana cikin masifa. Don kuwa ni dai ina sonta ko da kuwa ni ma kashe ni zata yi a ranar da na aureta ba zan iya daina sonta ba." . Alh.Bashir ya ci gaba da cewa. . "mutanen duniya sai dai a barsu wajen neman abin duniya mansur. duk da wannan abu da ya faru wannan "yar talika bata daina qoqarin ganin ta kashe ni ba." Kullum ina lura da ita, so take yi ta kashe ni, Kuma na san cewar yau da gobe bata bar komai ba." wata rana zata kashe ni. Zata yi masara." . Ya sake fadada murmushi ya ce da ni . "shi ya sa ni Kuma na fahimci kudina take so, sbd haka ne nake yi mata dukan kudina Kullum. Don kuwa Tunda ta mayar da ni gurgu, babu wani abu da zan yi a rayuwata in ji dadi, shi yasa nayi alqawarin daga nan har xuwa ranar da zata kashe ni Kullum sai na yi mata bulala hamsin mansur....na kasancewar kome zan yi mata ba zata bar gidan nan ba sai ta cimma burinta. Ina matuqar jin dadin zamana da wannan mata tawa mansur. Kada ka ta6a zaton don so da qauna take zaune da ni alhalin ina gana mata wannan azabar, ni na san Akwai abin da take son ta mallaka a wurina." . Ya yi dariya...Akwai alamar shi kanshi yana matuqar jin dadin wannan labarin da yake bani. To amma Kuma ni dai ban ji wani dadi da wannan labarin yake dashi ba." . Nayi ajiyar xuciya na ce dashi. . "wannan matsalar ka ce kai da matarka alhaji. Bai kamata ka sanar da ni ba." wannan sirri ne da ya shafeka kai da ita. . Ya yi min murmushi sannan ya harare ni. . "kaima ya shafeka mansur." . Na ji Gabana ya fadi. Me ya shafe ni? Na shiga uku, anya kuwa bai fahimci Akwai wata alaqa tsakanina da matar shi ba? . "wannan magana ta shafeka mansur." . Ya sake tabbatar min yana kallona. . "don kuwa a jiya da daddare lkcn da nake dukan matata nayi mamaki da na hangeka a bakin tagar falo kana kuka. Me yasa to kake kuka don kawai kaga ina dukan mata ta, ko kana jin tausayinta ne mansur?" . . ** ** ** . . Wasu tsofaffin mata ne su shida a zaune kowacce ta tasa qatuwar qwarya a gabanta Suna ta amada ba ji ba gani. Ni Kuma ina tsaye a gabansu ina ta kallonsu, gashi dai ina son in taka rrawa, amma Kuma wata qatuwar malum-malum da na jibga a jikina ita ce take rinjayata, ko motsi bana iya yi. Wasu Suna zagaye da ni Suna kallona Suna yi min dariya, waigo ina son in taka rrawa amma Kuma na kasa motsawa. . Ina nan Kuma tare da tsofaffin dake kidan amadar, sai naji sun sake kaurewa da kidan kamar zasu fasa min dodon kunnena. Na ji sautin kidan ya kaure ga Kuma dararrakun da "yan kallo suke yi ya ta"azzara. A daidai lkcn ne na farka a gigice daga barcin da na ke yi. Na ganni kwance a dakin da aka sauke ni matsayin direban Hajiya zubaida. Sai a lkcn ne na fahimci mafarki nayi. . A daidai lkcn ne Kuma naji anan kwankwasa min qofar dakina da qarfi. Na yunqura daqyar na fara qoqarin tare mayafin dake nannade da ni kamar ankwa. Wannan shi ne ya ganar da ni cewa ashes sautin amadar da nake ji ba wasu mata ne ke kidan ba, qofar dakina ake bugawa. San Kuma
Chapter 10 · 0% Book details