Sashe 18
Mugun Albishir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da mai gidan ya bani. Daya daga cikin buzayen wani sangamemen qato mai qirar 'yan kokuwa ya ce da ni. . "baring in shiga in sanarwar hajiya, bata son a shiga a dame ta in tana barci. Bamu son ka shiga ka bata tsoro, bata san da xuwanka ba, Kada ka jawo mana laifi a banza." . Sauran qartin suka yi dariya daya a cikin su ya ce. . "gskyrka mamuda, ya fi kyau ka jefi-jefi ka fara sanar da ita. Don kuwa idan rana ya 6aci sai ta rufe mutum da zagi kamar ita ta haife shi." . Qaton farko da ya fara magana Wanda shi ne suke cewa mamuda ya tashi ya shiga cikin gidan....xuwa can Bayan wani lkc sai ya fito ya dube ni.ya ce. . "ta ce a shigo da kai ta san maganar." . Na bi shi a baya muka shiga cikin gidan....tare. 6ata lkc ne na zauna bayyana aljannar duniyar dake maqare a cikin gidan. Don kuwa duk inda mutum ya kai dubana a farfajiyar gidan dawisu ne manyan da qanana fululu suke yawo, sannan Kuma a wani sashi bene ne hawa uku an qawatashi da gilasai da Kuma matattakalar zamani. Na ci gaba da zare idanuwa ina kallon abin mamaki a lkc guda Kuma ina biyu da qaton Wanda ke tafiya daqyar sbd qarfi kamar toron agwagwa. . Mun xo bakin wata qofa daidai inda wata siriyar hanya ta ratsa cikin wasu shuke-shuke, sai qaton da ya rakoni ya juyo y ce da ni.ya . "ka tsaya nan ka jira zata fito." . Sannan ya komai can wajen abokan aikinshi, ina nan tsaye dauke da diga ina mamakin a inda mutane suke samun irin wannan dukiya mai yawa a wannan duniya. Xuwa can sai naji an bude qofar, sannan an yi motsi a kusa da ni.ya na dawo da hankali na inda na ji motsin. Tana a tsaye a jikin qofar gilashi sanye da qananan kayan na dogon wando da kuma guntuwar riga. Ta xubo dogayen gashin kanta sun watsu a kafadarta kamar yadda ta saba yi a shekarun baya. . Ban san lkcn da na xube kayan haqan ramin ba na baje a qasa. Ko a wanne zamani, Kuma ko a ina na ganta to dole ne sai na gane ta. na dubi fuskarta mai cike da annuri duk da irin tsawon shekaru goman da nayi ban ganta ba, ni dai ban ga wani canji ba." tana nan radau da kyanta sai kace wacce ake canzawa fata. Sai sheqi take yi. . Na tuno muryarta dake a 6oye a dodon kunnena tun zamanin da muna makaranta. Tun muna yara. . "...yaya sunan ka...?" . Haqiqa nazo a sa'a. Na gano masoyiyata Zubaida. . . . ** ** ** . . . Zubaida!!!" . Na ambaci sunan a tsorace ina kallonta cikin tsananin kidimewa kamar naga aljana ko fatalwa. Na qara taku daya na matsa daf da inda take tsaye tana kallona sheqeqe kamar wacce take kallon mahaukaci. Ganin na matsa kusa da ita cike da farin cikin ganinta, sai ta ja da baya a tsorace. . "a ina ka ta6a gani na ka san ni malam." . Ta tambayeni cikin mamaki. . "Kuma wa ya fading maka Suna na?" . Na ce da ita a kidime. . "ni ne mansur.... Na fito daga fursuna tun wata uku da suka wuce. Ina ta nemanki, Zubaida me kike yi a nan gidan?" . Zubaida ta dan yi jim tana kallona, ga alama tana tunno inda ta sanni ne....! Xuwa can ta ce da ni.ya . "don allah ka sake tuno min inda na sanka, a ina muka hadu?" . Na ji xuciyata ta harba kamar talge . Na ji mamaki da damuwa sun taru a xuciyata. Wai ace Zubaida bata gane ni ba, Bayan Kuma ni ne masoyinta dake riqe da qaunarta fiye da shekaru goma shafi'u shida, tun ina saurayi dan makaranta. . "zaune kina nufin ki ce kin mance da ni'? Ni nefa mansur masoyinki. Ni ne Wanda na ceto rayuwarki a kotu a lkcn da na bayyanawa kotu ce ni ne na kashe mijinki Alh.Bashir ba ke ce ba." . Zubaida ta dan yi murmushi kadan kafin ta ce. . "oh...(i could remember), sai ynx na gane ka. Ashe dama kana a raye mansur? NI na dauka cewar tuni ka dade da mutuwa kaima. " . Na ji Gabana ya fading ras, don kuwa a yadda Zubaida take kollona tana fada min maganganun Babu wata alamar soyayya, kamar ma ba ta ta6a ganina ba sai ynxn. Ta ce da ni cikin damuwa. . "me ya Kawoka gida na, Kuma wa ka zo nema?" . Na ce da ita cikin damuwa. . "baiwa kamata ace kin yi min irin wannan tambayar ba Zubaida. Da ace kin san yadda na qarar da gaba daya rayuwata kan soyayyarki, da ba ki yi saurin mancewa da ni ba." . Zubaida ta ce da nia fusace. . "baka da hankali."Kai ynxn har kana tsammanin akwai wanii lkc da zan ji ina son wani mutum irinka a duniya mansur? . . Lp=28Mugun albishir Page 29 . