← Book details Mikiya Part 2 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 14 OF 17

Sashe 14

Mikiya Part 2 Complete Hausa Novel.txt · about 7 min read

Ya daka mata wata kafurar tsawar data sanyata ƙamewa, "Ke mahaukaciyan inace hala? Kinyi ƙanƙanta dana bibiyi tatsitsiyar yarinya irinki nevermine har gaban abada"
Duk da cewar a tsorace take kuma kanta a rufe yake da duka tafukan hannuwanta amma hakan be hanata murguÉ—a masa baki ba tare da furta.
"To nidai ko miye na haÉ—aka da girman Allah ka fice a gidan nan baki É—aya kaga nan gidan sarautane ba kamar nigeria bane daka saba dabanci wllh idan Mijina ya ganka zai iya halakaka! Tunda naji kowa na gidan tsoron shi yake ance É—an zafin kaine wllh tsaf zaisa bindiga ya harb......

"Keeeeeeeeee!"
Ya sake sakar mata wata tsawar yan faÉ—in "Allah ya kiyashe na harbe wani saboda mace macen ma ke irinki marar aji"

"Wllh zanyi maka ihun ɗan iska tunda ba zaka fita ata arziƙi ba"
"Uhumm Aha bara to na matso yadda zakifiyin me dalili ihun da kuma lasisi ganin dai da gaske gadan gadan nufo tan yake ya sanyata miƙewa a guje tayi hanyar data fito wata bathroom. Taku ɗaya tayi ana biyun taji ya ɗamki tsintsiyar hannunta, "wayyo Allah na wayyo Oum kina ina kizo wani ya shigo har cikin gida zai keta min haddi!"
Wani mugun bugu ya kaima bakinta a take gefen lips nata yaÉ—an fashe ba da yawa ba kaÉ—an, "Idan kuma nine mijin sai kiyi yaya kuma?"
Tuf ta tofar da miyau wanda jini ya ɗan biyo kaɗan "Allah ya rufa asiri ma ɗan daba irinki yazama mijina, kasani nan ɗin gidan mutumcine da masu mutumci kuma ka sakarmin jiki domin jikina me darajane me tsadane ba kowanne datti da ƙazamin jiki ne ke haɗa nasa da nawa ba na bayama ban yafe ba wllh"
"Sai kuma Akayi katari _ABDOUL-MALEEK HASSAN EMAAR's nine nan a matsayin mijin naki! Idan har baki haÉ—iyi zuciya a daren yau kin mutu ba ke É—in baki cika babbar mara kunya ba kuma naki _ZAFIN KAN_ kaÉ—an bame yawa bane"
"Allah ya rufa asiri wllh dana zauna da ɗan ta'adda marar kishin ƙasar sa kalanka kara na haɗiya zuciyan na mutu tirrrrrr da mugun fata"
Tana faɗin haka ta yanka masa cizon da yazo may a bazata wanda hakan shine ya bata daman guduwa tana Mirza ma bathroom ɗin Key. Numfashi ta shiga sauƙewa a hankali tanajin yadda zuciyanta ke bugawa, "Mugu! Azzalumi!!"
Ta faɗi tana durƙushewa a wurin wani abu me zafi da narka Zuciya na dunƙule mata wuri guda. Cikin muryan kukan taci gaba da faɗin "What do you want?,why did you bring me here?, leave me I can't Meerah yanzu ni ba merrah ɗin da ka sani bace ada ni matan wani ce sunan matar aure nake amsawa azzalumi ɗan daba me satar mutane I hate you."
Ashe ma bata sani ba ita kaÉ—ai take abinta don tuni yabar bangaren ma baki É—aya.
Da kyar ta iya fitowa a bathroom É—in tana jin yadda zuciyanta yake a cinkushe, Sallah ta gabatar anan idda take bacci me nauyi yayi awon gaba da ita duk wainar da ake toyawa kuwa bata sani ba har zuwa washe garin ranar.
Da misalin biyu da rabi na rana baki ɗaya duk wanda yake da kusanci da waccen maganar sun gama kammala a babban palon Mah, Harda Sarki Hassan Al-hassan kasancewar jikinsa da sauƙi sosae taron zayeet ash ya buɗe musu da adda'a kafin Sarki Hassan ya furta, "Alhamdulillah Ahar kullum Allah shine abinda godiya me bayarwa da kar6ewa a sa'ilin da yaso!, Ayau ma shine ya sake haskaka mana wani hasken da muka jima da rasashi ta hanyar disashewar daya mana ya bace mana battt! Amma kuma cikin ikonsa da buyawarsa da kuɗirarsa ya bayyana hasken da muka jima da fidda rai da wannan Hasken kwasan kuma da yaso a rana guda, a wuni guda ya haskaka mana shi kansa asalin wannan hasken wato ya bayyana mana ƴarmu da muka jima da cire tsammani daga gareta wato Eash.......

