← Book details Mikiya Part 2 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 12 OF 17

Sashe 12

Mikiya Part 2 Complete Hausa Novel.txt · about 7 min read

********
_NIGERIA'N_
*Lagos*
******************
_Mariya Kamaal_
Tana tsaye a kitchen sanye take da top irin wannan wanda daga ƙasansu ake ɗinkewa hakan yasa gefen cikinta yake a buɗe sai crazy 4½, shigowanta kenan
kanta a kunce a nutse tasa hannu ta tattare shi ta sakashi cikin trap band Yunwa take ji sosae hakan ne ya sanyata dafa couscous jallop bata jima kuwa ta fito ajiyewa tayi a dinning Area tayi sama domin É—aukar chocolate nata na gado batakai ga hawan stairs É—inba aka danna bell.
''haiiii waye kuma yake ƙoƙarin shiga haƙƙin ni da kuma babynmu?" da yanayi na gajiya ta faɗa da kuma yunwar da take azalzalarta tana me yarfe hunnuwa jan ƙofar tayi da ɗan ƙarfi Tana sake ambatar, koma dai waye zai shiga hakkin babynmu wlh"
"Baban babyn ya dawo domin sammm ya gaza samun nutsuwar zama ba tare daya sake jin dumin babyn da kuma maman babyn ba"
Kamaal ya faÉ—i yana jawota zuwa cikin jikinsa. ÆŠan bakinta ta tura sai kuma ta furta "yunwa mukeji first"
"Aha go ahead muje na kula da maman baby kar yunwa ta kama min baby tun a ciki"
Ɗan rufe idonta tayi alamarn kunya sai kuma tayi saurin janye jikinta tana wucewa gaba, "Ina kuma kike shirin zuwa haka?" ya tambayeta ganin tana ƙoƙarin hawa sama. "Zan ɗauko chocolate nawa ne fa!"
"Dawo a nan wai ban hana shan zaƙin nan haka nan ba ne kammm?"
Kwa6e fuskanta tayi kwalla na tarun mata "kuma fa kasan idan har bada chocolate naci ko miye ba ba zama yake mun a ciki ba zanyi aman sane Aiyn"
"Mrs Aiyn dawo nace badai chocolate bane ganan wani nazo miki dashi"
Ya faɗi yana tashi ya dawo da ita yana zaunar da ita kan ƙafafunsa...
Shida kansa ya bata abincin duk lauma bayan laum saiya haÉ—a mata da wannan chocolate É—in don haka shine wanzuwar zaman lafiyansu su duka tunda ta sami cikin nan kuwa.
"Sannu da zuwa Aiyn"
Ta furta bayan ta gama ƙoshi abinta tukunna. "Uyummmm saida kika gama cika ciki kana kika tuna damin sannun really?"
"To ai zuwa loƙacin ko kallon gabana banyi sosae ne aiyn"
ÆŠan shafa gefen fuskanta yayi yana faÉ—in "Babyn Aiyn rigima"
Haka dai suka shashance abinsu aikin dabai koma ba kenan.
★★★
Ta buɗe baki kenan da niyar sake wata maganar, amma maganar da maƙale a bakinta sakamakon tozali da idanuwanta suka mata da merrah.
Wani irin tsuma tare da yankar zuciya ta tsinci kanta a ciki da kallon meerah ɗin, jinin jikinta kuwa a take ya shigawani irin hautsina mata wanda hakan kai tsaye ke tabbatar mata da tafasa jinin jikinta yake. Ido Oum ta kafe Mah dasu domin ganin reaction nata, Sammm ta gaza janye idanunta akan meerah ɗin da ƙyar ta samu ta fusgo kalmar
"Easherh? DIDINA!!!"
Da sauri itama merrah É—in ta juyo da kanta zuwa inda tajiyo irin muryan Anne'nta masoyiyarta sakk. Itama chakkk É—in ta tsaya tana kafe matar da ido babu wata tantama zata iya rantsewa wannan fuskan Anne'ntane wllh. Saidai ita wannan É—in tsantsan hutu da jin dadi daya gama huda fatar jikinta da kuma tsananin hasken fatar ta.
To amma wannan kamannin ai sunyi yawa kuma dai tasan Anne'nta bata da alaƙa da matar dake tsaye a gabanta. Domin kuwa tasan basa da alaƙar gari ɗaya ma bare kuma ta jini.
Hannuwanta suna rawa ta matso ga Merrah É—in tare da shafan fuskanta cikin wani irin raunin murya ta furta.
"Irin kamar ki É—aya da DIDINA! saidai a yanzu duk inda take nasan tafi haka zama ta iya haifar yake"
Hannunta tasa tana kifewa saman na matar da ganinta ya bugar mata zuciya, wllh zata iya rantsewa da'@ Nig taga matar nan babu abinda zai hanata kamata tace itane mahaifiyar Anne'nta duk da kuwa cewan wannan matar baici ace ta haifi ya Annenta ba.
Muryanta yana rawa itama ta furta "Da'a ce a ƙasarmu na ganki babu abinda zai hanani cewa kene mahaifiyan Anne'ta"
Saurin rungumeta Merrah Mah tayi tana furta "Allahu ahad!! Allahu ahaad!!! Wllh irin muryan Queen Lajja na ce dake"
Kamar daga sama taji Mah taji muryan Oum tana faÉ—in.
"Taya barewa zatai gudu ɗanta kuma yayi rarrafe ita ɗin JININKICE! Ƴar gidan Easher'nkice RAZEERNERH"
Da wani irin bala'in ƙarfi ta sake rumgume Merrah ƙa ƙam a jikinta tana fashewa da wani mugun kukan daya kusan sarƙe numfashinta.
"A ina? A ina MARYAM? Kar dai kice min itane MATAR ABDOUL-MAKEEK? Inkuwa hakane lallai Allah da girma yake kuma shine buwayi gagara misali shi yasa tun a ranan data sanwo ƙafanta cikin wannan gida bugun zuciyana ya sanja, Sanyin da nakeji a tare da Easherh na wllh shi naji tun a ranar"
Sai kuma tayi shiru tana ɗan ɗago fuskan merrah idonta bai sauƙa akan komi ba sai kan wani ɗigo da yake kan gefen wuyan merrah ɗin wanda yake tamkar zanen tatto.
Sake rungumeta tayi sai kuma sukayi luuuuuuu sakamon sumewar da Mah É—in tayi.
Merrah kuwa dama bata san mike faruwa ba ita dai tasan mafarkine kawai take wanda a cikin mafarkin jinta da ganinta suka jima da shuɗewa, shi yasa ma loƙacin da sukayi bayan itama tabi ta kawai a tunanin ta duk a cikin mafarkin ne
Kafin takai ƙasa Oum tayi saurin tararsu itada Jesrah da shigiwarta kenan room ɗin Ak din don ganin Pa'pa'nta. Dawowarta daga wurin aiki kenan don Zaid ne ya isheta akan tayi maza ta dawi zata may wasu abubuwa kafin wannan kayan fushi da bacin ran ya dawo gidan wato AK.

