Sashe 7
Mugun Albishir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da Kuma rashin qarin guiwa sun kamani. Don haka ina xullumin wataqila idan Alh. Bashir yaga shigar da nayi ya ji ban kwanta mashi a raina ba." wataqila ma ya ce ya fasa daukata aiki a gidansa. To amma kuma me zai sa in damu kaina? Shi Fa gurgu ne, ni Kuma ina da qafafuwana. . Don haka sai na tunkari gidan kai tsaye, na samu tsohon dake gadi a zaune kan bench, tun kafin in yi masa sallama ya dago kai ya duba ni sannan yayi min murmushi, kamar damar can ya ta6a ganina, sai dai Akwai alama ya san da xuwana. . Bayan nayi masa sallama ya amsa, tun kafin in yi masa Bayani ko ni wane ne, sai ya tambayeni. . "kai ne mansur da aka ce zaka xo?" . Nayi saurin gyada masa kaina. . "eh, ni ne." . Tsohon ya riqe ya tarbeni cikkin girmamawa. . . Lp=10Mugun albishir page 10 . . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan bn ishak (Madugun taska) . . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . . Tsohon ya tarbeni cikin girmamawa. Akwai alamar fadanci a tattare da shi, sannan Kuma idan mutum yayi la'akari da busassun idanunsa da ya ragadawa kwalli da Kuma yadda Ya karkace hularsa gefe daya, nan da nan mutum zai gane cewar a wani zamani can da ya gabata sanda yana Saurayi da wahala idan ba taqadarin yaro akayi ba." . Tsohon ya sake ce min..." . "sannu da xuwa mansur...ai tun daxu Alh ke tsammanin xuwanka. Ya ce da ni in ka xo in jagoranceka mu shiga tare. Zo mu je mansur." . Na bi Tsohon a baya muka shiga cikin gidan, ina zazzare idanu kama 6atacciyar tunkiya. A farfajiyar gidan, danqara-danqaran motoci ne guda biyar Suna ta qyalqyali kowacce launinta gaban. Tsohon ya bude wata qofa. Muka shiga wani dogon daki mai cike da gwala-gwalai. Sai qamshin ke tashi a ciki. An malale darduma mai taushi kamar zata hadiye qafar mutum idan yana tafiya kanta. Na ja na tsaya a wuri guda ina kallon ikon allah. Tsohon ya juyo cikin mamaki ya ce da ni. . "zo mu je mana mansur." . Na ce dashi. . "ina Kuma zamu je banda nan baba?" . Tsohon ya bushe da dariya sannan ya ce da ni. . "ai bamu kai falon alhaji ba." nan ai zaure ne kawai mansur....kai dai biyo ni kawai mu tafi." . Tsohon ya sake ja na muka fita daga tsararren dakin, muka fada wani tanqasheshen falo mai dauke da wani qaton gilashi a bango yana bayyanar da hotunan namun daji iri-iri, da Kuma kyawawan furanni, sai ka ce fuskar majigi. Shima wannan gwala-gwalai ne a jiki kamar kayan wasa. Na rabu6e a jikin bangon falon ina jiran Tsohon ya bani izini, don kuwa tsammanin da nake yi duk inda na tsaya a cikin falon laifi ne....! . Tsohon ya dube ni cikin murmushi . "naga ka sake tsayawa mansur. Me ya faru Kuma?" . Na ce dashi. . "ai na dauka nan ne falon alhaji din da kake magana." . Tsohon ya sake yin dariya ya ce da ni. . "haba mansur, me alhaji zai yi da wannan falon, kai dai baka rabo da abin dariya Wlh. Wannan ai dakin saukar baqin ne, masu neman ganawa da alhaji kafin ya buqaci ganin su." Kada ka damu mansur, zamu je kaga falon alhaji." . Tsohon ya sake shigewa gaba, na bishi a baya muka fice daga wannan falon ya sake tura wata qofar zinare dake kalle, duk jikin qofar qyalqyali yake yi. Nayi tsammanin zan hango ko me ke a cikin dakin ta gilashin qofar, Maimakon haka sai na hango hoton razananniyar fuskata a jikin gilashin qofar. Nan da nan sai na fara addu'arziqi allah ya sa babu qananun yara a gidan. Don Kada in tsorata su su da abin da na gani a jikin qofar a matsayin fuskata. Tura qofar keda Wuya sai ta bude ba tare da wani sauti ba, a lkcn ne to naga wani abin mamaki, Kuma na gamsu haqiqaTsohon nan bai yi qarya ba, Sauran dakunan da muka je a baya, idan aka saka su a cikin tsararren falon Alh.Bashir Gurgu to duk sai sun 6ace ma an rasa inda suke. Tsohon ya shige gaba na bishi a baya. na saka qafata a cikin tsararren falon mai dauke da lallausan kilishi. Na fara kalmar shahada a 6oye a xuciyata, don kuwa nayi tsammanin xuqeni kilishin zai yi. . A zagaye da falon kujeru ne na alfarma shiga-shiga sun yi kuri sun saka wani faffadan teburi a tsakiya, yana ta sheqi da daukar idanu. Tunda nake a duniya ban ta6a ganin kwatan-kwacin kayan alatun da na gani a wannan falon ba." gabaki daya gidan cunkushe yake da kayan alatu. Sai da naga tsohon ya xube a qasa cikin girmama, sannan na lura da abin dake zaune dan surutu akan kujeru kamar kashin tsoro. Wani motsattsen mutum ne dan tsurut a zaune' qafafuwan