← Book details Mugun Albishir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 21

Sashe 20

Mugun Albishir Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

macen da yake so. Ko da kuwa ace ita bata qaunarshi, kamar dai yadda nima na fada cikin tarkon son Zubaida Kuma nayi rashin sa'a, ita bata so na a rayuwarta. . Nan da nan cikin sauri na fice daga dakin, na bazama xuwa babban ofishin jami'an tsaro don in ga masoyiyata, Kuma na dauki alqawarin sai na ceto rayuwar ta kamar yadda na ta6a ceto rayuwarta a wani zamani can da ya wuce. Mai yiwuwar a sake yanke min hukuncin daurin shekaru goma, idan ban ci sa'a ba kuma a yanke min hukuncin daurin rai da rai, ko Kuma hukuncin kisa. . To a qalla dai ko ma dai me za a yi min, na san cewar ba a kashe min wannan kyakkyawar mace da nake so ba shekara da shekaru. Wani dadin gushi Kuma na san cewar ko bani a raye zata riqa tuna ni tana baiwa mutane labarin soyayyar da nayi mata a duniya, Kuma ta haka ne zata gane cewar ni ne masoyinta na gsky, Wanda ba zata sake samun kwatankwacina ba a rayuwarta. . . ** . . Lkcn da na isabella ofishin 'yansanda na roqi ganin Zubaida na dan sha wahala kafin a amince a bani wannan damar. Daga baya ne aka hada ni da wasu kwalawa biyu suka raka ni xuwa wani daki inda aka kume ta da wani murgujejen kwado kamar Damisa. da yake Akwai dogayen qarafunna da suka tare qofar dakin, ta nan na hangota a zaune ta kifa kanta akan guiwoyin qafufunta tayi shiru ga alama kuka take yi. . 'yansanda suka ce sun bani minti biyar agurguje, sannan Kuma suka dan matsa daga nesa suka bani wuri. A lkcn ne na kira sunanta a cikin tausayawa. Zubaida ta dago kanta a cikin kaduwa da mamaki a lkcn da tajikistan muryata. Idanunta sun kode sbd tsabar kukan da ta ci. sannan Kuma duk gashin kanta ya hargitse da gani ka san ta ci uban wahala a wajen tuhumar. Ta taso cikin sauri ta matso jikin qarafunan, sanye da doguwar riga baqar mai kwalliya a qirjinta. Ta tsaya a jikin qarafunan muka qurawa juna idanu. Ta fashe da kukan nadama ta ce. . "ba zan iya hada ido da kai ba mansur....na cuci rayuwarka na zalunceka a duniya ka yafe min..." . Na ce da ita cikin tausayawa . "....kada ki damu Zubaida na yafe maki duniya da lahira, ba koma..." . Zubaida ta sake dubana hawaye Suna tsere akan kyakkyawar fuskarta ta ce da ni.ya . "tun lkcn da jami'an tsaro suka kamani suka kawo ni wannan wurin, Babu wani mutum da ya xo ya kawo min ziyara yaga halin da nake ciki mansur....amma gashi kaine mutum na farko da yaxo ya kawo min ziyara, duk da butulcin da nayi maka baka mance da ni ba mansur?" . Ta sake fashewa da wani kukan. Na ce da ita. . "ba komai Zubaida, wannan ya wuce, ki daina wannan maganar, na san cewar abin da ya faru sharrin shaidan ne. Kuma ynx ma na sake xuwa ne don in ceto rayuwarki, ba zan ta6a bari wani abu ya sameki ba muddin ina numfashi a duniya. Na zo ne in sanar dake cewar zan fadawa 'yansanda cewar nine na turo mijinki Alh. Rufa'i daga saman bene ya mutu. In yaso ke ma ki basu wannan labarin, na amince ko me zasu yi miki ni suyi min a madadinki Zubaida." . Zubaida ta girgiza kai cikin rashin amincewa. Ta zzaro hannunta ta dora su akan yatsun hannuna dake riqe da qarafunan. Wannan shine karo na farko a rayuwata da ta ta6a yi min haka. Ta ce da ni. . "ba zai yiwu ba mansur,don kuwa ka dade kana shanta wahala a dalilin qaunar da kake yi min.ko me ya faru da kai ni ce na jawo maka. Lkc ya yi da ya kamata nima in fuskanci na wa hukuncin, don kuwa na aikata laifuka masu yawa a duniyar nan. Ba zan sake bari laifina ya shafeka ba." ynxn kam na amince kai masoyina ne mansur,don ka san martabar soyayya, Kuma ka san haqqin masoyrka, amma Kuma baka yi dace da wacce kake so ba." ban dace da irin rayuwarka ba mansur....kai mutumin kirk ne, ni Kuma mai laifi ce. Ina fatan zaka samu wata masoyiyar wacce ta fi ni a duniya, don kuwa ni tawa tazo qarshe. A wannan satin za a yanked min hukuncin kisa!!!" . Naji takaici ya lulli6e min xuciyata, sannan Kuma hawaye suka fara xubo min..." Zubaida ta sake qanqame yatsun hannuna ta ce da ni.ya . "Kada ka damu mansur, mutuwata ita ce samun sauqi a gareka, idan ina raye zan ci gaba da jawo maka wahalhalu a rayuwarka, don kuwa kana matuqar sona, ba zaka iya bari wani abu ya faru da ni ba." kayi haquri kabarin su yanke min wannan hukuncin a halin ynxn na amince da soyayyarka, to amma kuma hakan Bashi da wani amfani. Bakin alqalamin ya riga ya bushe."l . Muka kalli juna muna kukan soyayya da baqin ciki. Zubaida ta yi min murmushi kamar Babu wani abu da yake damunta. Ta ce da ni a sanyaye. . "na da dade ina yi maka (MuGun ALBISHIR) mansur. To amma kuma yau a karon farko zan yi maka albishir mai kyau. Wannan shine sakayyar da zan yi maka a bisa wahalhalun da kasha da ni baya. . "wane irin albishir zaki yi min Zubaida?" . Ta rage muryarta kamar zata yi min rada sannan ta ce . "mansur ina dare yayi ka je Bayan gidan mijina da na turo shi daga saman bene, marigayin Alh. Rufa'i idan ka je zaka isle shuke-shuke a cikin lambun dake a bayan gidan. A cikin wadannan shuke-shuke zaka iske watgajeruwar bibiyar gwanda, ka tonal gindin bishiyar, zaka iske wani qaton akwatu na 6oye, kudi ne a ciki naira milyan hamsin ka dauka duk rabonka ne, damar na 6oye su ne don Kada azo bincike a gansu. Ka daukesu na bar maka su kyauta. Na gode Kuma da soyayyar da ka nuna min, Kada ka mance da ni masoyina, na gode, ina yi maka bankwan...."
Chapter 20 · 0% Book details