Sashe 15
Mugun Albishir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
hakan, Kuma ke ce kika roqe ni da kada in yi maki qarya. Shi yasa na fadi maki gsky." . Zubaida ta lumshe idanunta cikin damuwa, sannan ta dafa sitiyarin motar xuwa can ta bude idanunta ta qurawa gilashin motar idanu. . "me ya sa ka kashe min mijina mansur? A wane dalilin zaka kashe shi?" . Zubaida ta tambayeni lkcn da wasu sababbin wahayen ke gangarowa daga cikin idanunta. . Na ce da ita. . "sbd ina sonki Zubaida." . Ta juyo a tsorace ta kalle ni, muka hada ido. . "so?" . Ta tambayeni . Na share xufar dake a goshina. Sannan na ce da ita. . "ranar wanka ba a 6oyon cibi Zubaida, ina son ki san cewar na dade ina son ki a rayuwata. Tun ranar da na fara ganinki a makaranta, tun ranar na ji ina sonki a duniya. A haka na dauki shekaru uku ina faman da radadin soyayyarki a xuciyata amma Kuma na kasa sanar dake, don kuwa na san cewar kin fi qarfin matsayina Zubaida." . Har xuwa lkcn da muka gama karatu ban daina sonki ba Zubaida. Ban san inda zamu sake haduwa ba, a haka na sanyawa xuciyata tabbacin haduwarmu wata rana, don in ganki in samu sUkuni a xuciyata. . Lkcn da na zo nan garin neman aiki, sai Kuma sai na ci sa'a, mijinki yana neman direba, shi ya daukeni aiki, a lkcn ne na sake ganinki, sannan Kuma na ji soyayar da nake yi maki tun shekarun baya ta sake taso min ta dawo sabuwa. Sauran abubwan da suka faru kuma kin sani Zubaida. Don kuwa a dalilin lbrn da kika bani a daren jiya cewar mijinki ba zai mutu ba sai ya qara shekaru talatin a duniya sai na ji kishi da Kuma damuwa sun cika min xuciyata. Don kuwa ba zan iya tsayawa ina jiran shi ba, shi yasa na kashe shi, don ina so ki aure ne.kamar yadda kika yi min alqawarin idan ya mutu ba zaki sake auren tsoho ba, yaro zaki samu irina wanda zaki yi soyayya dashi ki more quruciyarki." . Zubaida ta sunkuyar da kanta a kan sitiyarin motar ta na xubar da hawaye a lkcn da ta ji na kai qarshe. Ta ce da ni. . "ka yi kuskure mansur,don kuwa wannan abu da aka aikata ni zaka dorawa laifi, kasancewar na fading maka mutane da damar Suna zargina waigo ina so in kashe shi, ynx idan aka yi bincike dole ne a nemo wani abu da za a rataya min, don a ce na kashe shi. Babu wanda zai dora maka zargin kisan kai mansur....na tunda kana so na da gaske. Me zai san ka jawo min laifin da ban aikata ba? Wannan ita ce soyayyar da kake yi min?" . Nayi ajiyar xuciya sannan na ce da ita. . "Kada ki damu Zubaida, Babu wanda zai dora maki zargi. Ni nayi alqawarin in har sun gane kashe shi aka yi, to zana fito in fadi masu gsky cewar ni na kashe shi. Ba ke ce kika kashe shi ba." . Zubaida ta dago kanta a sanyaye daga kan sitiyarin motar ta yi min kallon soyayya, to amma Kuma Akwai hawaye a idonta. Ta ce da ni cikin sassanyar murya. . "ban ta6a tsammanin kana sonar kamar haka ba mansur.. Allah ya bar mu tare ni da kai masoyina, Kuma in allah ya yarda ba zasu gano cewar kashe shi aka yi ba.da zarar na gama takaba zamu yi aurenmu na soyayya." . Tunda na zo duniya ban ta6a jinjinawa wata magana mai dadi da sanyaya xuciya kwatankwacin wannan ba." na ji farin ciki da kuma annashuwa sun cika min xuciyata. Ta6! Waigo ni ne yau Zubaida take kallo tana kirana masoyina. Abin da nake ta mafarki shekara da shekaru gashi ynx ya zama gsky. . A daidai lkcn da muke zaune a cikin motar ne muka ji 6urarin motar asibiti ta dauko gawa. Ita ce motar da ta dauko gawar marigayi mijin Zubaida. Motar tazo ta wuce mu kamar iska ta juyo mana baya a guje, muka bi ta da kallo ni da Zubaida masoyiya ta. . Don kuwa mun san Kowanne ne a cikin motar, muka kalli juna cikin kunyar abin da muka aikat, sannan muka yi saurin kawar da kanmu. Kafin motar gawar ta 6ace ne mu daina ganinta na tuno Alh.Bashir da kuma lbrn da ya bani da zaman soyayyarshi da zubaida, na tuno lkcn da ya kira ni muka ci abinci tare a falo. Yana matuqar so na! . Na tuno gargadin da ya sha yi min tun xuwana gidan. . ..ka riqe min amanar matata Zubaida....."Don kuwa duk duniyar nan babu abin da nake so kamar ta...." . A karo na farko na dan ji tausayinsa ya yi zarya a xuciyata. . . ** ** ** . . Bamu samu sukuni ba har aka yi biyar da yin rasuwar, don kuwa 'yansanda tuni sun miqa maganar xuwa kotu. Kullum sai mun samu baqin dake kawo mana ziyara, baqin kuwa ba wasu bane, 