← Book details Mikiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 45

Sashe 30

Mikiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

"KAMAAL A MATSAYINA NA MAHAIFINKA NA BAKA UMARNIN AUREN MARIYA!"
wani irin dokawa kirjin kamaal yayi amma saiya danne hakan cikin cikakken bin umarnin nashi kamar yadda ya daukar masa alkawarin ya furta.
"A MATSAYINA NA DANKA NA AMSHI AUREN MARIYA, AMANA SAI DAN AMANA! HALACCI SAI DAN HALAK, zan amshi wannan auren bisa wakilcin waliyina ABDOUL-MALEEK"
Da karfin gaske ya rungume kamaal din yana fadin "nagode na gode nagade kwarai da gaske bana da haufi akan baka auren mariya da nayi kamaludden uban daraja uban kamala"
..........Umayma cikin karfin hali ta gama kammala girkinta bayan fitar mijin nata. har zuwa yanxun da bayan tayi sallar isha'i take zaune gaban dakin malam liman, da abincinsa da take jirayin shigowadsa!
shigowar malam cikin tsantsan fara da kuma murmushin dake kwance saman fuskar sane ya sanya itama nata murmushin fita da sake fadada, "Alhamdullih umayma lallai Allah maji kan bayin sane ne, cikin hikimarsa da buwayarsa ya mana canji da mafificin alkhairinsa"
ya fada yana kaiwa zaune kan tabarmar da umayman ke zaune, sai kuma ga kai dubansa dakin mariya tare da kwalla mata kira. "MARIYA"
"na'am baba!" ta amsa shi cikin faduwaf gaba tana fitowa tare da tsugunnawa a gaban mahaifan nata. sannu da zuwa tama tayi mar kallonta yayi tare da mata nuni data zauna. zaman tayi tana sunkuyar da kansa kasa.
"kaddara wata abace me tsanani haka kuma me sauki! sannan kuma wata abace da ba'a iya ganin launinta da ido, hakanne ma yasa ba'a iya sauyata daga mummuna zuwa kyakkyawa, acikin kowanne rayuwar ɗan Adam akwai salon tarin ƙkaddarori masu tarin yawa, akowacce duniya akuma koda yaushe kaddara tana tafiya ne daidai da rayuwa. Sannan kuma babu wani bawa wanda ka iya gujema tarin ƙkaddarorinsa. haka kuma ana haifar kowanne bawa ne da salon tashi ƙkaddarar, kisa a ranki shima musan baya cikin kyakykyar kaddararki mariya. domin kuwa iyayensa sun janye kamar yan baya, amma da ubangiji ya tashi miki zabinsa saiya sanja miki da mafificin duka sauran samarukan da suke fasa aurenki. data tashi saiya baki kamaludden me kamala, me karamchi, me nagarta ki amshi wannan zafin a matsayin zabin ubangiji domin kuwa shi kadai yasan manufarsa akan hakan"
ita dai tunda baban nata ya fara fadar maganganunsa bakinsa kawai taga yana motsawa kamar sauran lokutan baya. Ita kuwa meta rayuwa da take juyin wainar masa da ita, daga wancen kasko zuwa wannan kasko? kodai ta aikata wani zunubine da yake ta bibiyar rayuwarta?.

*KUWAIT*
***** *****
Cike titin yake da motoci ba komai ya haddas hakan ba sai wani uban shegen go slow da wata ƙshegiyar bakar mota mai kyan gaske ta hada kirar lexus. anyi crossing dinta akan titin yadda ta rufe titin completely duk glasses dinta tinted ne. dan haka ba'a hangar wanda yake cikin motar,mutane sai hayaniya suke.
kallo daya zaka ma motar kasan ba dan karamin kudi aka narka wajen siyar motar ba.
gurin ya cunkushe mutane sai hayaniya suke yi,abu mafi ban mamakin shine normally gurin yake babu traffic, murfin wata farar mota aka bude wata kyakykyawar matashiyar budurwa ta fito sanye cikin shigarsu irin na larabawa. bakar abayane a jikinta tayi rolling da siririn vail abayar, sai bakin shadow data sanya a fuskanta da alamu sabo da kare hasken rana ta sanya shi.
kai tsaye inda akayi bloocking hanyar ta nufa a nutsenta.
cikin harshen larabci wani matashin balarabe ya furta "yan kibi a hankali mutumin is very dangerous, shegun kasar kuwait kenan ake magana anan" ko inda yake bata kalla ba saima ci gaba da tafiyarta da tayi.

