← Book details Mikiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 45

Sashe 23

Mikiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

kenan da ga audu bashasha shi kadai ya haifa a duniya.Shi yasa yaron ya taso cikin wani irin sangarta da tabara, Duk inda ake neman wani teteros to in akace maka Farouq fakat kenan. A yanxu haka Audu bashasha yana kasar India wurin kwararrun likitoci don kula dashi.
Ashe be mutu ba da sauran ranshi lokacin da ak ya fasha kansa, Sun boye hakan ne domain gudun bacin sunan Sa, shi da kansa shine ya dauke RIYYA, ya mata wani irin mugun boye mahaifiyarsa kuma irin muta nan ne da sammmm babu ruwansu da duniya. Itace ma dalilin daya sanya ta hana.
Cikin muryar da yake cike da tsantsan sarauta Hajiya Khadija suraj sunusu shureim ta dubi Dan nata Tare da furta.
„Idan har Jinin dake gudana a cikin naka Jinin nawa to ban amince maka ba”
Ta furta hakan tare da bar masa palon, shi kuma ya bi bayanta da kallo domin duk wani Iya shegensa da ji da samartaka da zafin kansa jinsa yake shiba komai bane a gaban hajiya Khadija.
Ya ta biyu kenan ga me martaba sarki suraj sunusu shureim.

*BY AMMEY LAYLERH*

*🦅 MIKIYA 🦅*

*~We want an end to oppression💪~*

https://chat.whatsapp.com/GiLzmY90dz17bRbw5yMYBg
____________________

*MARYAM NASEER*
~AMMEY LAYLERH ✍️~

✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~*

Page 27&28

# ROMANCE
# BLACK MONEY
# DEEP
# BEST LOVE

🤍🔥✅

★★★★

2 months ago

Haka dai al'amurra suka ci gaba da wakana. Tuni baffa ya kashe waccen maganar haka kwanaki suka ci gaba da juyewa zuwa satikai satikai sukaci gaba da juyewa zuwa watanni.
Cikin iko na Ubangiji meerah ta koma bakin aikin da ko a mafarki ba tayi tunanin komawa ba, Bisa matsawar MD da kuma wasu manyan anguwanni ta koma bakin aikin ta.
Haka kuma maganar aurensu da Salman yake neman kan kama, Wannan abu shi yafi komai ɗaya hankalin meerah matuƙa saidai tana danne hakan a ranta.
Kusan kullum yanzu shike zuwa har ƙofar gida ya ɗauke ta zuwa wurin aikinta saidai ta dakatar dashi first.

A tacen ɓangaren su Salman kuwa wasu irin abubuwa suke ma shirye shirye shida mahaifinsa Isa Manu.

*******

Yamma ci ne mai daɗi haka kuma yau din rana ne da ya kasance na musamman wato Jumma'a, ranan da yake ɗauke da albarka da kuma rahamar Ubangiji kala kala.
Wannan dalilin yasa sassanyar iska mai cike da tsananin daɗi da kuma sanya shauƙi ke busawa, a gaba daya ko wani lungu da saƙo dake cikin gidan jaridar zamani TV
Kowa ka kalla harkar gabansa yake cikin tarin nutsuwa, amma banda meerah da tayi zurfi a cikin duniyar tunanin data jima ta faɗawa.

*"MEERAH!"*
*"MEERAH!!"*

Disha dake tsaye kanta ta shiga ambata tana me ƙoƙarin rataya handbag ɗin dake hannunta, Wanda kuma ahankali ta ɗan ranƙwafowa da kanta, tana me kallon Meerah.

"MEERAH wake up kodai bacci kikeyi ne?."

Disha ta faɗi tana me gyara tsayuwanta, tare kuma dasa hannu ta zunguri meerah ɗin.

Ahankali ta ɗago kanta wanda ta kifashi akan desk almost 15mn ago.
Sam ba bacci takeyi ba hasalima duk abunda ƙawar nata ke faɗa tana jinta.

Numfashi ta ɗan sauke Ahankali tare da ɗago manya manyan eyes nata me kama dana mashaya masu matukar kyau, Wanda hakan ya sake bayyana tsananin kyawun dake kwance akan fuskarta, Idanunta da suka ɗanyi blue ta lumshe tare kuma da buɗe su aloƙaci guda.

Cikin unique voice ɗin ta mai daɗin amo da sanyin sauti, tamkar ana busa sarewa tace.

"What happen DISHA? ba bacci fa na keyi ba, just I'm tired."
Ta ƙare maganan tana ɗan kwantar da wuyanta gefe.

