← Book details Mikiya Part 2 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 16 OF 17

Sashe 16

Mikiya Part 2 Complete Hausa Novel.txt · about 7 min read

''Duk da ance shi icce tun yana ɗanyensa ake iya lanƙwashi, to amma ni duk da bushe ɗin zan iya lanƙwashin! Idanma ta kama da karyewa to kuwa karyashin zanyi don buƙatan kaina ya biya Moh'' duk da a karkace tayi maganar amma tasan inda maganar ta dosa.
Murmushin gefen baki moh ta saki sai ta É—ago batare da nuna komai ba ta furta "Uhmmm dakyau ki kula sosae wajen lankwasar dai kar yazam mu ta sake kwabewa"
Wani kallo ta jefa mata wanda kai tsaye jiddon ke ankare da ita, itama wani shegen murmushi tayi ita kaɗai tasan abinda take kwancewa da saƙawa.
"Zan kula sosae karkj damu Jiddoh komai zai tafi a tsarinane tafiya a tsarina kuma baya nufin kwa6ewar aiki irin na wasu!"
Kai tsaye jiddo tasan maganar nata ne kuma ta amsa kamar yadda umayman ke buƙata dama, "Aha Allah temaka na ce saimun sake haɗuwa". Dama kamar jira umayman take ko irin wacce take akan ƙayar nan haka ta miƙe zimbir tana barin parlou'rn a zuciyarta take faɗin.
{Mayyar mata kawai kullum tana kan sallaya kamar wata mutuniyar kirki nan kuwa sai shegen iya ƙulla makirci da haɗa tuggun tsiya...}

Tana tafe tana duba wayanta loƙaci bayan loƙaci kuma tana jan tsuka, kamar daga sama kuma sai ganin ƙiran yasmine tayi ya shigo wayanta. Saurin peak call in tayi gudun kada ta katse mata ƙira don tasan kaɗan ne daga cikin aikin Yasmine ɗin.
Daga ta can bangaren cikin harshen larabci yasmine ta furta. "Hala akwai abinda yake tafiya ba daidai ba tunda naga saƙonninki harta email!ok?"
"Loƙacin zamanki America ya ƙare yasmine don loƙacin fara farautane wannan! Amma ya kamata ki taho haka nan my be not my be forever kuma"
"Kina nufin A maleek na Emaar's a yanxun haka Mommah?"
"Yana a harma da tsarabnan wifey a tare dashi"
Daga kwancen da take ta mike tsaye zimbir tare da faÉ—in "Ma me? Kamar fa mata naji kin ambata mom a taya A maleek zaiyi min haka? Shikenan kitsimayi zuwana Later"
Daga haka ta datse ƙiran tare da dafe kanta da taji loƙaci guda ya balain sara mata. "A wannan karon dole ka faɗa hannuna Abdoul-Maleek Emaar's ko kaki ko kaso mata ne bisa kanka wanda ake mana laƙabi da gangar shaiɗan"

_Amma wait! Nidai nace babu ni Ammey Laylerh tare da duk me karanta littafin Mikiya Uhummmmm_

★★★

_Some late_

Karon dataci da wani abu kamar gini ne yasata saurin É—agowa tana yin one step back hannunta dafe da hancinta data buge tare da forehead É—inta amma hancin yafi mata azaba
A hankali ta soma ɗagowa dan son tabbatarma kanta wanda ke tsayen saboda wannan unique ƙamshin da bata ta6a jinsa jikin kowa ba sai jikinsa ɗin.
Kallon kallo sukewa juna ita dashi kasancewar sa mutum mai tsayi sosai kuma dai kunsan tsawon mace dana namiji yanda suke hakan yasa ta koma wata ƴar karama. ''Halan kai makaho ne?'' da ƙarfi tayi maganar dan ganin yanda yawani mata tsaye a gaba tamkar wani bijimin sa. Idan inda suke tsaye yayi magana to shima Ak yayi, jin yaƙi ko tanka mata ne ya sanyata sake faɗin
''Malam nace baka gani ne? kokuwa iccen daka buge baiji maka ciwo ba?'' ta faɗa tana hayayyaƙo may ta buɗe baki kenan da niyar sake magana muryan Jesrah ta dake tahowa ta katseta.

Cikin shegen rainin hankali ya dubi jesrah tare da faÉ—in''dalla malama hold it na ce miye wannan aka kawowa mutane gida'' da sauri jesrah ta duba ak É—in tare da faÉ—in
''Akie Merrah ne fa''
Wani kalan yamutsa fuska yayi tare da furta''miye wani Merrah kuma?'' yanda Yake yatsina fuska kamar yaga kashi ne sake hasala Meerah É—in itama.
''Akiey Matarkane fa wanda aka É—aura ma aure da ita already tuni'' wani irin shegen murmushi yayi yana yuja kai ya tabe baki irin anzo wajen Nan.
''Au cemin zakiy kaskar data maƙale tace saini, wacce tabi duk wani lungo da saƙo don ganin ta shigo rayuwana. Fine amma bara na tuna miki wani abinda basu faɗamiki ba nan gidan ba kowane mara aji ko jani talau ne yake iya shiga ba bar ganin kin samu shigowa fitan ma ba wahalan zaiyi ba kamar shigowanki EMAAR's......
ÆŠagowa Merrah tayi a karo na farko tunda suke tsayen ta kalleshi straight in the eye. Tare da furta.
"Who are you? How dere you?"
Ta faɗi in a low dangerous voice, kafin taci gaba da faɗin. "Saidai gidan ma ai beyi kama dana mutane tunda ba'a daidai ɗinsa yake ba, Kuma a kallon farko ma gidan beyi kama da gidan da mutane ke rayuwa a cikinsaba baki ɗaya duhu da duhuwa ne kewaye da durƙushashshen kangon ginin daya yake a baybay"
Da wani kalan kallo ya bita me kama dana rainin hankalin nan.