wasu shegun manyan motocine guda shida suka ratso ta cikin titin da wannnan motar tayi blocking hanyan, dole sukaci burki suma kafin mamallakin motocin wanda yake sanye cikin wata iriyar shiga ta alfarma ya bama daya daga cikin tight security'n umarni ha duba ya gani mene ya haddasa wannnan go slow din.
"ba bukatar a duba ZAID EMAAR'S ne"
mahboob ya fadi dake zaune a kusa da sit driver.
"innalillahi yanxun dama gantalewar zaid din shima harya kai haka? bayan shigo mana gida a bugu banda yawon club's club's dinsa ashe harda tarema mutane hanya ya iya!"
cewar MOH JIDDO da take zaune a kusa da AL-HUSSEIN EMAAR'S.
a mugun fusace AL_HUSSEIN ya bama wannan tight securityn umarnin
su farfasa motar su fito dashi suyi masa shegen duka su jashi su kaisa gida.
cikin cika umarnin alhussein suka diddira a motocinsu suka nufi inda motarsa yake.

dai dai windown driver wannan mudurwar tayi knocking a hankali zaid dake kwance cikin motarsa ya kure A/CN yana latse latsensa a wayana ya dan dubi inda ake knocking glass na motornshi.
da sauri ya sauke glass din fuskarsa ta bayyana dauke da murmushin mamaki ya furta.

"Hey JESRA me kike yi anan?"

dan bata fuska tayi tare da daura hannayenta akan windown tayi tagumi ta furta
"unguwa zanje kuma yayana ya tare min hanya yaya kenan?"

ta fadi cikin dan bata fuska kansa ya ciro ya kalli dandazon motocin. da suka taru a tsakiyar titin tare da sakin wani dan murmushi kadan ya furta
"lallai kice yau dara taci gida kenan?"
ta fadi daidai lokacin da security'n suka karaso wurin. Tafiya suka yi har zuwa bakin motar saidai ganin jesra tsaye a bakin motar ya sanya suka ja burki. domin su basusan waye a ciki ba sudai umarnin su may duma kawai aka basu.

Bai san da zuwansu ba sai ganinsu yayi a gabansu.
wani shegen kallo zaid ya jefa ma securityn tare da furta
"Duk wanda yasa darty hands ɗinsa ya taba ni kuwa sai na kwantar dashi a gadon asibiti kuma ya bar aikin sa kenan har gaban abada, bama a cikin gidanmu ba harma kasar baki daya saina lalata duk wani offer nashi na samun aiki"
ja da baya security'n suka shigayi suna barin wurin baki daya.
jesra ce ta furfa
"me yasa har abada a jawa oummey magana kake? bawa kai ba bawa shi wancen din ba! zuwa yanxun ya kamata ace kun fuskanci rayuwa daidai akie"
ta fadi tana shiga cikin motar woyarta dake cikin hand bag dinta ta ciro ta kira driver'nta tace ya koma gida. Mazaunin driver ta zauna tana zare glass din idon ta ko kallon inda yake batai ba ta furta.
"Ina muka nufa?"
..shima bai tashi daga kwancen da yake ba ya furta.
"BELOW SNOW muka nufa"
"gun wasa kuma me zakayi a wurin wasa?"
"AIKI"
Ya bata amsa a takaice tare da furta "ke ina kika nufa"
"four seasons hotel alshaya na nufa tare da willtopin fun tiki back future"
wani irin dan yatsine fuska yayi tare da furta.
"nafa kusa janye wannan shegen aikin naki JESRA na sanya kai a hadari kina matsayin mace"
saurin kallonshi tayi tare da banka masa harara ta sanya hannunta ta dunguri keyarsa tare da fadin.
"to bismillah sa idanawan duniya kai duk abinda kake oummey ko paah basuce sun gaji da kai ba saini?"
ta fadi daidai tana shan kwanar below snow din da suka kawo. a bakin wurin ta ajje shi tana fadin
"bari na wuce domin nine nake son fara haska latest amazing story innan akaf kuwait"
"take care ki kula sosai fatan nasara uktie"
zaid ya fadi yana shigewa cikin gun wasa.....

**POLAND**
*Salman pov*

A lullume garin yake sakamakon yanayin sanyin da garin yake da, Hazo ne ya yi wa samaniya ado ga iska mai ƙkarfi dake ta shi tana ƙkara haddasa sanyi irin mai shiga jika nan, yayyafin dusar kankara aka fara wanda hakan a wurin mazauna garin ba komai bane.
A wurin bako kuwa wannan sanyin ka iya haifar masa da wata illar.
Chapter 30 · 0% Book details