← Book details Mikiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 45

Sashe 16

Mikiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ya sake tambayar mahaifiyar nashi cikin cukurkuɗaɗɗen English nashi. Idanunta ta ɗan lumshe kafin ta miƙa mashi kyakkyawan farin hannunta, noƙe nashi hannun yayi a bayansa tare da furta.
"Ohh ohh Papa na" ya faɗa cikin sakalci tare da noƙe kafaɗa.
Da hannun tamai nuni da wani tsararren room wanda yafi kama da ɗakin tan garan Domin an kawata room ɗin ne da wasu shiles row glasses tamkar irin gidan lantarkin nan.
A zafafe ZAID ke taka ƙafafunsa yana tafe yana fesar da numfashi ta cikin bakinsa kansa ƙasa yana tafe cikin sassarfa. koda wasa bai yadda ya ɗaga kansa ba bare ya kalli irin yadda uban kuyangain ke zubewa ƙasa bisu gwuiwowinsu. Shifa sammm koda wasa bai ƙyaunar duk wani abu daya dangaci sarauta ya tsani gaba ɗaya calture nasu komai a takure yake yinsa. So shi yasa sammm Allah bai haɗa jininsa da wannan sarautar ba shi mutum ne da yake son yayi rayuwarsa yadda yake so.
Da wani irin sauri yakai gwuiwowinsa ƙasa tare da kafe mahaifinsa da lulu eye's nashi da suka sosae ganin yadda jikin PAPA'N ya koma loƙaci guda.
"PAPA?" Ya ambaci sunan mahaifin nashi cikin wata iriyar raunatacciyar murya. Tare da ƙoƙarin kai hannunsa jikin PAPA'N shi.
Da wani irin Mahaukacin mari yaji ya ɗauke kyakkyawar Innocent face nash, amma tsabar jinin sarautar dake yawo a gaba ɗaya ko wacce magudanar jini ta jikinsa ya sanya ko gezau be yi ba.
"Kada ka kuskura ƙazamin hannunka ya taɓamin tsarkakken jikin ɗan UWA na" muryar 2wins ɗin mahaifinsa ya katse shi a kausashe a karo na biyu da yake kokarin sake kai hannunsa jikin PAPA'N shi bayan uban marin da MOH Ta bashi.
Da wani irin mugun gudu *JESRA* ta kulle idanunta cikin kunar zuciya.
A nutse Zaid ya ɗago da kansa zuwa ga baki ɗaya jama'ar parloun.
EL-HUSSAIN wanda ya kasance biyunini PAPA'N shi, sai MOH JIDDO wadda ta kasance mahaifiyar su PAPA'N shi.
MAHBOOB,DAWOOD, MUZAFFAR, MUSADDIQ, AL-MUSTAPHA, MANDOOD, EYESHA, MANSOOR ,REYNA.
Sune a room ɗin baki ɗaya wanda mafi yawancin cikin su ke binsa da wani irin mugun kallo, kallo ne irin na tsantsar tsana suke binsa dashi.