"Idan ma dalilin wani abu yasa kika nace saikin shigo gidan nan toh ki sani bakida muhalli a yanzu dan the house is full with children's no more room for you''
Yana faÉ—in hakan ya wuce abinsa bayan ya mata wanna shegiyar alaman datafi tsana fiye da komai daga gareshi. "Babu wanda besan halin Akiey ba so inaga hakan ba abinda damuwa bane dear!"
Taji muryan jesrah tana jan hannunta lips nata taɗan ciza bada yawa ba tana bin bayan jesran don dama wurin oum suka nufa data aiko ƙiranta.
Oum ɗin ta tarar zaune tare da jesrah wacce ta labartama oum ɗin komai daya faru. Cikin ƙarfin halin Oum tace "$higo man Meerah kinzo kin tsaya a Kofa? Zonan kusa dani kinji ta faɗa tare da nuna mata gefen da take zaune,murmushi ta yi tare da karaso ta zauna kusa da itah kamar yadda oum ɗin ta buƙata ta sunkuyar da kanta ƙasa tare da faɗin.
"Oum good afternoon" Murmushi Oum ta saki tare da da amsata da "Lafiya Alhamdulillah baki biyo bayan iyayenki nema zance ns ko kakanni nema"
ÆŠan murmushi kawai meerah ta saki tana jinta a takure da zaman da sukeyi É—in, dan har yanzu ta gaza sakin jikinta da oum don sosai take kunyar matan yanzun ma jinta take kamar ta gudu haka taji aranta.
"Jesrah kuje ku gaida mutanen cikin gidan"
"Tomm Oummuh"
Jesran ta faɗi ko kafin ta miƙe kuwa tuni zaram har meerah ta rigata miƙewarma, kai tsaye bangaren Umaymah jesrah ta fara raka Meerah ɗin. da wannan shegen makircin nata da zagon ƙasa ta tar6esu faran² Allah'n baka. Basu wani jima ba sosae suka mata sallama wasu manyan arabian jallabiya tare da Alkyabba da turaruka masu tsada sosae ta haɗa meerah dasu. Ko kallon kayan batai ba jesra ne ta amsa tana mata godiya.
Daga nan bangaren Moh jiddoh suka yi a loƙacin tana zaune ne akan caution tayi crossing ƙafafunta tana karkaɗasu idanunta a lumshe ita kaɗai tana aikin saƙawa da kwancewa. Wani kalan buɗe idonta tayi tare da juyowa zuwa wani mummunar faduwa gaban moh jiddoh yayi zuciyarta ya shiga harbawa da sauri-sauri idanu ta rufe ganin wani irin haske mai bala'in karfi ta cikin idanun meerah ɗin batayi auni ba taji muryarta na cewa
"Innalillah wa'inna ilaihir raji'un meke shirin faruwa dani ne haka ni jiddoh yau na shiga uku!"
Da sauri jesrah ta fita a ɗakin tana cema Meerah tana ɗan zuwa don wayan da aka ƙirata.
Wata nannauyar ijiyar zuciya Moh ta sauƙe tare da furta "wllh shegiyar yarinyar nan tsoro ta bani kodan jinin mayuce masu shegen ƙarfi jinin tsiya tirrr dai wllh har abada ba'a taba sarki biyu a guri ɗaya" tayi maganan tare da buɗe idonta ba kuwa su faɗa ko ina ba sai cikin na meerah. Baki ta buɗe mata tare da daƙune fuskanta sai kuma gata zaram akan jiddon.
"Da kina yarinya bakiy karatu bane? Cokali ɗaya na nonon sa yafi daro ɗaya na nonon jaki, uhmmmm dama saida nai tantamar ba'aje makaranta ba. duk aukin jakuna ba zasu taba kama ƙafar doki a gudu ba. Kuma har abada zakara shi kaɗaine sarki Moh ɗinmu ta ƴan gayu"
Ta waske abinta tana kamar gyara mata rufin hulan kanta tayi ganin shigowar jesrah. Saƙeƙe haka moh tayi tana me bin meerah da ido kawai fakar idon jesran tayi tare da ƙyafta mata ido ɗaya da kashewa. "Ina ganin mutafi haka nan ko dear?"
"Ehhhhh hakan ma yayi. Moh sai haɗuwa ta gaba yanzu ta wuce sauri muke ki kwana cikin sauƙin zuciya Allah kuma yaja da ranki kisha kallo my kakas"
(Yau naga yadda ake bariki ni mai jiddah, to kodai akwai abinda yake ba daidai ba ko yake a baybay bana da masaniyar hakan kuma?)
Ta ayyana a zuciyarta tana jinjina ƙarfin halin yarinyar, {kai ina wllh ma tana da aljanu yarin yarnan}
ta sake maimaitawa tana faÉ—awa bedroom nata.
Haka Moh ta kwana datunanin abunda ya faru tsakaninta da Meerah sosai abun ya tsaya mata a rai,tunda take bata ta6a ganin makaman cin haka ba a iya tsawon rayuwarta duk me hakan ke nufi?, ya zama dole ta shirya ma zuwan waɗan nan jerin abubuwane ma zata ce ko ƙaddarori ne ma oho da wanan tarin tunanin bacci ya ɗauketa.
Chapter 16 · 0% Book details