← Book details Mikiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 45

Sashe 12

Mikiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ba ƙaramin tashin hankali su anne suka shiga ba ganin har bayan sallar isha'i babu baffa babu dalilin sa Raiha sai kuka take, baffa kuwa da kansa ya gama kullewa ne yasa jininsa naiman hawa nan take, bai sake tsorata da lamarin ba sai loƙacin ƴan sanda suka zo da batun mutumin da ya yi belin meerah ƴan fashi sun sun tare sa a hanyar sa ta mika Meerah ga iyayen ta a round about ɗin sa na shan kwanar anguwar su malam Abdullahi gwani.
Cikin abinda bai wuce kiftar ido ba labaran suke zake hargitsa media, ƙura takai ƙura kam a wannan loƙacin, a kuma daidai loƙacin ne aka shiga musu da malam Abdullahi gida a yanayi mafi munin gani. Nan da nan matan baffa biyu suka shiga yaɓama Anne maganganu baƙaƙe. Wai akan yarinyar data gama gantalewarta a titi suke neman rasa malam, wllh baza su yarda ba. Anne kammm zuwa lokacin ma ita kam babu abinda take iya fuskanta daga cikin maganganun nasu, a fisge taji kalmar ƙarshe daga cikin ɗaya daga cikin matan.
"Dama ai barewa ba zata yi gudu kuma ɗan ta ya rarrafa ba, wllh malam ka auro mana masifa da bala'i, gashi kuma masifar daka ɗaya ƴanta sune suke ƙoƙarin ajalinka, kaje garin kwashe kwashenka ka auro mace mara asali wanda ba'a san inda asalin ta take ba, wanda ya wuce ƴar gaba da fatiha me bakin duniya"
Dipppp ji da ganinta suka ɗauke daga nan bata sake sanin ainihin abinda ke faruwa ba.
★★★
Sannu a hankali na shiga motsa idanuna da suka min matuƙar nauyi da ɗaurewa. Sai kuma na shiga buɗesu sannu-sannu harna gama buɗesu. hasken daya cika idanunane ya sanya na ɗan tashi a zabure da sauri. komi daya faru ya ringa dawo min daki daki har zuwa sleeping pawdern da suka shaƙa min. Ƙirjina ne yay wata irin masifar bugawa da sauri na ambaci sunan Allah.
Cikin sauri na mike na nufi ƙofar bathroom ɗin da nayi amfani dashi wajen uzurina. Alwala na ɗauro sauri² gudu² na fito praymad ɗin da nayi sallah akai jiya yauma na nufa, a nutse na fara sallar cike da nutsuwa.bayan na idar na sulale a wajen ina saki wani irin kuka mai tsuma rai da da zuciya. Na jima kwance a wajen ina kuka kamar numfashina zai rabu da gangar jikina. Nama rasa ina zan kai tunanin na. Handle ɗin dakin naji an taɓa tare da shigowa mutumin jiya da dare ne duk da cewar fuskarsa a rufe take amma tsab na gama gane shi, kasancewata mutum bai kaifin basira, plate ɗin dake ɗauke da soyayyar wainar kwai ya ajje min tare da ledar bread recipe ya juya abinsa da niyar tafiya.
"Lallai hakan da kuka yi shi ne ya sake tabbatar min da cewar ku dukkanin ku lusaraine, kolaye ne tunda har kuka rasa abinda za kuyi sai kidnapping mace" nayi maganar tare da jan wani mugun tsaki.
Duk da ya tsaya cak tun fara maganata bai juyo ba. Harna kammala maganar kuma bai tanka min ba ya buɗe ƙofar ya fice tare da sauri tare da kulleni ta baya. Ido kawai na zubama ƙofar wasu kalar hawayen bakin ciki na sake gangaro min da gudun tsiya.
A yanzu ba wai kaina kawai nake tausayi ba su  Annena baffana Raiha ɗina nake tausayi da halin da zasu shiga sune suke matuƙar tada min da hankali fiye da komai.
