← Book details Mikiya Part 2 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 9 OF 17

Sashe 9

Mikiya Part 2 Complete Hausa Novel.txt · about 7 min read

"Kada in damu fa kike cewa beenanzer? Kinsan kuwa irin tashin hankali da nake ciki duk sanda na buÉ—i idanuna na kalli waÉ—an nan shegun yaran? A matsayin Æ´aÆ´an sarki hassan Al-hassan wanda sune magadan sarautar Emaar's ko kin mance sune manyan Æ´aÆ´an maza a masarautar nan?
shin baki ganin iyakata da mulki sai dai gani sai hange tunda sune manya akan nawa ƴaƴan? ko baki ga yadda komai ya fara juye min ba? Shi wannan tantiran ya ɗauke uban nashi da ina dab da cikar burina Amma shegiyar tsohuwar ta ɓata min aiki, Kuma sama taka an kuma shammatata ta hanyar ɗaura masa aure wanda shine babbar barana a gareni! Ya kike son nayi? Zuciyata na dab da tsayawa da aiki beenah! A ko wanne hali a ko wanne irin yanayi inason a sake tarwatsa ahalin Maryam inba ta kama da ɓatarwa tamkar shekarun baya da aka ɓatar da ƴar Razeenerh to suma a ɓatar min dasu,yanda ko labarinsu ba za'a sake tayarwa bare na baya su riska tamkar da yadda akama Eesha Emaar's"

Cike da wani irin tsoro jesrah taja da baya tana me toshe bakinta da hannuwanta, cike da tashin hankali da tsananin tsoro ta zaro ido da tarin mamaki bata gama dawowa hayyacinta ba taji Mum Mandood na sake faÉ—in.

"Wallahi tallahi billahil azeem zanyi komai dan ganin bayan Maryam da yaranta, zanyi duk abinda ya kama domin in kauda _ABDOUL-MALEEK da kuma zAID_ A matsayin magadan sarautar Emaar's masu jiran gado, dan wlh Allah a wannan karon zan iya kashesu bawai ɓata su a matsayin mashaya da kuma maneman mata ba, domin kuwa wannan rana tana ɗaya daga cikin abinda yasa nayi bore a shekarun baya. Amma sai gashi nayi GUDUN ƘADDARAR wannan rana me kama da irin yau!. kuma sai gashi yanzun alamu na gwada min dukkan wani dagewa da taƙarƙarewata wajen gujewa wannan rana irin haka saidai kamar ma biye take da nawa sawayen ƙafa da ƙafa domin al'amura ne keta faman yimin warwara ya zamanane kamar ina dufka ana min warwara.
Loƙacin mutuwar _JADDERN ASHAAN_ yayi ba tare da wannn kwalmaɗaɗɗiyar tsohuwar ta sani a tunaninta ita kaɗaice me basira har wani tinƙaho take da babu wanda yasan ida jaddern ashaan take! Bayan kuma ta haifi ɗa mara amfani lusari Tirr da mutum me irin halin Hussein.....

Cikin tsananin kaÉ—uwa jesrah ta juya da sassarfa tana tafiya da baya baya harta samu tabar sassan Mummy Mandood Iska kawai take fesarwa Sam tama rasa ma wanne irin tunani zatayi,gaba É—aya kwanyarta ta toshe Shin su waye waÉ—annan Eesherh da kuma jaddern ashaan? Tambayar da tazo ta mata tsai a zuciya kenan, ko gabanta bata gani babban burinta kawai ta ga Oum É—inta domin tasan ita tana da amsar duka waÉ—an nan tambayoyin nata.
Karon da taji tayi da mutum ne ya sanyata saurin cin birki, itama a nata ɓangaren da sauri merrah taja nata birkin dafe da goshi. "Wayyo kin fasa min goshi"
Ta faÉ—i tana me duban jesrah É—in da sukaci karo a hanyar shigarta palon Oum ita zata fito ita kuma zata shiga. Dake ba'a cikin nutsuwanta take bane ya sanya ta furta. "Sorry Habeebty banganine sosae" tana faÉ—ar hakan ta shige palon Oum É—in....

Oum dake tsaye har yanzun bayan fitan merrah ne tayi saurin duban bakin ƙofan, ganin saɓanin tunaninta ne ya sanya ta faɗin, "Jesrah bakin fita wurin aiki bane kamm?"
Kanta take girgiza mata tana kuma nufota É—an daidaita numfashinta dake seezing tayi tana dannar setin haert nata tare da furta.
"Oum Su waye _JADDERN ASHAAN_ da kuma _Eesherh_ ?"
Da wanj irin masifar karfi Oum ta juyo tare da riƙo hannuwan jesra ɗin cije da matsanancin tashin hankali ta fuskanceta dakyau tare da faɗin.
"A ina kika ji? Waye kuma Jaddeern Ashaan? Easher kuma ƴ.. Ƴar...... Sai kuma ta ƙarasa furta abinda take son faɗin sakamon zuciyarta da taji ya mata wani irin mugun nauyi, tare da hautsuno mata da wasu shuɗaɗɗun al'amura maban banta cikin abinda bai wuce second biyu ba.
Zaune takai gefen haɗaɗɗen royal bed nata tare da matse hannun jesrah ɗin cikin nata tana fesar da numfashin daya mata tsai a ƙahon zuciya.
"Komai ya kusa bayyana kansa, komai kuma ya kusan zama tarihi Insha Allah kiyi shiru da bakinki Allah yana daga bayan me gaskiya"
Haka kaÉ—ai Oum ta faÉ—im ma jes tace ta fita aikinta Allah ya bada sa'a jiki a sanyaye ta fita ba tare data fashimci komai É—in da taso ffashimta, amma ba komi insha Allah a matsayinta na Æ´ar jarida dole sai tasan wani abu daga cikin labarin kafin bayyanar komai É—in kamar yadda oum É—inta ta fadin mata......

Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sake a loƙacin data gama tabbarwa da cewa jesrah tabar room ɗin baki ɗaya Goshinta takai ƙasa tare da furta.
Ya wadud,Ya zul'arshin makin, Allahu ahad kaci gaba da ƙare wannan bayin naka daga duk wani sharrin me sharri. Ya Rabbis samawati wal'ard karkaci gaba dabe mugyaye damar da zasuci gaba da zalumtar keɓantattun bayinka, Allahu kaine Allah kaine me yadda kaso a duk sadda kaso ɗin kuwa Allah ka mana maganin Azzaluman da burinsu suci zalinmu su zalumcemu Ya ilahi ya mujibud da'awati Allah kare ɗaukakin keɓantattun bayinka wanda basuji ba basu gani ba, Allah ka mana maganin wanda suke ganin sunfi ƙarfinmu Allah ka zarta da ikonko na _KUN FA YAKUN_ akansu ya Allah!!!"
Oum takai ƙarshen adda'ar nata tana me fashewa da wani iri kasalallen kuka irin wanda ya daɗe yana cin zuciyar nan.

★★★

_AK_

Gaba ɗaya ɗakin tsit yake daga sautin karatun Afif muhd taj bakajin komai a room ɗin sai iskan dake kaɗawa irin ta farkon daminar nan da kuma ta sanyin AC kawai kakeju. Sai wani irin ƙamshin Air freshsheners da turarukaan wuta masu daɗi da babu jimawa aka gyara may, Ɗakine me girman gaske dake ɗauke da setin royel furnitures masu tsananin kyawun gaske White colour sai ɗan adon milk color daya aka musu. Daga ta nan bakin bed ɗin wani haɗaɗɗen kuwait carpet ne me tsananin laushi da aka shimfiɗa wanda yakai har tsaƙiyar ɗakin, daga gefen window's kuma wata keɓantacciyar kuwait sofa ce Ajiye da ƙaramin fridge.
daga gefen mirror kuma wani babban table ne da aka jera littattafan Addini shimili guda gasunan, daga ta gefen gabas akayi wani zagayyen wuri na musamman wanda ke shimefiÉ—e da wata kalan lallausan praymed me taushin tsiya, sai wasu zagayayyun kuwait decoration's irin masu haskaka room É—in, sammm É—akin baya da woni tarkace haka yake simple gwanin birgewa wanda mutum zaiyi normal real life nashi cike da bada cikakkar nutsuwa.
Agogon ɗakin ne ya buga ƙarfe 11:31 am na ranar yau Monday daidai bjgawn agogon ɗakin yayi daidai da Mirza handle na ƙofar bathroom ɗin da Ak yayi, Anutse ya fara ɗora santaleliyar ƙafarsa me cike da gargasan gashi baƙi siɗik akan ƙaramin carpet ɗin dake shimfiɗe bakin ƙofar bathroom ɗin. kafin ya Ida fitowa gaba ɗaya ya a nutse ya fara taka sawayensa cike da nutsuwa take ɗakin ya gauraye da ƙamshin shower jal ɗin da yayi wanka dashi.
Ahankali ya nufi gaban dressing mirror yana ɗaure da towel navy blue iya ƙugunsa da yama wani irin loko lokon ɗauri, sai wani milk saman wuyansa yana goge ruwan jikinsa dake yarara lafiyayyar tsayayyen jijinsa me jini a jika sai faman walainiya take tamkar woni beby sabuwan haihuwa.
Wannan fuskar da cikar kamala mai nuna barazana wa maƙiyinsa dole ne ya yarda yaci wannan suna na jarumi kuma ingarman namiji me ji tashen samartaka wanta jinin mulki ya gama ginashi, zuciyar nan nasa samm babu daɗi baƙar zuciya ta ɗan motsa da dukkan alamu kenan yau don a matuƙar haɗe take.
Ba kuma komai ne ya fusatar dashi ba sai zancen matar shi da Oum ta masa a daren jiy!, wani ɗan numfashi ya sauƙe a karo na farko tare da ware lumsassun idanunsa yana me sauƙe ganinsa saman Abubuwansa da yake da tabbacin Zaid ne ya kawo mishi.
Komai yake yi cikin tacin zuciya yake tsafff ya gama shirya kansa cikin wasu haɗaɗɗun egyptanian riga da wando ya sanya sky blue, pcarp nashi ya zira inda farar lafayayyar cutie face nashi ta ƙara fidda ainihin taswirar kyawu da kuma zatinsa. A natse ya isa gaban Iphone nashi inda sautin karatun ke fita take karatun kuma ya tsaya sakamakon shigowan ƙira ɗan lumshe Ido yayi ya kuma sake buɗewa ya kalli agogon dake manne jikin bango, red lips nashi ya ɗan ciza bada yawa ba yana ɗaukan phone in dama yasan ƙiran bazai wuce Oum nashi bace, ba tare daya ɗauka wayan ba ya nufi hanyan fita,
kamar yadda yana yinsa na rashin fara'a yake haka yafito daga cikin ɗakin hannunsa riƙe da key nashi na Keken da yake son hawansa yau. Drectly Sassanta ya fara nufa tana zaune akan wata royal sofa ruwan zuma, tayi crossing ƙafafunta wanda da duk alamu a wurintane Ak namu yayi gado aha.
Chapter 9 · 0% Book details