← Book details Mikiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 45

Sashe 2

Mikiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

” I got out of the case, will my strength come back to me, or I will die! AK what happens What is wrong with me in life that you want to see my back, Woooooo wiiiiiiiii huhhhhhhh ahhhhhh Pain, pain, pain”
Haka ya shiga hargitsa kalamansa wanda Ni ban fashimci ko manganun waye ba. Wanda naji an ƙira da AK kuwa ba tare daya tsaya sauraran kururuwan wannan dattijon fa ya juya yana barin ɗakin rai bace. ɗaki mai 117 ya kuma nufa. Shiru alamun babu wata rai mai Numfashi a wurin duk inda ya gitta sai kaga manyan security na sara masa, haka ya ratsa har petal na dakin. Wani irin gurnani na ringa jiyowa irin na ceton ran, kafin naji an sheƙe da wata uwar mahaukaciyar dariya, cikin sautu me amo kunnuwana suka fara jiwo min wasu kalamai
"Ke a tunaninki har kin wani alhakin da kika isa tona min asiri Kina ƙarƙashin ikona REEYAH, akwai dubin ki kafin ke amma sun buga dani sun barni, domin ni AUDU BASHASHA ban fito ba Saida na shirya, ayau zaki sheƙe reeyah bayan na wulaƙanta rayuwarki na yagalgala ta” da ƙarfin masifa ya shiga fincikar kayan dake jikinta, da iyaka ƙarfin da ya saura a jikin ta, tayo kaki ta tofa samar baƙar fuskarsa, cikin muryarn da taci kuka harta gode Allah ta ce.
”Wawa! Jaki, dabba, daƙiƙi, wai kai a tunaninka kama ni! Kayi? to ka sani wannan karon ma shine ya kama ka, shine ya ɗana maka tarko kuma dole yayi wining wasan”
A ɗan razane ya dube ta kafin fusata ya ce, ”reeyah sau nawa wai ake haifo shi?! shi wanene menene abinda yake taƙama dashi. Dariya mai tafe da hawaye ta saki loƙaci guda, sai kuma ta shiga nuna shi da yatsarta manuniya tana faɗin.
"Wai ka tsorata ne, ka sani sau dubu billions dollers ake haifo irin sa, kuma shi ne wanda baya mutuwa, EAGLE"

Ratsatsa haka sautin kararn fashewar glasses in daya ma dakin ƙawanya ya bada loƙacin da wannan mutumin me ɓoye fuskarsa ya faso ɗakin, a razane a kuma kiɗeme mutumin daya ƙira kansa da AUDU BASHASHA yaja baya yana zare jajayen idonsa irin na mugyaye. P-carp ɗin dake samarn kansa ya zare a take wata kyakkyawanr fuska ta bayyana wacce kallo ɗaya zaka masa ka san wannan ba daga ƙasarmu ya fito ba, kunnen ɗaya na gefen hagu na manne da wani gold ring bari ma daya huja. gun ɗin dake maƙyale a bayan wandon jikinsa ya ciro yana fasa kan wannan mutumin a take ko shurawa bai yiba, ko inda budurwarn nan take bai kalla ba ya sanya kansa yana ficewa a ɗakin, bayan ya ɗebe duka wayoyin mutumin duka biyun, yana bi ta wani door na daban ba wanda ya shigo ba.

A hankali yake saƙƙowa daga saman benen hannuwansa zube cikin aljihun wandon sa, yana tafiyar nan nasahi tamkar wani King
Yana sanye da wasu haɗaɗɗun riga da wando na trouser, yayinda fuskar nan ke sakaye cikin sun glasses ya sanya hular jacket ɗin dake saman kayan jikinsa, sannan ya sanya face mask. gentle yaci gaba da saƙƙowa zuwa downstairs, jikin sa na fidda wani irin fitinannen ƙamshin perfumes nasa mai kwantar da hankalin mai shaƙa

