← Book details Mikiya Part 2 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 7 OF 17

Sashe 7

Mikiya Part 2 Complete Hausa Novel.txt · about 7 min read

Kowa besan da zuwansu ba har sai washe garin ranar domin kowa yana a cikin alhinine, kuma alhamdullih Oum ma ta farka saidai Ak yaƙi bayyanama kowa hakan me martaba kuwa dama tun a daren ya farka. Jesrah ce tama fulani jagora har zuwa ɗakin da Oum take ba tare da Merrah taje ba domin ita kanta jesrah ɗin bata san fulanin tare take da baƙuwa ba.
Ta jima sosae tare da oum É—in kana ta koma kodan merrah data baro ita kaÉ—ai, shi kuwa zayd suraj yana can tare da zaid Emaar's da kuma arms da dama shima yana a cikin masarautar......

_Bayan kwana_

Alhamdulillah zuwa yanzun oum tana shashinta ta warware dama shock ne har yau babu wanda ya sake ganin me martaba AK ya kasa ya tsare a halin yanzun ma yana part ɗinsa. Kuma babu mahaluƙin da yayi gigin zuwa ko kofar sashen. Sosae fulani tayi jinyar merrah kuma itama oum ɗin bawai ganinta tayi ba tunda itama kusan a kwancen take. Zaune suke su duka A ƙayataccen palon oum ɗin domin yin dinner, Ak da zaid ne kawai babu se merrah da ba kowane yasan da zuwantaba ita dama.
Fulani ce ta ɗan dubi jesrah tare da fadin "Kije ɗaki ki tahomin da baƙuwa"
Da mamaki ta ɗan dubi kakar nata tare da faɗin "baƙuwa kuma grenny?"
"Ehhhhhh zakije ko tsareni da idon zaki tsaya na aiki uwarki tunda ita na isa da ita!"
Tsammmm ta miƙe domin tasan halin kakar nasu ba wasa take dasu ba. Babu jimawa kuwa sai gata riƙe da hannun meerah. A sanyaye ta zaune kan kujerar data saura ita kaɗai wacce take fuskantar kujerar da oum take zaune kai tsaye. Gaisar da duka mutanen palon tayi wanda ya sanya oum ta kusan kwarewa da tea ɗin da take sha, wani irin ɗago kanta tayi daidai meerah na sake ɗagowa tana me sake gaisar da oum ɗin ganin kamar ko bata jita bane. Wani irin tarine ya sarƙeta idanunta kafe akan merrah ɗin.
Da sauri zaid ya ɓalle gorar ruwa yana bata a baki tare da dan buga bayanta kaɗan, Mahaifiyarta ta kalla tare da faɗin "Mommah wannan ai DID......
Saurim katseta fulanin tayi ta hanyar faɗin "eat itt, yanzu loƙacine na dinner bana magana ba ok?"
Duk yadda taso ci gaba dayin dinner ɗin kasawa tayi dole itama fulanin ta miƙe tana me mata magana data bita zuwa ɗakin data sauƙa.
Magana sukayi sosae wanda sai faman ɗaga kai oum take tamkar wata kaɗan garuwa, sun jima kafin ta fito tare da kama hannun meerah tana faɗin "Yarinya na muje mu sake gaisawa ki bani labarin ƙasata"
Ita dai merrah cike da kunya duk wannan zafin kan ya tafi nashi wuri na wani ɗan loƙaci.
Itane tayi ta janta da fira harta samh taɗan sake idan ta mata tambaya daƙyar take bata amsa. Amma kuma mamaki sosae take da ganin matar domin ka tsaye fuskan wancan tantirin na ƙasar Nigeria take a face na matar, saidai tasan gari banban Allah ɗaya domin babu ta yacce za'ai wannan kamilallar matar tama haɗa jini da wancan da satar mutane kawai ya iya, kuma ma tasan me zai kawo wancan babban criminals ɗin cikin ƙasar nan kuma ma har gidan sarauta me girma irin wannan. Sallar zuhr itane ta fito da meerah daga sashen oum. Bisa taimakon jesra da kawai taji merrah ɗin ta shiga ranta kai tsaye ta komar da ita har sashen da fulani take.
Itama anan tayi sallar nan suka fada fira bata sake jin ƙaunar meerah ɗin ba sai da taji ashe itama jornalish ce wato ƴar jjarida, Dan duban Fulani tayi fuskanta na bayyana zumiɗinta ta furta "Ayya Mommah dama zaki bar mana merrah anan dan Allah!".
Dake babu wanda yasan da batun auren sai Oum da shi kansa Boss É—in wanda shi harma ya manta da wancan batun na Sarki suraj.
"Gata nan dama ai tazo kenan tunda Yayanki take Aure"
"Da gaske mommah wanne amma akie zaid aka aura mata ko?"

"Abdoul-maleek, dai waye yaje nig a cikinsu?"
Wani irin zaro ido waje Jesra tayi tana rufe bakinta da hanunnunta, "Wai kinanufin Gargalion din Oum ne yayi aure ba tare da mun sani?"
Wata harara fulani ta watsa mata tana faÉ—in "Tunda kina matsayin uwar ne meza hana ki raba auren tunda baki sani ba"
Daga haka ta miƙe tana bar musu ɗakin domin jirgin gobe zatabi Insha Allah ma kuwa.