wandon shi biyu suna ta reto babu komai a cikin. Idanuwanshi jawur kamar garwashin wata. Dogon hancinshi da Kuma tsukakken baking shi hade da motsattsiyar fuskarshi su ne suka maishe shi xuwa siffar aku kuTuru sannan suka maida shi mai siffar 'yan bori . "rana ya dade ga mansur din da ka ce in ya xo a shigo dashi." . Tsohon ya fada a sanyaye sannan ya tashi cikin girmamawa ya fice daga falon kamar walqiya. Mutumin da na kasa tantance aljani ne ko bil adama , ya dube ni sannan yayi murmushi. Ina tsaye akan shi qerere ina dubanshi. Wani in ya zo ya same shi zaune a falon, yana iya daka mashi tsawa ya ce zai kore shi. Don kuwa sam muhallin baiwa yi kama dashi ba sam. Zai yi kimanin shekaru hamsin, kanshi cike yake da furfura, kamar an yi 6arin garin masara. . "ga wuri nan mansur, zauna mana." . . Lp"11 mugun albishir Page 11 . . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . . Tare da ni. Abu ihsan bn ishak . . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . "ga wuri nan mansur, zauna mana." . Ya ce da ni, sannan ya nuna min kujera da hannunshi. Nayi ajiyar xuciya sannan na za6i kujera daya na zauna. Duk da yake Akwai na"urar sanyaya daki a falon, hakan bai hana ni jin xufa na keto mani ba, don kuwa na tabbatar wannan firirinn da na iske a ynx shi ne attajirin da ya dauke ni aiki, Kuma shi ne ke da wannan tarin dukiya kamar qasa. . Ganin na qurawa qafafuwan wandonshi idanu, sai mutumin ya dubi datsattsun qafafuwanshi sannan ya dubenni ya ce da ni. . "kada kayi mamaki mansur, na san cewar kawunka ba zai rasa baka labarina ba, bani da qafafuwa, ni gurgu ne, yadda ka ganni zaune a haka nake kwana nake tashi babu inda nake xuwa." . Na girgiza kaina cikin damuwa. Don kuwa ban san abin da zan iya cewa ba, ya sake cewa da ni. . "to amma duk da wannan naqasar da nayi mansur, ina da milyoyin kudi masu yawa. Sannan Kuma duk abin da nake neman a duniya na samu." . Ya yi murmushi, shi kanshi ga alama abin da ya fada yayi mashi dadi. Nayi shiru ban ce dashi komai ba, xuwa can Kuma sai na ji yayi ajiyar xuciya, ya dawo maganar da ta kawoni gidanshi. . "mansur kamar yadda ka sani, ka xo gidan nan ne a matsayin direba to amma Kuma ba ni zaka riqa tuqawa ba, ni Babu inda nake xuwa, matata zaka riqa tuqawa a mota, duk inda zata je kai nake so ka riqa tuqata kana kai ta." . Ya tsayar da idanunshi akaina sannan ya rage fara"a. . "ka san abin da yasa nake son ka zama direban matata mansur?" . Na ce dashi. . "A 'a." . Alh Bashir ya ce da ni cikin damuwa, . "ban yarda da ita bane mansur, ina zarginta, don kuwa ta kan dauki mota ta fita ban san inda take xuwa ba." Babu mamaki don taga na zama gurgu na naqasa shi yasa take xuwa wajen wasu mazan a can wani wajen. Shi yasa na yanked shawarar in nemo mata direba. . Ya sake yi min murmushi, ina zaune ina kallon shi. . "ina matuqar son wannan mata tawa mansur." . Ya ce da ni. . A duniya kaf ban ta6a ganin abin da nake so ba irin ta, shi yasa nake masifar sonta, ko kallon ta naga wani namijin yayi, sai in ji duk na damu. Zan iya sa bindiga in harbe mutum idan na fahimci yana son wannan mata tawa. Shi yasa aka nemo min kai mansur, don kuwa na samu labarin kai yaro ne mai amana. Kuma nutsttsen mutum, na san cewar zaka riqe min amanar matata. Na barta a hannunka amana mansur, Kada ka bari mutane su riqa kallonta. Ko kallon ta ba na so a riqa yi. Ina fatan zaka riqe min amanar ta mansur?" . Nayi ajiyar xuciya sannan na ce da shi. . "ba komai Alh. In allah ya yarda zan riqe maka amanarta kamar yadda kake so." . Alh.Bashir yayi murmushin jin dadi. To amma ina matar tashi take? Na qosa in ganta. . Muna nan zaune sai muka ji sautin shigowar mota cikin gidan, a can harabar gidan. Aka ba motar wuta xuwa can kuma aka kashe motar, sai muka ji an rufe ta da qarfi garam! Alh.Bashir ya ce da ni cikin damuwa, bayan ya dube ni. . "matata ce ta dawo mansur, haka take Kullum bata tuqa mota a hankali, duk ta lalatamotocin gidan nan." . Muna nan zaune sai muka ji sautin tafiyarta zata shigo falon. Qwas-qwas! Naji gabana ya fadi, don kuwa akwai wani zamani da ya wuce na ta6a jin irin sautin tafiyar. . Ta turo qofar falon ta shigo a fusace Babu ko sallama, na waiga cikin kidimewa na dubeta. Jikin jikina ya tsaya cak!! Sannan hantar cikina ta kada. Numfashina ya tsaya na wucin gadi sbd tsananinn kaduwar da nayi a dalilin ganiNta . Tana nan da xunxurutun kyanta kamar yadda na santa tun a shekarun baya