← Book details Mikiya Part 2 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 11 OF 17

Sashe 11

Mikiya Part 2 Complete Hausa Novel.txt · about 5 min read

Harda ɗan guntun gudunsa ya isa ka dattijuwar dake zaune ta juya bayanta da dukkan alamu woni abu me muhimmanci take ko take dubawa. Ta baya ya ɗan yi hugging nata yana ɗora kansa akan bayanta. Alqur'anin da take karantawa ta ajje bayan kamar good 5mints da shigowansa, gashin kansa ta shafa yana me sauƙe wata boyayyar ijiyar zuciya. Jin ta taba shine ya bashi tabbacin takai kejin da take son kaiwa ɗinne domin kuwa tun a farkon shigowansa yaga tana karatun alqur'anin.
"I miss u so much haskena!"
Ak ya faÉ—i cikin wata kalon muryan da yau kaÉ—ai ya bayyana raunina muraran. " and miss u shalelen Hasken haske!"
Kamilallar voice nata ya bugi kunnuwansa,
Ɗan lumshe idanunsa yai yana me jin zallar farin cikin ganinta cikin ƙoshin lafiya.
"Ya yanayin jikin haskena yake?"
Ya jefa mata wannan tambayar kai tsaye, "komai yana ta sake zama kamar a tarihi ne shalele, iyaka kulawanka kaÉ—ai kan wanzar da samun cikakkar lafiyana hasken haske sai dai muce alhamdulillah, tun a nan zaka gane lafiya ba kamar baya ba da nake kan ganiyar hauk........
Kasa ƙarasawa tayi domin ta hanyar toshe mata bakin da yayi, domin a duniya ya tsani jin wannan kalmar daga wurin koma waye bare kuma daga bakinta. "O'ohh kina son zuciyan shalelenki ta buga ne kawai ko J..... Hasken shalele? Pls ki manta komai kamar komai ɗin bai taba faruwaba! Yanzun baga kinan ba darai da kuma lafiyankiba and ya kamata ki goge duka sauran memorie's ɗin daya saura a cikin brain naki hasken shalele right?"
Sake shafan gashin kansa tayi tana jan kaÉ—an ba da yawa ba.
"Alhandulillah Allah alhamdullilah I don't have enough words to thank u or described how am feeling right now after open my eyes and see me in front of the apple of my eyes the favourite part of me"Ak yasake furtawa yana juyowa yayi facing matar yana sakar mata wani lafiyayyen murmushinsa daba kowa ke samun kalansaba. Wani irin hawaye ne ya ziraro daga idanunta sanda taji yasake rungume ta sunfi 1mnt a haka sannan yayi breaking hug É—in yana kama hannayenta yayi kissing nasu.
Chaliey robbot ɗin dake kula da duk wani al'amura na gidan Ak ya ƙira cikin abinda bai gaza 3minst ba sai ga wani saƙagon robbot ya bayyana . wanda shi da kansa ya ƙirƙiri abinsa domin kulawa da lafiyan grennpa nashi domin bai yarda da kowa a fannin kula masa da hasken saba.
Gidane ke6antacce da babu wani halitta da yasan yana da tun a loƙacin da ya kawota gidan. Komai dake wakana a gidan waɗan nan robbot ɗin sune ke aiwatarwa domin gudun kada aci amanarsa, ko'a ha'inceshi hatta da komai da komai sune suke kama daga kan kitchen har zuwa su moping, wanke² dadai sauransu. Da nu'urar jikinsa yayi amfani ya duba abinda yake son ya duba ɗin kana ya sallami chaliey. Babu jimawa saiga rakatun maganan Yesh,tare da zurat sun cika palon, "Ohh god!"
Ya faÉ—i yana me zamewa ya kwanta don yasan halin yesh ba barinsa zaiyi ba shike nan, "Barka da xuwa babban aboki!"Robbot yesh ya faÉ—i .
"Dud!" Ak ya ambaci sunan robbot ɗin yana me cewa. "Pls bansan stress ka barni kona maka filla² Ka tashi a aiki na ƙirƙiri Afuuh, kai ka tashi a aiki okoy?"
Yanajin hakan tun be ƙarasa ba ya ɗauki hanyar barin bedroom ɗin yana daf da fita yace "Battery na yayi sanyi, kana plash nawa yana gaf da samun matsala ayi gaggawar sauyasu tare da charging piont na samu rauni ba dayawa ba kamar yadda nake d.......
"Najiiiiii"
Ak ya faÉ—i yana cewa "bani zanyi aikin ba chaliey zai chajeka!" ita kuwa dama zurat tuni tabar wurin. Daga nan baccin daya kwana biyu baiyi irinsaba yayi wuff dashi, Ido sosae dattijuwar ta zuba masa tare dajin wani mugun tausayinsa, "Kana ganin jarabawa yaro sannu É—an baiwa"
Cikin wani irin slow ya juyo da face nashi suwa kan fuskanta, sauƙo da idanuwansa kan fuskarta yayi kallon ta yake kamar ba gobe a hankali ya motsa bakinsa wanda nima da banji meya faɗa ba? wani guntun smiles ta saki tana me sake gyara mishi Konciyarshi, nan baccin gasken yazo yayi awon dashi.

_Almost 2:37pm
★★★

A nutsensa ciki wannan yanayin na kamewa da muskilanci yake saƙƙowa a saman stairs ɗin, Sanye yake da 3q jeans black sae armless brown.
Hangota yayi zaune cikin babban falon nata hannunta riƙe da mug tana sanye cikin wata doguwar rigar kuwait Jallabiya. Zana yayi a kusanta yana amsar mug ɗin tare da ɗan sipping shayin kaɗan bada yawa ba. "Kafito kenan?" ta faɗi tana kallonsa da kai ya amsa mata domin yana tashi yaji zuciyansa tamay nauyi, Zama kaɗan ya ƙara ya mata sallama ya fice bacin sun tattauna wasu muhimman sirrika.

★★★
_MOH JIDDOH_

"Haba jidd0h Ae tun asali ma laifinki ne da kika bari har ma ya kai tsawon wannan loƙacin muna sponsoring nasa da kinyi duk mai yiwuwa tun a baya kin sa an kawar dashi ne ae yanzu gashinan ya zame mana ƙarfen ƙafa shida shegun ƴaƴan san nan!. Yaufa kimanin 7 days kenan ko ikon ganinsa bamu da bare mu kawo ƙarshen wasan kowa ma ya huta!"
"Bazaka gane ba Hussein na fika jin raɗaɗin hakan dahar na raini ɗan kishiyata a matsayin nawa ɗan! Sai yanzun nima nake sake tabbar dacewa ba ɗan ƙaramin ganganci nayi ba! Amma ba komi anzo ga6ar da dole su kwalba su bayyana domin kawo ƙarshen komai a yanxu bana da buƙatar sake jin komai ko ganin komai fa ce lalacewar family'n _JADDER'N ASHAAN_ Ina son kafin numfashinta na ƙarshe bayar ganganr jikinta ta ɗanɗani ɗaci da kuma azabar da hakan shine zaiyi sanadiyar bugawan zuciyarta. domin kuwa tana ji tana gani ɗan data haifa zaice ba itace uwarsa ba tare da shegun jikokinta. Ina buƙatar yau naje tare dakai domin kuwa shine na ƙarshe kuma ta fito kenan, A gaban idonta za'a harbe kan ɗanta bata ikon hanawa Hhhhhhhhhhhhhhhh..........
Ta sheƙe da wata kafurar dariya tana ƙarasa shigewa bedroom nata.
Chapter 11 · 0% Book details