← Book details Mikiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 45

Sashe 44

Mikiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Du inda ka gimla ta cikin shilton hotel ɗin sautin Night music ne ke tashi. Wata iriyar badakalar rawa ake gudanarwa a cikin hotel ɗin. Duk wasu ƴaƴan manya kuwa wanda basu samu halartar sauran shagulan dasu Salman suka shirya ba to ayau kammm sun sami isowa, domin na daren yau din shine shakundum.
Wadan da manyan yara suka shirya ma Salman ɗin ♡BACHELOR's NIGHT✩ duk wasu ƴan gang bang nasu masu ji da fatu da tsantsar wayewa suna cike a wurin. Kallo ɗaya zaka ma wurin ka gane Are not my kind of people domin bana kowa da kowa bane.
Kowa ka kallo yana tare ne da Ben ɗinsa suna kwalɓewa a tare wasu kuma Romance na junansu suke. Kamar yadda uban gayyar da yake tare da dolly ɗinsa da suka shirya tun daren jiya, yanzu ma rungume suke da juna daga shi se wata shegiyar fit out ɗin riga da wani guntun wando, gaba ɗaya gaban rigar a bude yake sai sake shigar da kanta da babu ko wula take. Kwalbar wine ce a hannunta idan tasha saita bashi.
Daga nan surar ta yayi suka faɗa wani bedroom wa'iya zubillah, babu ruwandu da jama'ar dake dakin wanda suke aikata masha'arsu. Suma wani wurin daban suka faɗa........