A ƙasaitance ya kai zaune zama irin na sarauta saman Royal caution ɗin dake jere a parlourn, binsa da ido wannan samudawan suka ci gaba dayi har sanda ya fara sarrafa system nashi.
Cikin kwanciyar hankali yake danna laptop nasa ga sanyin A/cn na ratsa ko ina na parlourn, duk yadda suke faɗin "Boss good morning, Boss good morning!" Amma ko saurararsu bai yi ba.
Ba tun yau suke anya kuwa AK cikakken mutum ne kamar kowa, daba da murɗaɗɗen mutun ne shi wanda baka taɓa gane gaban sa bare bayan sa, kullun cikin gindayar da mutane yake, sai ka rasa ina ya dosa kwata kwata, shin wacce iriyar zuciyace gare shi Sammm baya tsoron mutuwa, A yayin da sojoji suke tsaka da musayar wuta zaka yadda kowanne soja ne sanye da bulletproof, domin kare harsashi daga shiga jikin su. Amma banda AK, yayin da kowa ke gudun mutuwa to shi tunkararta yake shi yasa ake masa laƙabi da mutumin da baya mutuwa.

__________★★★
*Nigerian army headquarters Lagos*

Tun daga farkon shiga headquarters ɗin zaka fashimci ba lafiya, domin ta ko ina ta ko wanne saƙo da longo kewaye suke da manyan sojoji masu jini a jiki.

A babban ɗakin taron dake cikin headquarters ɗin, duk wani army dake da babban matsayi ne kewaye a cikin ƙaton ɗakin, suna Zazzaune saman kujerun da kowanne ke pacing dan uwansa, a matuƙar fusace mr. President ya doka saman table ɗin dake gabansa, cike da ƙonar da zuciyarsa ke masa da kuma takaicin wannan abu ya dago jajayen rinannun idanunsa yana zuba su saman duka soldier's ɗin dake zaune cikin Office ɗin.
"What are you doing and you are giving your feet to this militant boy, he is taking use dahar ya samu zarrar da zai riƙa mana dauki ɗai ɗai, ya zama dole a wannan karon mu kawo ƙarshensa"
Yayi maganar ne tare da duban duka soldier's ɗin dake fuskantar sa, cikin dakakkiyar sautin sa ya kalli ɗaya daga cikin soldier's ɗin yana furta.
”Ajmaal har yanzu kana kan bakar ka na kama EAGLE?”
"Yes sir."
Wanda aka ƙira da Ajmaal ɗin ya faɗa tare da sara ma mr. President ɗin.
Ɗaya daga cikin soldier's ɗin ne ya kuma miƙewa Saida yayi solid na mr. President ɗin kana cikin bauɗaɗɗar murya ya shiga magana kamar haka.

”Har yanxu ina mamaki sir.mutumin daya bamu horo sannan kuma ya kashe ƴan ta'addar da babu adadi!, me Ze sa ya zama ɗan ta'addar?”
Wani kafirin murmushi mr president ɗin ya saki tare da tsare wannan soldier's ɗin da firgitattun idanunsa, cikin dakakken sauti ya furta.
”Har yanxu kana son eagle kenàn?"

"Kwarai sir amma ba kamar yadda nake son ƙasata”
Cikin tsare shi da ido mr. President ya furta ”Idan har kai ka samo shi zaka iya harbinsa?”
Saida ya kuma solid na president ɗin kana cikin Amon murya furta
"Kwarai sir zan iya!, amma idan na tabbatar bashi da laifi, nayi ma wannan alƙawarin sir.”
Cike da jin zafin Ajmaal ya mike cikin fusata ya fuskanci wannan soldier's ɗin.

"Jaheed kodai kana tare da AK ne, in banda haka ta ya kake tununin cewa Eagle bashi da laifi?”

Shima wanda aka kira da jaheed ɗin ya juwo yana sake fuskantar Ajmaal ɗin, kafin cikin yaƙi ni yace.