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . Ba ka da hankali." . Ta ce da ni.ya . "kai ynx kana tsammanin akwai wanii lkc da zan ji ina son wani mutum irinka a duniya mansur? Kada in sake jin ka fadi irin wannan maganar a nan gidan, don kuwa ni matar aure ce, Kuma nan gidan mijina ne." . Zubaida tayi ajiyar xuciya, sannan ta ci gaba da cewa. . "bari in fadi maka wani abu wanda baka sani ba." tun lkcn da ka fara gani na a makaranta ni matar aure ce. Ban ta6a zama babu aure biyu ko uku akaina ba." na ta6a zama da maza hudu a lkc daya, Kuma babu wanda ya sani a cikin su, ba qananan milyoyin kudi na ke samu ba a dalilin wannan aurace-aurace da nake yi mansur. Ni ce nake kashe mazajena in kwashe dukiyarsu. Idan na qarar da wadannan mazajen sai in qara auren wasu. Abin ya zame min kamar sana'a." . Na ji tsoro da fargaba sun kama ni, na xubawa Zubaida ido ina mamaki jin cewar wai ita ce da bakinta take iya fadin wadannan kalamai. To amma Kuma dama marigayin mijinta ya bani wannan labarin a wani zamani da ya wuce. . Ta ci gaba. . "duk lkcn da naga wani miloniya, Kuma naji ina son ya aure ni in zama matarshi bana shan wahala mansur. Don kuwa ni kyakkyawa ce. Ba Kowanne namiji zai ganni ya ce baya sona ba!" . Zubaida ta fadada murmushinta tana kallon wani dawisu dake gudu a harabar gidan cike da jin dadin abin da take fadi. Har xuwa lkcn da dawisun ya 6ace a cikin 'yan uwanshi, bata dauke idanunta daga kansu ba." ni Kuma ban daina kallon ta ba." ta ce da ni tana tunani. . "na dade ina son in kashe Alh.Bashir don kuwa duk a cikin mazajen dana aura shi ya fi bani wahala fiye da kowa a cikin su." ya cika taurin ran tsiya, na bi hanyoyi da dama don in kashe shi, amma Kuma ban samu nasara ba." gsky ne, haqiqa ni ce na tura shi a rami da gangan, musamman na samu waje nayi fakin da motar don ta dawo baya ta fada cikin ramin yana barci bai sani ba." tun kafin mu fito na zuba mashi maganin barci a shayi. Nayi haka ne don in tuqa shi yadda nake so ba tare da ya farka ya fahimci abin da nake son aikatawa ba." to amma a wannan hanyar ma ban samu nasara ya mutu ba, sai dai kawai ya rasa qafa ya zama gurgu." . Zubaida ta dan yi siririyar dariya, sannan ta dawo ta hade ranta. Naji xufa na keto min ta ko ina. Ta dube ni cikin raini , sannan ta ce. . "ina ta neman hanyar da zan bi in kashe gurgun mijina kwatsam, sai ga ka mansur wai ka zo mijina zai daukeka aikin direba. Da ganin haka na san cewar na samu hanya da zan kashe mijina cikin sauqi Kuma in fitar da kaina daga zargi. Don kuwa na san cewar kana sona, kana qaunata tun muna makaranta. Ban ta6a fitowa na nuna maka na fahimci kana qaunata ba sbd baka kai matsayin da zan yi soyayya da kai a duniya ba mansur." . Don haka sai na yaudareka, nazo dakinka a cikin dare na baka labarin qarya don ka ji tausayina ka taimake ni. Kuma na baka tsoro na ce mijina ba zai mutu ba sai ya qara shekara talatin a duniya. Abin da baka sanin ba shi ne; Tun kafin in zo in baka wannan labarin dama tuni na zubawa mijina guba ya sha a lemu. Sai da na tabbatar ya mutu san naxo na same ka a dakinka. Nayi maka haka ne don ka tashi ka je ka kashe shi ka riqa tsammanin kai ka kashe shi ba ni ba." ina ganin lkcn da ka shiga falon kana sanda a cikin dubu ka mirdewa gawarshi wuya. Sannan ka koma daki. Nayi haka ne sbd kodak anzo shari'a ba zaka bari a dora min laifi ba Tunda kana qaunata, Kuma kayi alqawarin zaka yi wa kotu bayanin kaina ne ka kashe shi." . Bayan mun je kotu an yanke maka hukuncin daurin shekara goma, ni Kuma sai na sake samun wani attajiri, Wanda yake son yaga ya ajiye kyakkyawar mace yarinya. Kafin wata hudu ya bi Alh.Bashir shiga na kashe shi. A cikin shekaru goman da kayi a furzun ba zan iya fadin adadin mazan da na aura ba kai tsaye, sai dai Kuma a halin ynx sun zama tarihi." . Xuciyata ta ci gaba da bugawa kamar zata fasa qirjina ta fito waje. Don kuwa Zubaida ta gama rikita ni. Na bi ta da kallo cike da takaicin ganin na qarar da rayuwata a qaunarta, amma Kuma ita ba ma ta ni take yi ba." sannan Kuma na dorawa kaina laifin da ba ni na aikatashi ba, don in karen rayuwarta da mutuncinta naji nayi shekaru