← Book details Mikiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 45

Sashe 34

Mikiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Saida ya buɗe deep freeze ɗin dake makale da dab shiga asalin living room ɗin ya ɗauka kwallar wine ɗin sa. Nan ma Saida Gellary odyssey dpy ɗin yayi on locking up nashi kana ya suka shige Mahaukacin katon parloun da ma'adanar cctv footage ɗinsa yake. Wani irin matakan tsaron na'urori ne kawai ke magana a wurin.
Tanbuwal da tun da aka jeho hi aka garkamesa jiya be kuma sake jin motsi ba sai yanzu. Da wani irin sauri ya sanya hannunsa yana kare Mahaukacin hasken daya kusan ɗauke ganinsa, jikinsa rawa ya fara na tsabar azabar yunwar dake kwakular cikin sa.
Zaune yakai kan Chiar silinder caution ɗin dake facing da wannan mutumin. Ƙafarsa ya sanya tare da mirza ƙafar tanbuwal babu shiri ya saki wata ƙarar azaba cikin tsananin wahala ya furta.
"Pls kuɗin su waye ku? Me kuke nema daga gareni?, Kuɗi!?, Suna?, Mulki?, Ko kuwa ƙarfin Iko kuke da buƙata?"
Ya faɗa cikin muryan jigatuwa da wahala.
Shiru babu alamun amsa hakan ya sanya shi sake faɗin "please let me know waye kai?"
”Makwamishin guba! Mashekin rayuka matunzirin ruhi. Sannan kuma mai kare mabuƙata! Ni dabaibaiyi ne me harɗe duk kan wani azzalumi na kaishi har kasa ÆK”
Ya furta a fusace tare da kwance ɗaurin da akama tanbuwal ɗin. Wani irin mugun shock ne ya ziyarci ƙwaƙwalwar tanbuwal, AK AK AK haka sunan shi ya shiga masa amsa kuwa a tsakar kansa. Cikin Wata iriyar jarumtaka tanbuwal ya sheƙe da wata mahaukaciyar dariya kafin ya dakata. Cikin Wata irin dangerous voice ya furta.
"Ai baka cika cikakken NAMIJI ba tunda Saida ka hada hannu da mace kafin kawoni i zuwa gare ka,karkaga ina karkashin ikon ka ka zata zaka iya min wani abu.
duk da cewar zaki shine sarki a dokar daji amma karka manta damisa itace gwana wajen iya farauta"