A ta can ɓangaren Moh jiddoh kuwa Abubuwane suke neman hargitsa mata kwakwalwar kanta, domin Abubuwan da suka faru cikin kwanaki biyun nan zuwa uku. Shin mene fassarar abinda ya faru da ita a daren ranar can? Shin me hakan ke nufi Kenan sanya idon da akama ma hassan Al-hassan ya ninka na baya. Da ita a ranar taso aika shi inda ba'a taɓa dawowa har gaban abada, me wannan nu'urar take nufi kenan wani ya ganta kome? Amma idan tai duna da ganin har yanzu babu wanda ya magantu a kan maganar sai wani sanyi ya ziyarci zuciyarta.
Amma har yanzun abunda ya faru ya gaza barin tunaninta domin kamar tarihi na shirin maimaita kansa kenan, rabo da taji irin wannan yanayin tun a sadda da ɓatar da _AYESHERH_ babbar ƴar sarki Hassan Al-hassan ta farko. A ranar da tabar cikin masarautar a ranar akayi makamancin irin wannan yanayin idan lissafint ya tafi daidai kenan yau kimanin shekaru ɗɗaɗɗai har Hamsin da arba'n da shida kenan. A fili ta furta "me yasa tunanin yaƙi barin raina ne?"
Haka dai tayi ta tunane abubuwa maban banta na mata kai kawo a tsakar kanta.

Zumbir ta miƙe tamkar wacce aka zabura ta firta "JADDERN ASHAAN"

Fita tayi a duhun magrib ɗin cikin shigar ɓatta kama kamar yadda ta saba. Wani surƙiƙin yankakken daji ta nufa na wani shashi daga cikin masarautar.
Tayi nisa sosae ta tsinkayi muryan mahboob ata bayanta yana faɗin "Kai waye wannan tsaya anan, Ko waye kada ya kuskura yayi ƴunƙurin guduwa domin zan saki Nightingale, da Rhino da pig tare da unicorn su yagalgalamin namansa"
Ɓari jikin moh jiddo ya ɗauka cikin tsantsan tashin hankali mara misaltuwa tasan ba shiri take da mahboob ba bare ya fuskanceta,ta kuma san tana gudu zai saki su pig ɗin kamar yadda yayi alƙawari. Cikin dakewa da kuma kame fuska tana dawo da ainihinta na jiddoh ta tsaya cahkkkk. Cikin wani irin shegen tuggu ta taryi numfashinsa tare da faɗin.
"Taya zaka saye da haka ita dama kuskuren kunya ai da hauka ake naÉ—eta, wato fahimta kayi da ina bibiye dakai shine zaka wayance da faÉ—ar haka! Idan baka sakar min suba kaiba haifaffe bane a cikin _ASAAD EMAAR's_ ubanka da yake gudun mahaifarsa dan ubanka da uwarka _SOFIYYERH ANAAN_"

A gabanta yaja ga tsaya riƙe da ƙugu kallonta yayi daga sama zuwa ƙasa kana ya fesar da iska yana me faɗin cewa
"Ai shi ba lusari bane da zai zauna zaman dogaro dana wasu, neman halak ɗinsa yake kinga kuwa babu laifi da bai zauna zaman jiran tsammanin na wani zuciyarsa a tsaye take shi ƙamm Kuma zaman. _ENGLAND_ yan zun ya fara muje kuma ko yanda babu kowa na ɓalla ƙafafuwanki na zubar anan"
"Tirrr da haihuwar É—a irinka wllh Assad ya haifamin masifa har abada jinin uwarka Sofiyyerh da jinin Maryam ba alkhairi bane a gareni masifa ne ku a cikin rayuwata"
Kota kanta baibi ba haka dole don kaucema zargi tabi bayansa suna komawa ta barma gobe.

Washe gari jirgin fulani ya lula bayan ta sake duba jikin me martaba da sukayi magana sosae da shi, Anan ta tajama Ak mugun gargaɗi akan matarshi. Shi kallon basu da hankali daga ita har mijin nata ma yake musu yasan kawai gigin tsufane ya fara kamasu. In banda haka Shi me zeyi da wata mace kuma ai ya ɗauka dan jin daɗi da samun nutsuwa ake yin auren?, to shi kuma duk baya da buƙatar hakan wine ɗinsa tafiye masa komai na cikin duniyar idan aka ɗauke mahaifansa.
Dan haka ko maganar bebe wani muhimmanci ba yace koma wace idan ta gaji da zama tama ware da ƙafarta, Shida kansa ya kaita airpot zayd suraj nta famar tsokanarsa yana cewa kardai daga baya ya kwarema matarsa kuma yazo yana musu mimison goɗiya wllh ubanshi zasuci, haka jirginsu su fulani ya tashi cike da kewar ƴarta........

A gimtae

*BY AMMEY LAYLERH*

*🦅 MIKIYA 🦅*

_A wonderful world & Special anti terroRism squad_
____________________

*MARYAM NASEER MIRRAH*
~AMMEY LAYLERH ✍️~

✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~*

BOOK Two…………………………񆬍✍

7&8

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

# The friendship
# Romance scene
# His bloved_friend Meerah
# Meerah Ak drama's

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
_NIGERA'n_
~Lagos~
Chapter 7 · 0% Book details