A...MALEEK.....
Idan baiyi ƙarya ba kamar haka Papa ya ambata saman laɓɓansa ko takan jama'ar da suka ma room ɗin ƙawanya bai biba ya haɗe fuskarsa dana mahaifinsa sa. Ta ƙarfin bala'i ZAID ya furta "ABDOUL-MALEEK?"
Wani irin razanannen kallo mafi yawancin ɗakin suka shiga bin ZAID dashi. _ABDOUL-MALEEK_ kowa ya shiga maimaita wa cikin zuciyarsa har jikkunan wasun na ɗaukar mazari, sunan da Ambatarsa kawai tashin hankali yake haifar wa, sunan da jinsa yake tada hankula bama hankali, sunan da suke ɗaukar sa wani shuɗaɗɗan al'amari a cikin tarihin rayuwar su.
_Tasssss_
Wannan karon EL-HUSSAIN ne ya ɗauke fuskar ZAID da wani irin bahagon marin da dole ya sanya shi dafe kuncinsa. Kiiiiiiiiiiiiiii MANDOOD da yafi kowa na wurin zuciya haka yaja hannun Zaid ya kaishi har bakin door yana cilla shi woje. Cikin tafasar zuciya MANDOOD ya dubi Zaid rinannun eye's nashi ya furta.
"Wannan wani shuɗaɗɗan al'amari ne, wata kirkirarriyar tatsuniya ce, sunan ABDOUL-MALEEK shafaffene a cikin tarihin wannan masarauta ka kula"
Fuuuuuuuu ya kaɗa da niyar juyawa chark ya dakata jin wata mahaukaciyar dariyar da Zaid ya sheƙe da ita. Hakan ya sanya A tsananin fusace mandood ya ɗaga hannu zai wanke fuskar Zaid ɗin da wani wawan mari. Cak Zaid ɗin ya rike hannun nasa tare da cewa "Kada kayi wannan ganganci"
Zaid ya faɗa tare da wurgar da hannun mandood ɗin gefe tare da sakin wani ɗan iskan kill smile Yana furta.
"Waya faɗa ma cewar haihuwar Sarki a Dawa kamar ABDOUL-MALEEK yana zama shuɗaɗɗen al'amari, An haifesa ne a Dawa tsaƙiyar karnuka domin farauta. Ubangiji ya bashi ƙarfin zuciyar da zai iya fuskantar ko wanne irin ƙalubale, Iyaka ambatar sunan sa yakan sanya wasu girgizar ƙasa......

"ZAID!!!!.....
MANDOOD ya katse shi a matuƙar tsawace.

Ko inda yake bai kalla ba saima cikin elevator ɗin daya wuce Direct bedroom nashi ya wuce Cikin kwanciyar hankali.
Zaune yakai kan caution tare da jan table ɗin system nashi, cikin kwanciyar hankali yake danna laptop nasa ga sanyin Ac na ratsa shi sai faman cizan lallausan laɓɓan sa yake, ga lips ɗin nasa ya kara yin jawur kamar yasa lipstick saboda ciza su da yake duk wannan latsa laplop da yake hankalin sa na can duniyar wani tunani na daban.
Shiru yayi yana tunani abubuwan sun haɗu sun cakushe masa ya jima sosai akan system nashi kafin ya kashe yana fadawa bathroom.
_1:15am_
Ya fito sanye cikin haɗaɗɗun riga da wanda palazzo ride vizzon Loƙacin da ya fara sako ƙafarsa sa a benen sauƙowa palon ƙasa, ji kake tsit duk wani halitta mai rai dake cikin palon ya nitsu tsit sun sha jinin jikin su, wasu daga cikin bodyguards kam jikin su har kerma yake saboda tsoron mugun haɗe fuskar da yayi. Domin ZAID tamkar ICE and FIRE🔥 haka yake yakan rikiɗe a duk sanda yaso. wucewa yayi ko kallon in da kuyangain suke bai yi ba ya faɗa cikin wata Black jeep Wrangler. Duk kuwa da har haɗa baki suke wajen rige rigen ɗaga masa gaisuwa, bai amsa gaisuwar ko ɗaya daga cikin suba dan dama ba amsawa yake ba sai dai ya ɗaga musu hannu dan magana na masa a duk lokacin da yake cikin irin wannan yanayin.
Yana shiga kai tsaye ya basu umarnin *Flash dancing club* (gidan rawa) Amma baki ɗaya ya rufe ko ina na jikinsa.