★RANA BATA ƘARYA

Masu iya magana suka ce wai Rana bata ƙarya sedai uwar ɗiya taji kunya.
Ni Meerah Ayau nafi kowa yarda da batun domin kuwa nima da kaina na yarda wannan rana tawace kam. Domin A yau gidanmu cike yake taff Yan uwa na kusa dana nesa duk sun gama hallara kansu. Ta ko ta ina hayaniyar ƴan bikice kawai ke tashi masu farin ciki nayi haka basu baƙin cikin ma duk nayi. Ga tarin abinci kala-kala da ake ta hidimar yi saidai kash! Babu dangin Anne'nmu ko ɗaya. Sai Hajiya umma kawai wanda za'a ƙira da dangin Anne'n sai kuma mutanen da ake mutunci dasu.
Zai wasu ƴan ƙananun gulmace gulmacen dake tashi wai babu abinda Anne tayi tanadi na biki. Tanaji tayi shiru ta share su domin ita sammm wannan ba matsalar ta bace, Ni kuwa Ina cannn kuryar ɗakin Anne'n zaune cikin shigar wani mayen leshi maroon color's.
  Wanda yay masifar fitowa dani sai na tashi tamkar wata irin jinin larabawan nan ko kasashen ketare, ga gyaran da aka min ya sake tsatstsafo da zallar kyawuna na asali sosae dan ba ƙarya Anne tayi ƙoƙari ba lefi ita da Hajj umma. Acan ƙasan zuciyata kuwa jina nake duk wata iri kamar yanda aka san duk wata amarya da shiga irin wannan yanayin a irin ranar Ranan. gefe.Shigowar Disha da wasu kawayena suna rangada min guda aka shine ya sake sanyaya jikina sai kace ba wannan meerah'ɗinba ƴar zafin kai. "Allah yayi an daura amarya a gidan Salman, Ni zaki fara Bama wannnan kwallelen farin goran albishir ɗin"
Ban sake tsinkewa da lamarin ba Saida naji shigowar babban yayanmu yaya Ibrahim. hakan shiya sake tabbatar min cewar shikenan an ɗauro auren. gabana sai ya shiga wani irin luguden daka da sauri-sauri wani irin tsoro da fargaba na ratsa min cikin ɓargo da duk wata magudanar jini ta jikina. Shikiyancin da su disha sukaci gaba da min tare da guɗa a saman kai shine ya sake tattare duk wata nutsuwa data saura wa jikina. Sai na samu kaina da sakin hawaye masu zafin gaske da ban san dalilin yinsu ba, domin na gagara banbance komai a yanda ya dace na fahimcesa wanda kai tsaye Ni zan iya kiransa dana baƙin cikin zama mallakin Salman da nayi a wannan rana. Bugun da zuciyata taci gaba yine ya sanya ni lumshe idona a take wasu hawayen suka sake sakkomin. Shewa da dariya suka shiga min suna cewa duk hawayen farin cikin mallakar Salman ne ai hawayen. Ni kuwa ni kaɗai nasan kalan yanayin da nake ciki. Ya tabbata kenan ƙaddarar wani sabon fejin ta sake buɗe min? Ganin kuma yanayin sanyin nawa yayi yawane ya sanya su disha kyaleni, batare da sun fahimci kamar akwai abinda ke damuna ba don sun dauka ƴan izzar ne a kusa.
Daga can tsakar gida kuwa taro yay taro gida ya sake kacamewa da hayaniya irin ta biki, Wasu na hotuna wasu na kwalliya wasu na hirarsu haka ma masu aikin abinci nayi. Bayan daura Aure da kamar mintina ashirin baffanmu ya ƙira Anne, bata ɓata loƙaci sosae ba ta dawo fuskanta da ɗan sassauci ba kamar kwanakin bikin ba. Nan abokan zamanta suka shiga kus kus a tsakanin su bayan sun gama gulmar wanne irin sulun bikine da babu dangin mahaifiyar amarya, a loƙacin ma Saida Aunty labiba babbar ƴar Hajiya umma ta taka musu birki kana suka shiga nutsensu. Domin kowa ya san labiba bata da mutunci kona miskana zarra.
Nan akaci gaba da shagalin biki kowa be tsinke da lamarin ba Saida Anne ta fito cikin wata rantsatstsiyar shigar farin less. Howowo zanso ku hango yadda Anne ke walainiya cikin danyen leshin data dautsa.
Mu kuwa muna can uwar ɗakan Anne wajajen lassar la'asr Aunty labiba ta shiga tare da aunty adawiyya da baby autar Hajiya umma suka shiga niki niki hannuwansu dauke da wasu shegun bags har guda uku. Badan kar ace na fiya kyauyanci ba dana rantse ban taba ganin kome kala da bags ɗin ba. Zama suka yi fuskar ko wannensu dauke da murmushi a fuskarsa.
"Amarya ya kamata ki sanjà shiga ga sabbin kayanki da Anne'nki ta sai miki na fitar biki su zaki sanya"
Ijiyar zuciya na ɗan sauke inajin yanayin bugun zuciyana ya sanjawa tare da cinkushewar yanayin dana tsinci kaina a ciki.
"Amma aunty adawiyya wannan shigan na jikina ma ai babu laifi nake ga, nifa bana gayyar kayan zafin nan!"
Meerah ta fadi tana miƙewa tsaye banɗakin cikin dakin ta shiga alwula ta dauro kamar yadda aunty labiba ta faɗa. Nan kowa ya shiga yin alwular muka gabatar da sallar la'asr. Bayan mun idar aunty baby ta shiga tsara min kwalliya a fuskana duk da banso hakan ba. Gashin kaina da shi kansa nasa gyaran na daban ne aunty baby tama wani irin style. Ta raba shi biyu ta kai har karshen ƙeyata wanda ya sauka har gadon bayana wasu shegun style ta shiga yi da gashin. Saida ta kammala kana ta sake nado shi da ribom's. Wata fitinanniyar riga da sket half bubu na wani shegen luxury catton less, irin me haɗe da jakar nan ta tamarmi sai mayafinsa. Wasu shegun barima me kama da diamond ta sanya min tare da zobenta da agogon hannu. Ya subhanallah a take wani irin kyalkyali ya shiga tashi a jikina. Ga wasu Mayun turarukan da ban taɓa jin koda irin ƙamshin su ta shige ɓarinsu a jikina. A take dakin ya ɗauki sowar kawayena jan hannuna aunty labiba tayi tana faɗin ALHAMDULILLAH sai gaban Anne da baffa har dama wanda basu so ganin wannan babban rana ba, namu ba irin nasu bane.
Ina sanyo kafata tun bai kai ga fitowa ba duk wata jama'a dake tsakar gidan suka zubo idanuwansu a kan bakin kunshin daya wani irin sake fidda kyawun kaɗana. Kwallace take kokarin zubo min ganin tabbas waɗan nan mutanen sun taru ne a yau domin ni, hannuna aunty labiba ta janyo tana karasa fiddo ni zuwa tsakar gidan. Wani irin tsitt duk hayaniyar data kacame gidan a ɗazun sukayi. Ko wanne idonsa na kaina, harda masu sake mitsirtsike idanuwansu.
Wata babbar guda Hajiya umma ta saki tana cira hannuwana sama tare da sake ranbada gudarta tana faɗin.
"ALHAMDULILLAHI! ALHAMDULILLAH!! ALHAMDULILLAH!!! Yarinya tayi goshi Ubangiji ya baki zaman lafiya tabbatacciya a gidan aurenki MEERAH, Allah ya kare ki daga dukkan sharrin masu sharri. Allah ya tsoka ne idon makiya akan wannan auren da Allah ne ya hada shi, bawai mutum ba saidai Allah Wllh kuwa mutum din zaija da ikon Allah to bismilla!"
Duk wannan abin ciki daga murya Hajj umma tayi nan fa wasu suka sha jinin jikinsu domin kaff ya'yan baffa mata babu wanda yaba Anne ko gudun mawar nera biyar. A cewarsu a gudun mawa karin ƙarfin biki.
Nan marasa kunyar cikin su suka shiga amshe Hajj umma suna shiga tare da jeruwa da meerah ɗin aka fara buga photuna na garari. Babu kunya Anne ta rungume DIDI'ƊINTA aka musu photos da yawa. Nan manyan yayye maza ma suka shigo akaci gaba da hotunan Raiha ce nanuke da meerah duk inda ta yi cikin tata shigar na cotton less.
Nan fa gida ya sake ɗaukar hayaniyar data fi ta ko yaushe kawayena kuwa sunyi cannn ta bayan kewayen gidan sun kafa party tare da shan disko harda mardiyya da bama shiri, dake dama rashin shirin akan hayatuddeen ne saita sauke ta shigo ake shan shagalin da ita. Wajajen sallar magariba kawaye suka fara mitar basu ga ango yazo ba bare ayi zancen photo dake baby na tare dasu sai tace musu ai suma suna da party'n da suke yine da an daura auren shi yasa bai zoba.
OHO nidai bansan abinda ake ba domin ina cennn ɓangaren baffa wani zazzafan zazzabi ya rufe ni tun ina dauriya har Saida ya kaini ga kwanciya. Nan baffa kuwa ya sameni da nasiharsa na komai naga ni a lamarin aurena tabbacecce ne tun daga rabbi izzati, karna yadda nayi jayayya da hukuncin da Allah yay min. Kana karna taɓa butulcema zabinsa na zama mace mai tsananin haƙuri da biyayya a gidan aure na Insha Allah zanga sakamakon auren nan ko bayan babu ransa. Abinda ya sake sanyaya jikina kenan sai kaina ma ya soma sara min.
Chapter 44 · 0% Book details