Tana zaune bata san sadda ta miƙe tsaye ba zumbir tana furta "Wacce Easher'n ?"
Ta tambayi hadimar nata wanda dama shigowarta kenan ta dawo daga fitar da tayi tun da sanyin safiya. dog year rigace a jikinta abaya wacce aka narka manyan kuÉ—aÉ—e kafin a siyeta ,saikuma gyalenta data yane kanta sai jakarta da kuma takalminta suma duka designer ne.
Damƙar wuyanta tayi tana me sake faɗin"Nace miki wacce Easher'n?,ba tambayarki nake bane wai?"

Ta faɗa cikin ɗaga murya wanda hakan saida ya razana Hadimar daganin yanda yanayin Moh jiddon ya sanja loƙaci ɗaya.
"Umm ummm dama dama.....
"Ummm dama me ki buÉ—e baki kimin magana dama me?
Ta faɗa tana sauƙe wani irin wahalallen numfashi mai nauyi haɗe da dunƙule hannunta A lokacin inka ganta zaka kasa gane inda yanayinta yake,shin baƙin ciki take ji kokuma tsoro da fargaba Ko tashin hankali ne?
"Ke beenanxeer wai ko kunnuwanki sun daina aiki yadda ya kamata ne na dawo miki dasu daidai.?"
Haka Moh Jiddoh ta sake rikirkita beenah cikin rawan jiki da dama yawanci a kawoma wani gulman wani kake cin ubanka jikinta baki ɗaya bari yake ta buɗi baki cikin sarƙewar numfashi ta furta.

"Wllh da gaske ne nazo wucewa ta cikin balcony É—in Oum jesrah naji tana zance da dukkan alamu ma waya take yine, shine fa na lafe naji tana cewa Æ´argidan Mah data batace ta bayyana amma anan É—in ba ita bace Æ´artane ma wacce aka É—aurama Boss Aure da ita wai Merrah!"

Wani irin wulgar da beena ɗin moh tayi duk kuwa da cewar jikin tsufa gareta amma kai dama kallo ɗaya zaka mata kasan cewa irin tsofin najadun nan ne maƙirai. Wata sakakkar ijiyar zuciya ta sauƙe tana jin duniyar ma baki ɗaya na juya mata, kanta kuma na neman juyewa zuwa na masu ta6in hankali.

Wayanta dake gefen Royal chiar ta É—auka tana dannawa da alama wani ko wata take nema a wayar cikin gaggawa.
"Hello Hussein? Maza ka bincikamin yanzu shin da gaskene matar da aka aurama Aboul-maleek aure da ita Æ´ar Easherh ta bayyana kokuma watace ne daban?, ina son bayanai yanzu yanzu sannan ka tabbatar babu wanda ya zargeka don nasan halin haukarka idan ya motsa kana iya kwa6emin aiki"
"To shikenan Moh yanzu kuwa zan bincika É—in"
"Idan har ya tabbata haka ne to da akwai gagarumar matsala! don shirin da mukayi tsawon shekaru gaba ɗaya wargajewa zayyi,dan haka ka taka tsantsan ka ganomin komai, Amma ta wata hanyar da sauƙi domin idan harya tabbata Yarinyan itace, kuma ita aka aurama wannan shegen kaga kenan babu Aure tsakanin su, tunda da uwar yarinyar dashi tantirin uba ɗaya suke."

Daga tacen Hussein É—in yaja ijiyar zuciya hankalinsa na É—an dawowa jikinsa sai kuma ya furta.
"Wai to garin ya haka ta faru a bazata taya ma zakice haka duk shirin da mukayi na 6atar da Ita a duniya saida ta dawo? mtswwww aikin banza nikam ba samm ban yarda ba wllh moh"
Chapter 12 · 0% Book details