"Be kuwa bayyana muku ba wllh"
Suka jiyo muryan moh jiddoh tamkar wacce aka wullo daga sama. "Idan har ina numfashi hakan bame yiyuwa bane! Kuma idan harda gaske ne yarinyar itace wacce aka É—aurama aure da wannan tantirin kenan babu Aure a tsakaninsu kenan?, tunda uwarta yayar Abdoul-maleek ce"
"Ba yayarsa bace"
Nusassiyar muryan Sarki ash ya daki duka kunnuwansu tare da ratsa tsakiyar ƙirjin kowa.
Gaba ɗaya kallo ya koma kansa ciki kuwa harta ita ƴar tijarar wacce dakyar mahboob ya samu ya cetota daga wannan shegen ginin ƙasar.
"Kwarai kuwa ba yayarsa bace hasalima basa da wata alaƙa saita musulinci!"
Cikin muryan nan da yake fita da kaushi kaushi da kuma hargagi ta furta "To saika mana ƙarin bayani tunda daduk kan alamu daga sama ta faɗo ba haifarta akai ba"
Moh jiddoh ta faÉ—i tana wani harare hararenta. "_EASHERH ASH MAYESH_ , Ita É—in cikakkiyar Æ´ata ce ta sunna kuma Æ´ar Auta ta"
"Rainin hankali taya ƴar da na ni ce mutum ta farko na fara amsarta da hannuwana Loƙacin da Razeenerh ta haifeta yanxu kuma don son cika wani mugun nufi kace ba ƴarta bace?, to wllh inma auren kuke son halastawa to kuwa tabbas haramtaccene"
"Moh Easherh kwarai ba Æ´ar dana haifa bace Æ´ar Ash ce"
Wani mugun kallo ta data cillama Hassan ne ya sanya shi shanye maganarsa.
"Uhummm tell me ina jiran ka sanar dani ta yadda aka haihu a ragaya"
"Ganin a waccen loƙacin MATATA RAZEENERH bata haihu ba har shekaru biyar da aurenmu ne ya sanya sarki ash ƙirana ya sanar danj cewar, Idan har queen lajja ta haihu mahaifiya ga Razeenerh kenen ya bamu duk abinda ta haifa halak malak. amma karna sabarwa ma kowa tun kuma daga loƙacin Zeenerh ta koma can madina da zama da nufin tana laulayi me zafine moh idan baki manta ba a loƙacin haka na sanar dake?"
Ya faÉ—i yana kallar moh É—in kanta ta gyaÉ—a mishi alaman ehhhhh ta tuna da hakan, ci gaba yayi da faÉ—in.
"Bata tashi dawowa ba sai a daren ranar da queen lajja ta haifi Autarta mace wacce suma haihuwar taso musu a bazata. A kuma daren naje nazo da zeenerh sai tayi kamar a masarautar ta haihu sai mukayi amfani da hakan gashi kuma dama babyn kamanninta ɗaya da Razeenerh kasancewar uwa ɗaya uba ɗaya ba ƙarya ba. a haka tayi rainon babynta saidai tarin wani abin mamakin sammm babyn taki amsan mama a wurin Razeenerh dole muka renata da madara har takai yaye ba tare da kowa ya fuskanci komai ba.
A haka har takai shekaru takwas kwasam kuwa dare ɗaya rana ɗaya sama ƙasa muka Nemi Easherh muka rasa, wanda wannan shine tushen komai har bayan wasu shekaru tun muna san ran wata rana zamu ganta har muka haƙura muka fawwalama Allah komai. A haka mukaci gaba da zaman mu ba tare da zeenerh tayi ko 6atan wata bane, ganin hakan ya santa cemin nayi wani auren ko allah zai bani haihuwar, haka har auri Yasmine wato mahaifiyar Adeenerh abin mamaki ko wata biyu bata cika ba ciki ya bayyana a wurinta wanda kuma wata ƙudirar na allah saiga itama Razeenerh'nan da nata cikin.
Kusan loƙaci ɗaya suka haihu fikonsu kwana biyar a tsakani, A kuma ranar da zeenerh ta haifi ɗanta namiji a kuma ranar Yasmine ta rasu. Bayan ta faɗamin wasu maganganu masu girma da nauyi.
Rasuwanta babu daÉ—ewa sarkin kano na nigeria ya bani auren Æ´arsa wacce ada naso bijerama hakan saida zeenerh ta tunasar dani kana na amince,cikin ikon Allah kallon farko nama maryam naji soyayyarta tsantsa a zuciyana. Ashe Allah ya soni da rahamarsane da naso bijire masa ashe itace cikon mahaÉ—in garkuwan haskena.
Bikinmu babu dadewa sai gata da ciki wacce ansha gwagwarmaya ba laifi baga Moh ba ba kuma ga matar biyunina ba matar hussein kenan domin kiri² suka nutsa tsanarta a fili babu ko kara. Daga inda ta haifi ƴan biyun ƴaƴanta duka maza wata _ABDOUL-MALEEK_ da kuma _ZAID_ Daga nan mabuɗin wasan ya soma har kawo kwanan yau kuwa!!!"

A fusace ta miƙe tana furta "lallai na yarda gyaɗa mayaudariyace tunda akayita da kwanso amma ba komai ko anan A-Hassanu ka nuna min ban isa dakai ba na haifekane ban haifi halinka ba"
Fuuuuuuuuuuu ta fice tana barin ɗakin domin wasan ai bezo karshe ba dole saita cika burinta kota kuwa shine ƙarshen numfashinta.
Chapter 14 · 0% Book details