”Idan baka son mutum zai iya siyar da borkono kuce ba zafi, haka zalika zai zai wuce ta cikin ruwa kuce ya tada kura, mutum kan gwada zafin wuta ne sau ɗaya a rayuwa, wannan sojan shi da kansa yake ta famar fafutukar shiga wutar, taya kuke tunanin mutum mai tsananin gaskiya da kuma sadaukar da rayuwarsa domin ƙasar da kuma aiki da zuciya kamar ABDULMALEEK KUWAIT AK zai iya zama ɗan ta'addar? kamar yadda kuke ƙiransa da shi, dole Akwai dalili ko nace dalilan da suka sa ya zare kansa daga cikinmu”
Ba shi Ajmaal ɗin daya qA@@ maganar ba shi kansa mr. President ɗin yasha jinin jikinsa, wani irin shiru ƙatoton office ɗin ya ɗauka, kowa da abinda yake sakawa acikin zuciyarsa, wani irin shiru ƙaton office ɗin ya ɗauka na kusan second 40.kafin Ajmaal ya magantu "ko tantatama bayana yi kana ɗaya daga cikin ƙashin bayansa"
Ya buɗe baki da shirin sake yin magana keñan mr president ya Wani irin doka table a take komai da yake kai ya tarwatse komai yayi nashi wuri fuuuuu ya fice a office ɗin a fusace, ganin haka ya sa duka soldier's ɗin suma suka mimmiƙe suna barin office ɗin, wani irin kill smile Ajmaal ya saki loƙacin da yake dab da fita.

*ISAH MANU EMPIRE🔥*

Wani katafaren ƙerarre haɗaɗɗen luzary ne iyaka ganinka gini ne Irin na manyan ƙusoshin kasar,wanda suka ci suka sha kai harma suka tada kai, baki ɗaya ginin gidan ya kasance na glass da glasses ne. Duk kuwa irin girman da gidan yake da, amma kewaye yake da uban wasu jibga jigban soldier's.
Kai tsaye katafaren parlourn gidan na kutsa kaina,da wani farin dattijo na fara cin karo wanda keta faman safa da marwa. Hannuwansa goye a gadon bayansa wanda a ƙalla zai iya kaiwa shekaru 80 ko irin da biyar ɗin wani irin sintiri yake famar yi, wanda kallo ɗaya zaka mashi ka kai tsaye ka gane cewar tabbas baya a cikin hayyacin sane, da ƙarfin masifa ya dunkule hannunsa tare da kaima iska naushi.

"Why is everyone afraid of him? Wanene shi yaushe ma aka haife shi dahar zai sanya ni gudun tseran tsira"

Yayi maganar Cikin zallar ɓacin rai da kuma jin ƙona daga cikin tsaƙiyar ƙirginsa.

Da sauri ɗaya daga cikin samudawan mutanen dake zagaye a ɗakin suka haɗa baki wajen furta.
"Ko wa ye izini kawai zaka bamu!, mu kawo maka kansa BOSS"
Idanuwansa da suke rine sosea ya ɗago tare da zuba musu jajayen idanunsa da suka ƙanƙance. Numfashi ya fesar me zafi kamar bazai magana ba, sai kuma ya magantu, Cikin wani irin dakakken sauti ya furta.
"EAGLE, MIKIYA Shi nake da buƙata!"

A razane A ƙiɗime hankali tashe suka ja baya namomin jikinsa na rawa, suka shiga bin boss in nasu da kallon You are smart 😳😱👀

Hhhhhhhhhh to ai shikenan 😅🥰 A gimtse 🫰 🙃♥️✅

*BY AMMEY LAYLERH ✍️ ✅*

*🦅 MIKIYA 🦅*

{Mai hangen nesa 👀}

*~We want an end to oppression💪~*

https://chat.whatsapp.com/GiLzmY90dz17bRbw5yMYBg
____________________

*NA MARYAM NASEER*
~AMMEY LAYLERH ✍️~

✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~*
Page 3&4

🤍🔥✅
Chapter 2 · 0% Book details