"What happening kike tambaya? time ɗin tashi a aiki yayi, kalla ki gani babu kowa ya watse sai nidake kawai, oya tashi mu tafi kodai zaman wurin ne bai isheki ba?."
Disha ta faɗi tana ɗan hararanta tare da yin gaba.

Fuska meerah ta ɗan kwaɓe kana cikin yanayin gajiya da kuma tsananin damuwar dake cinkushe a cikin ranta ta miƙe itama. cikin sauri ta rufa mata baya tana me ƙoƙarin rataya jakanta bisa shoulder nata.

Atare suka fito compound ɗin, tafe suke suna fira sama sama abinsu.
"Disha a raina inajin ina gab da ajje wannan aikin nake ga"
Meerah ta furta cikin cushewar yanayi.
Dafa kafaɗarta disha tayi cikin sanyin jiki ta furta.
”Haba meerah komai yayi zafi maganinsa Allah, ki barwa Allah komai Insha Allah shine maganin komai”
"Hmmmmmm!"
Ta sauƙe ijiyar zuciya me ɗan ƙarfi haka suka ci gaba da tafiya har suka fito gefen titin. Napep suka tara suka hau suna mai kwatancen anguwar da zai kai su.
Ko a cikin napep ɗin ma wata sabuwar duniyar tunanin ta ƙara faɗawa. Na irin daskararriyar K'addarar dake kwance acikin jininta wacce ta fara motsawa kanta.
Haƙiƙa akoda yaushe rayuwa tana tafiya ne tare da tarin ƙalubale.Haka kuma kowa da salon nashi Kalon ƙaddarar amma nata ƙaddarar gani take yafi na kowa, domin daga ta fita daga wannan sai kuma wannan ya kutso kai.

Kamar kuma yanda yake a bayan kowani baƙin ciki akwai farin ciki, haka kuma a bayan kowani kunci akwai sassauci. rayuwa mai juyawa ce farinciki ko akasin haka mummunan ƙaddara ko akasin haka, wayewar garin yau sun waye shine da maganar kawo kuɗin aurenta da iyayen Salman sukai har Naira miliyan ɗaya. Wanda ya tashi hankalin jama'ar gidansu, suka wuni zazzaga ruwan bala'i da masifu kala daban daban.
Ita kuwa wacce ake yi ɗin dan ita sammm ba abinda ke gabanta kenan ba. Wani abu ne daban ke damun rayuwarta wanda da tayi ƙoƙarin zurfafa kanta yake neman juyewa zuwa wani ɓigiren na daban......
Cikin nisan da tayi a duniyar tunani har suka isa ƙofar gidansu bata ma san sunzo ba, Saida disha ta mata magana da ɗan ƙarfi kana tayi firgigit ta dawo hayyacinta Cikin duniyar mutane bata tunani.

*AK*

Msalin ƙarfe biyar na yamma manyan motocin Ak dake cikin garin Abuja suka ma airport ɗin tsinke.
Wasu irin zafafan motocin kusan goma sha biyar irin su Range Rover, Bugatti Veyron, Toyota Highlander, Toyota Tacoma, Ferrari California,gefe ga wasu mahaukatan manyan jifa jifai har guda biyar da aka ware su baƙaƙe wulik dasu. motocine a wurin babu colourn da babu shi kansa airport ɗin kewaye yake da tsaro na musamman.
Ahankali cikin takun izza dajin kai ya fara tako matakalar benen.
Su kuma samudawan sa na aikin su na take mai baya, cikin sauri manyan security'n dake zagaye da airport ɗin suka shiga bashi kariya wa kallon da jama'ar airport ɗin ke binsa dashi. Don kuwa kallo ɗaya zaka masa ka kasa ɗauke idonka a kanshi. Sanye yake cikin Wani arnen cashmere valley wanda kallo ɗaya zaka ma yadin ka tabbatar da ba karamin kuɗi aka narka wurin siyen shiba...
Ahankali yake taka Fararen sawayensa da tamkar wanda bai taɓa takasu ba haka suke, don tsananin taushi da kuma yadda suke sumil luwai.
Wata kafurar Black blue ɗin Mota ƙirar Mercedez Benz aka buɗe masa Armstrong kuma ya faɗa cikin wata narkakkiyar bakar jeep Wrangler . Suka ɗauki hanyar wannan haɗaɗɗen Hotel ɗin na da sukayi booking tun a daren jiya.
Dake babu wata tazara tsakanin support ɗin da kuma Hotel ɗin babu nisa cikin 25 minute suka isa ƙaryataccen hotel ɗin.
A room me lamba 105 AK ya ɗauka su kuma duk suka rarrabu daban daban.
Chapter 23 · 0% Book details