Sashe 17
Mikiya Part 2 Complete Hausa Novel.txt · about 5 min read
A ta bangaren meerah kwana tayi da tarin abubuwa maban banta wanda suka farun min dama wanda suke kan faruwan. RuÉ—ani,mamaki, al'ajabi sun taru sun hana Meerah runtsawa a wannan dare. Kanta ya gama kullewa dangane da abinda duk suka faru É—azun tsakaninta da Moh da kuwa wannan Aljanin. Shin mutumin nan É—an dabar ne da gaske? Kokuwa wani abu daban da bata sani ba. Babu abinda ke mata kaikawo a zuciya sai kalan yadda ya ringa yaba mata maganganu da kuma haÉ—uwarsu na jiya daya bita har É—akin ta me hakan ke nufi kenan?
Ita kam al'amarin wannan gida ya fara birkita mata lissafi tun a farkon shigarta komai ya gama bayyana kansa gareta.
A lissafin ta dai Moh jiddoh itace uwar masu gidan to amma ta ya ya Akai ta kasance me fuska biyu. Abubuwa sosea ya hango tattare da matar baƙaƙe ba masu lissafuwa ba. Zuciyarta a ƙone take babu ko ɗigon rahama idan har lissafinta ya bata daidai Kenan 6atar da Annenta akayi a cikin wannan masarautar? A tunaninsu ita ƴar gidan ce kenan miye silar mutuwan matan me martaba ga biyu? Zancen daya faɗa a baybay ita tuni ta gama fayyace abinta filla filla tun a ranar. Kuma ita kaɗai tasan abinda taga ni ta kuma ɗaukarma kanta alƙawarin bibiyar kowa da kowa na wannan masarautar har zuwa kan dalilin da yay bacewar annenta. Kenan Anne ita bama ƴar nig bace Sarki Ash dai shine cikakken mahaifinta Allahu ahaad lallai Allah da girma yake.
? Sai wajajen ƙarfe biyun dare bacci yay ciki da ita cike da tarin wasu mafarkai masu ban tsoro.
A hankali hasken rana ya bayyana a sararin samani.
Wanda haka yayi dai-dai da farkawanta tare da bayyanan ciwon da taji maranta ya harba mata, ya mamaye duka har sassan jikinta da zuciyarta.
Wani irin rumtse idonta tayi tare da tashi zaune cikin wani irin gigitaccen ciwon da ya mata dirarn farat É—aya tace.
"Sheehhhhhhh Wayyo! wayyo!! wayyo Allah Anne na ciwo zafi wayyo Raiha wayyo kowa da kowa na cikin duniyar ma baki É—aya. Wayyooooo"
Ta faɗi da ƙarfin daya farkan da jesrah a zabure don babu jimawa da komawansu bacci bayan sunyi sallar subhi.
"Subhanallahi Aunty meerah mike faruwa?" ta tambayeta cikin muryan bacci tana mikewa tare da nufo wurinta, wani irin juyi haɗi da murƙususu meerah keyi wanda hakan kai tsaye ya sake firgitar da jesrah kai tsaye ta fita a dakin da gudunta domin sanarma da Oum.
★★.....★★★
A ta bangaren umaymah tun a daren jiya ta gama shirya komai na tarbar dolky'nta tun daga kan abincin da takeci har zuwa tsaftar sashen ma a yau ta kasance ta musamman duk da a kullum a tsaftace yake. An shirya kalolin abinci da ƙamshinsu ya gama cika ko'ina na sashen har maƙwaftan shashen ma ka iya jiyowa. Duk ata dalilin son ta farantama dolly'n.
A mugun guje rantsatsiyar baka wulik ɗin lafiyayyar motar da dolly ke ciki ta tsaya gab da ƙofar shashen umaymah, cikin rawar jiki ɗaya daga cikin Hadiman ya buɗe mata motan, sauran kuwa tuni sun zube ƙasa kan gwiyawunsu kawunansu a ƙasa domin kai tsaye sun san dokar madame dolly'n DA'DAH. Tun a farkon shigowan motanta kuwa cikin Mention ɗin hadima suka dinga tsere don gujema haɗuwa da ita bare takai ga yi mata laifi.
A ƙalla taja Sama da mintuna goma batafito ba duk da kasancewar an buɗe mata, sai da taga dama dan kanta sannan ta ziro ƙafarta fara tas dake a cikin ƙyaƙyƙyawan blue ɗin takalmi mai tsananin taushi da ɗaukar ido da zai iya birge duk wani mai kallo, Wanda yaci uban naɗi da igiyoyin dake jiki, kusan sakan biyar a tsakani sannan ta ƙara zuro ɗayar cike da ƙasaita.
Tashin ƙamshin turarenta da takun sawayenta ya tabbatar ma duk wani rai mai numfashi ata bangaren isowarta. Wanda hakan kai tsaye ke sanya su rusuna kawunansu ƙass gudun haɗa ido da ita kayi laifi. Cikin wani shegen taku take wucesu hancinta ɗage a sama tana wani huhhurashi sama ita ga ƴar zafin kai.
Wasu shegun ɗamammun riga da wando ne a jikinta na jeans iya ma'alwantarta kan nan naɗe cikin swear band me shegen kyau da tsaɗa, da wani irin maɗaukakin farin ciki umaymah dake zaune ta miƙe tana rungumar yarin yar nata.
Kafin da hannu taima dukkan amintattun hadimanta dake zagaye da ita nunin su fice. Har rige-rigen bin ƙofar da zata kaisu falon farko dazai fiddasu ta ainahin ƙofar sashen nata suke. "I miss u my dolly'n Dada"
Wani iska taja tare da jan numfashi ta fesar a hankali.
Idanunta ta ɗan ƙankance da jinjina kanta tana sakin ɗan karamin murmushi domin Dada ɗinta da tafi kewa fiye da komai har ita kanta momman kuwa.
Ita kuwa Umaymah da take jin duk wannan ranar tanajinta rana ta musamman ne a gareta, sakar mata kiss a goshinta haÉ—i da zaunar da ita tamkar bata baby.
"Mommah Kina lafiya?".
"A zahiri dai lafiya nake, amma a baÉ—ini cike nake da tarin damur dake cinkushe a raina first"
Umayman ta faÉ—i fuskanta na sauyawa daga yanayin farin cikin da take ciki zuwa kishiyarta.
"Uhhm!" Yasmine ta faÉ—a da É—an lumshe idanunta ta buÉ—e Still a lokaci guda.
"Kai tsaye ki faÉ—in damuwar don nima yanzun haka a cikinta nake saidai jin wannan lamarin ya shafe wancan É—in don shi serious bane kamar wannan É—in"
Kai tsaye ta ɗan tsaƙuri lamarin a ciki ta bata. Idanunta a lumshe suke buɗesu tayi tare da fesar da numfashi ba tare data bata amsan tambayar data mata ba ta furta.
"DADA fa?".
Tay maganar a fisge tamkar yinta ya zama tilas ne a gareta. "Yana mashel kotra" Wani kalan zaro idonta tayi wanda suke a bugu wanda kai tsaye inkai mai fashimtane a take zaka fahimci ba'a daidai suke ba.
"Be dena zuwa Mashel kotra ba har yanzun kenan?"
???...........
*BY AMMEY LAYLERH*