Motocin su Zaid na fakawa a *TOWER'S IN KUWAIT. tawagar *GANG BANG* ɗin su na kewaye motar tamkar irin wanda suke Bechelor's Night ɗin nan. Wani irin ɗan iskan aski ne akawunansu. Wasu kuma sun fake Tulan sumar sune da band.
Sune suka buɗe masa car In da kansu tare da fito dashi woje baki ɗayansu, shigarsane kawai ya fita daban da sauran domin wasun su suna sanya ne da gajerun wanduna, wasun su kuma suna sanya ne da trouser sweetheart riga...... Wani babban ɗakin dake zagaye da Gellary DPY WELPAPER suka suna wurin sai walƙiya yake.
Lallai Abin mamaki baya ƙarewa suna shiga duk waɗan da hannuwansu ke riƙe wine 🍷 suka farfasheta, sai kuma suka shiga jona manyan na'urori tako ta ina.
Tawagar Manyan DDS kenan ta ƙasar Kuwait masu ɓadda kama domin duk wata ƙungiyar dake ji ta tantiranchi a garin Kuwait zaka taras su ZAID sune na gaba gaba. Mugwayen ƴan ɓadda kama ne tsabar Tantiranchinsu basa ayyukan su a ko ina sai manyan wuraren da suka fi ko ina tacewa.
A take ɗakin ya ɗauki sautin joing na'urorin cikin kwarewa da sanin makamar aiki suka shiga aiwukansu, Rankwafo da kansa yayi zuwa ga study table ɗin dake gaban Afif tajuddeen.
Baki suka juye cikin harshen larabci suka shiga wasu maganganun dana kasa gane musu. Saidai cikin labarcin suke yawan ambatar sunan *LION🦁*.

★★★★
_LAGOS-NIGERIA_
*Ak*
Sanye ya fito cikin wasu American suit blue black Winter Sports Hat ya sanya a kan sa, bayan ya ɗaure dark black curly hair sa da ɗan ƙaramin ribom's inda tulun sumar ya fito ta ƙasan ƙeyarsa, yayi kyau over ita ma hulan ta masa kyau sosai sai dai ya bar wannan ɗan guntun gashin gaban goshin nasa a waje bai shigar da ita cikin hulan ba, fuskar nan nasa a ɗaure take tamau kamar kullun sai dai na yau ma tafi na kullun, dan ina ga yau idan sukayi ido huɗu da mai karamain zuciya nan take zuciyar zata buga ya mutu awajen saboda tsoron yadda fuskar AK tayi yau abun ba'a magana ya wuce tunanin duk wani mai tunani. sai tashin fitinannen kamshi yake hannun sa na ɗaure da diamond watch kyawawan kafafun sa na sanye cikin Hermes Birkenstock sandal wadda a kalla kuɗin sa ya kai $96000, kasan cewar takalmin launin baki ne sai yayiwa farar kafar sa bala'in kyau na ban mamaki wayar sa da kuma laptop na sa ya ɗauka ya nufo waje, yana taku irin na manyan jarumai ko baka gan shi ba kaji sahun takun sa kasan cikkaken namiji ne mai jini a jika kuma lafiyayye kakkafa ne ke tinkaro ka.
Kai tsaye Restroom nashi ya shige domin wani muhimmin aikin dake gabansa. Akan stool ɗin dake gaban coffee table ɗin yakai zaune cike tsantsar izzar sarautar dake gudana a cikin kowacce magudanar jini ta jikinsa. Shade ɗin dake saman kyakkyawar Innocent face nashi ya zare tare da jona manyan na'urori room ɗin. Sosae ya ɗauki lokaci me tsawo a cikin Restroom ɗin don wajajen 2:30am na dare ya fito.

Bathroom ya faɗa wanka yayo me rai da lafiya ya fito sanye da blue bathrobe a jikinsa, farar fatar nan sai walƙiyar kyau da tsantsar jin daɗi take. Tsaye yakai gaban ƙaton mirror'n hannun sa ɗaya riƙe da ƙugunsa, ɗayan kuma yana sharce ruwan dake yarara saman jikinsa.

*🦅 MIKIYA 🦅*

*~We want an end to oppression💪~*

https://chat.whatsapp.com/GiLzmY90dz17bRbw5yMYBg
____________________

*NA MARYAM NASEER*
~AMMEY LAYLERH ✍️~

✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~*

Page 21&22

# ROMANCE
# BLACK MONEY
# Treason
# Strong love
# Right
# Women's travel
# The Secret Society
# Oppression

# KIDNAPPER'S
# Informants
# DEEP
# BEST LOVE

🤍🔥✅

★★★★
_5:6Am_
Chapter 16 · 0% Book details