Wani irin lalataccen kallo Æk ya wurgama tanbuwal tare da Crossing ƙafafunsa yana kora kwalbar wine ɗinsa. Cikin wani irin hosky voice ya ce.
"Ko wanne mafarauci garzone har sai sanda ya fuskanci ingarman zaki.
Wannan haushin ƙaramin kuykuyon kare kake! Ka sani haushin ɗan ƙaramin kuykuyon kare kuwa ba gurnanin damisa bace! Ammah Ka jira hasalin yadda gurnanin ta yake. Ka sani ABDOUL-MALEEK ba kamar sauran sharar daka saba takewa bane, wannan Asalin Cikakken fusataccen damisar daya fito domin farauta ne a gabanka"
Ya fadi tare da rotsa kwalbar wine ɗinsa kwalbar tai ratsatsa ta baje a wurin. Zuwa loƙacin babu komi a tare da Ak sai asalin fusatarsa kawai ake iya hangowa.
Armstrong dake tsaye ne ya tunkari inda tanbuwar ɗin yake tare da soka masa allura a gefen yuwansa Yana bin bayan Ak ɗin shima. Bai tarar dashi a main sequence parloun gidan ba, wayarsa ya fidda tare da tambayar su Boss ya fito ne?, Tabbacin be fito ba suka bashi hakan ya sanya shi sauke wayar tare da bin ko wanne entrance door da kallo.
Wani irin zafaffen numfashi ya fesar tare da tsananin tausayin uban gidan nasa. Kabar ƙasar ka kabar gidanku kabar danginka kazo ƙasar daba taka ba kana musu aiki da dukkanin zuciyarka da rai da ruhinka. Ko dan wannan abin ma bai ci ace gurɓatattun cikin ƙasar Nigeria'n sun sauya ba da kunya ma ace an rasa gwarzo zakwakurin da yake tsaye akan ƙasar sa. Kodan sun riga sun sanya tsoro ne a zukatan al'ummar OHO? Duk wani namijin da yake jin kansa da zafin kansa ta kawo akan ƙasar to kuwa Insha Allah sai an san yadda akayi aka kawar da wannan mutumin. Shin me masu kuɗin duniya da masu mulkarta suke son zama ne???. A kullum shine tambayar dake bisne cikin zuciyar Armstrong. Shi kikakken ɗan Nijeriya ne amma baya alfari da hakan saboda gurɓatattun cikin ta da ɓata garinta suka kewaye ko ina na cikin ta. Kasar data zamo koma baya ko lissafinta ba'ayi a cikin duniya.
A cikin gidanku ma babu adalci bare akai ga wani wuri me nisa, a gaban idonsa dangin mahaifinsa da suke ƴan uba suka sanya wuƙa suka yanke makogwaron mahaifinsa sa!, Akan dukiyar da guminsa ne shima ya bashi ba sata yayba ba kuma haram yabi wajen tara taba. To taya muke tunanin duniyar mu zata gyaru a cikin gidajenmu babu adalci? Sai tsananin azaba yakai tsanani mu dinga ƙiran Allah gyara. Tofa baya gyara ba dole muma sai mun gyaro ɓarnar dake cikin gidajenmu. Bawai Ƙasarce a ɓace ba mu al'ummar cikin ta mune a ɓacen mune ɓatattun dole kuma dama gyara ta cikin gidajenmu yake farawa. Idan muka gyara halayenmu sai Allah ya gyaramu Amma muma muna da kaso mafi girma akan tarin abubuwan dake faruwa da kasarmu uwarmu......
Wani irin zafaffen numfashi ya furzar tuno yadda ƙanwarsa ƴar shekaru uku a loƙacin take kuka tana dukan ƙirjinsa tana ƙiran mommy na daddy na. Gaba ɗaya jininsu ya ɓata jikinta. Wasu hawaye Masu zafin gaske ne suka zuba masa a lokacin daya tuna sadda mahaifinsa ke faɗin.
"Ka gudu! Ka gudu kai da ƙanwarka ka tabbatar kun rayu ABDOUL-MAJEED, ka reni zuciyarta akan gaskiya da gaskiya ka tabbatar ka kulamin da RIYYERNERTOU, ka zama gatan ta,haskenta, ita kaɗai ce danginka ƴar uwa ɗan uwa ku tafi ka tafi wata duniyar kaje zaka rayu tare da tsarkakkiyar zuciyar da zata reni taku zuciyar da irin tashi zuciyar da ɗabi'arsa.kamin alƙawarin zaka zamo mutum na farko da ƙasar sa zatayi alfahari da shi...
Wadannan sune kalaina na karshe da suka tsaya masa cakkkk acikin tsakiyar ƙirjinsa. Mahaifiyarsu kuwa ta mutu ne ba tare data iya furta masa komi ba sai idonta dake kan Riyya. "Ka gudu karsu dawo su sameku domin a zatonsu kuna makaranta ne, yanzu haka sun tafi ne da niyar su dauko ku kuma su kashe ku. Wannan kuma shine babban zunubi mafi girma da zasu aikata idan har suka taɓa lafiyar koda ɗaya daga cikin kun!........... Be ƙarasa maganar da yake shirin faɗar ma rai yayi halinsa haka ya ɗauki RIYYERNERTOU akan shoulder nashi ya gudu da ita. Sun sha matuƙar walahar gaske har tsawon shekaru uku a lokacin yana shekara na goma sha biyar ita kuma riyya tana da shekaru bakwai. A haka wani baƙin dare ya riski rayuwarsu shida ƙanwarsa.
Daga nan babin sabuwar rayuwarsu ta fara shida ƙanwarsa ta hanyar keta mata mutuncinta ta hanyar mata fyaiɗe Anyi Raping ɗin.
Masu iya magana sunce ko wacce ƙaddara tana da nara madubin,sudai nasu madubin Ak ne domin a lokacin da yake tsaka me wuya cikin mugun yanayin makauniyar ƙaddarar data riski ƙanwarsa. A daidai lokacin Allah ya kawo masa Ak shine ya shige masa gaba akan komi! Shine yake amsa sunan UWA UBA a gare su shida ƙanwarsa har kwanan gobe da safe. Ya basu tarbiyya ya inganta rayuwar da tarin ilimin addini da na boko. Ya shige musu gaba wajen ganin sun zama wani abu A koda yaushe Har abada abadan abada ABDOUL-MALEEK KUWAIT shine kashin bayansu.
Hawayen tausayin gwagwarmayar rayuwarsu da suka fuskanta ya share ya nufi entrance door ɗin da yake da tabbacin anan Ak ɗin yake. Shima ɗaya daga cikin room din ya fada yana kokarin ganin ya kawar da tunanin dake kokarin zeroying maid nashi.
Duk kokarinsa nason ganin ya kawar da tunanin dake neman addabarsa abin yaci tura, kansa ya jingina da jikin kofar tare da lumshe Idonsa. Numfashi yake fitarwa Ahankali yayinda yake furta kalmar. " Innalillahi wa'inna ilair raji'un,² Ya hayyu ya qayyum" daga cikin zuciyarsa domin kuwa tsabbb komai din da yake gudun ya faru ya rigada ya farun. A take kwakwalwar kansa ta nemi juyewa amma ambaton sunan Allah da yake hakan ya sanya. Ahankali nutsuwa ke saukar masa acikin zuciyarsa yayinda yaji tarin damuwarsa na gushewa.sosea yaji sanyi da cikakkiyar nutsuwa da salama acikin zuciyarsa.
Gaban fridge bottle water ya nufa kai tsaye tare da ɗauko bottle water ya ɓalle murfin, ya kafa bakinsa Saida ya tabbatar ya shanye ruwan dake ciki tsabbb kana yayi wurgi da gorar. Wata iriyar ajiyar zuciya yake saukewa tare da sanya hannu ya ya dafe kansa. duk yanda zuciyarshi taso sanya shi dogon nazari yaki aminta da hakan haka kuma yaki bama brain nashi daman yin tunani kamar yanda ya saba a wasu lokutan.
Ya jima a tsayen da yake kafin ya nufi bathroom, ya sakarma kansa ruwa Ya ɗebi mintoci kafin ya fito jikinsa na faman ɗigar da ruwa, mini towel ɗin dake rike a dayan hannunsa na aikin tsanewa.
Wani farin trouser ya zira da t-shirt ita ma farar directly ƙroom din daya tabbatar da ak din na ciki ya nufa, tare da danna door belt din bedroom din yana jiran a bashi umarnin shiga.
Chapter 34 · 0% Book details