'yansanda ne da lauyoyi wadanda ke xuwa su tsare mu da tambayoyi. Don kuwa mutane da damar Suna ta bayar da jita-jitar wai wwannan mutuwar da mijin Zubaida yayi wai ba ta allah da annabi ba ce. Kashe shi aka yi. Ni da zubaida masoyiyata muna shanta tsinuwa a wajen mutanen duniya kamar 'yan kashin kasuwa. Don kuwa ni da ita aka dorawa zargin kashe Alh.Bashir gurgu. . Tun anan saura kwana biyu a fara shari'a. Zubaida ta dauki lauya Wanda zai karen mu a kotu. Da ranar shari'ar ta zo tun da sassafe jami'an tsaro suka zo suka yi awon gaba da mu har da mai gadi muka dunguma. Aka fara shari'a. . Abin ya zo a bazata, don kuwa 'yansanda sanda sun yi dogon bincike, mai tsanani . Kuma sun gano abubuwa da dama fiye ma da yadda muka yi tsamni . . Lauya kotu shi ya fara miqewa yayi jawabin share fage a shari'a ar. Kuma miqewarsa ke da wuya ya fara jawabinsa kai tsaye. . "wannan shari'ar ba zata daukemu xuwa wani dogon lkc ba, don kuwa tuni mun gano yadda wannan ala'amari ya gudana. Zubaida ce ta kashe mijinta, Kuma ta kashe shi ne ta hanyar ba shi guba a cikin lemon gwangwani . Jikina ya auna gawarmarigayin kumaa zamu tsayar dashi a gaban kotu don ya ba.da shaida a bisa binciken da ya yi. Sannan Kuma shi kansa Wanda ya siyarwa da Zubaida wannan guba zamu gabatar da shi a gaban kotu don ya ba.da shaida..." . Abin ya bani mamaki, Kuma ya yi matuqar jikina ni. . . Lp=24mugun albishir Page 24 . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . Abin ya yi matuqar bani mamaki Kuma ya rikita ni, don kuwa ni dai na san cewar ni na kashe shi. Ni na karya mashi wuya, to amma Kuma gashi lauyoyi sun yi bincike sun gano cewar wai guba ya sha ya mutu. Wata qila Kuma biri yayi kama da mutum, don kuwa ni dama a lkcn da na je na kashe shi, ban ga yayi motsi ba." . Lauyan kotu ya gabatar da likitan da ya xo ya auna gawar Alh.Bashir yayi gamsasshen bayani. Kowa ya gamsu tabbas gubar marigayin ya sha ya mutu. Daga baya Kuma Lauyan ya gabatar da wani mutum, mutumin ya ce sana'arsa ne sayar da magungunan qwari shekara da shekaru. Zubaida ta zo wurin shi ta sayi magani mai qarfin wanda tace zata xubawa wasu qwari dake gina mata rami a lambun gidan ta...." a ranar da ta sayi maganin a ranar ne Kuma mijinta Alh.Bashir ya rasu ta hanyar shan guba a cikin lemonn gwangwani . Lauyan dake karemu ya tashi yayi nashi surutun, to amma Kuma bai samu wasu hujjoji ba da zai dogara dasu. Don kuwa lauyoyin dake a 6angaren kotu sun fi shi hujjoji da za a yarda dasu. . Na dubi Zubaida dake a tsaye naga tana hawaye a gaban kotu, naji tausayinta ya kama ni, don kuwa ni na jawo mata wannan masifar, dama ta ce da ni dole ne a nemo wani abu da za a dora mata zargin a ce ita ta kashe shi, tunda dai tayi qaurin Suna a wurin mutane. . Da na tuno alqawarin da na yi mata cewar ba zan ta6a bari a dora mata laifi ba, sai na ce da Lauyan dake a 6angarenmu ina da magana. Mutanen dake a kotu suka dube ni, alqalin da lauyoyi kowa ya dawo da hankalinshi wuri na. Na ce. . "ba Zubaida ta aikata wannan laifi ba, , ni na aikata laifin kashe mijinta. Ni na sayo guba na xuba mishi a cikin lemo ya sha. Amma ita Zubaida da ta sayo tata gubar qwari ta xubawa a cikin fulawoyi." . Mutane da dama sun yi mamakin abin da na fadi. Don kuwa ba a ta6a ganin wanda ya dorawa kanshi laifin kisan kai ba don kawai ya kare wata mace. To amma Kuma mecece soyayyar? Idan har da gaske kana son wata mace kamar yadda nake son Zubaida to dole ne mutum ya sadaukar da rayuwarsa. Dominn kuwa mace kamar Zubaida ta cancanci komai daga wurin masoyinta. . A qarshe alqalin kotun ya nuna damuwarshi akan yadda wannan shari'a ta zo a rikice. Don kuwa shaida qwaqqwara da hujjoji sun nuna cewar Zubaida ce ta kashe shi. Gashi Kuma na fansheta na ce ni na kashe shi, amma Kuma ni ba a ga wata hujja da za a bi ace ni na kashe shi ba." don haka sai alqali ya yanke min hukuncin daurin shekaru goma a gidan yari sbd babu qwaqqwara hujjar ni na kashe Alh.Bashir Kuma a yadda kowa ya fahimci shari'ar shi kanshi alqalin ya san Zubaida ce ta kashe shi, a 6angarena Kuma ina ganin tunic nayi alqawarin karemu masoyiya ta, bayan haka Kuma ni ma ai na murde wa gawar wuya a cikin dare. . A haka 'yansanda suka yi awon gaba dani. Muka hada ido ni da Zubaida masoyiya ta tana kukan baqin ciki. Nayi mata murmushin Kada ta damu,