Bai cika 20 minute da fita ba sai gashi ya sake dawowa farin handkerchief ɗin dake hannun sa ya jefa saman fuskana hakan yasa na fara ganin bibbiyu kafin kuma na tafi luuuuuu.
Ban ƙara sanin inda kaina yake ba sai bayan sallar zuhr, a wani bedroom ɗin na daban na sake tsintar kaina ba wanda aka fara kaini ba. Da kyar cikin mutuwar jiki na miƙa na nufi hanyar da tsammanina ya gama bani bathroom ne, ilai kuwa bathroom ɗin ne toothpaste da brush na farke su a ledartarsu, saida na fara wanke bakina kafin alwala sallar zuhr tayi tare da fara duk wasu addaoin da suka zo bakina. Ledar takawey ɗin dake gaban gadon naja bisa dole zuwa gabana. Domin kuwa in banda kukan yunwa babu abinda cikina yake. Kaɗan na ɗan chakala na ture gefe domin ma samm sai naji bana jin cin abincin ma.
Mahaukacin ƙamshim da hancina ya shaƙar min ne ya sanya ni saurin ɗago kaina zuwa Said ɗin da naji ƙamshim na fitowa. Da wannan idanuwan dana zana na fara cin karo, wanda har ƙarshen numfashina baran taɓa mancewa dasu ba.
Sanye yake cikin wasu tsadaddun luzary Ride vizzon sky blue colour daga ƙasar rigar kuma fari kaɗan irin hadarin Dubai ɗin nan ce dai.sai lallausan farin wando trouser kansa sanye cikin hular luxary supereme irin ta sanyin nan sai facemask irin Turkish ɗin nan shima, yau kam babu glasess ɗin da yake toshe idonsa dashi. Fuskarnan a matukar haɗe. Chair lind ɗin dake gefe da gadon ya janyo zuwa gabansa, zaune yakai zama irin na wanda suka isa zama ne irin na zaratan sarakunan da suka kai sarakai ba muna sarki ba. Wanda hakan da yayi ne ya shagaltar da Meerah a kallonsa.
"What wrong with you flower pie?" Ya faɗa cikin daƙilallalliyar muryansa, a rikice ta dawo nutsuwarta tana dedeta kanta, tare da hararar inda yake zaune. A fusace ta furta
"miye Amfanin kidnapping na da kuka yi?"
Wani malalacin kill smile ne ya subce mishi a bazata. Domin samm baiyi zaton bakinta zai iya murta wata magana ba, amma kuma idan yayi duba da tsaurin idonta da tsaya samm hakan ba abin mamaki bane.
"Wannan bakin naki zai kaiki ya baro ki silly girl! Idan kika ce zaki buga game da Ak to kuwa tabbas zubar hawaye bata shirya barin idaniyarki ba ke nan"
Cike da tsiwa da son hana ganin lagona na sake maida fuskana gare shi tare da furta "Never for ever ka rubuta ka ajje Ni Meerah Abdullahi gwani saina sanya ka gudun ceton rai a tsakiyar karnuka"
A bazata yaji sauƙar kalaman nata don haka ya zuba mata cat eye's nashi tare da folding hannun wansa saman ƙirjinsa. Don shi maganar nata dariya ne yaso bashi amma dake tantirin kansa ne hakan ko ajikin shi. Saima gira ɗaya daya ɗage mata tare da furta "weldone pie" tare da juyowa da kallonsa a kanta ya sakar mata wani lalataccen murmushi.
"Tabbas kuwa karen zai mutu da haushin kurar"
ya faɗa idonsa cikin tsakiyar nata idanun still murmushin gefen bakin nan bai bar fuskarsa ba.
"Bad boy da dukkan alamu kana wasa da wannan Meerah ɗin amma dai muje zuwa musu iya magana sukance ba'a san maci tuwo ba sai miya ta kare"
Cikin majestical takunsa ya nufo inda nake tare da matsowa daf dani. "Did I look like a comedian to you?"
Yana faɗar maganar ya nufi hanyar barin bedroom ɗin baki ɗaya cikin nutsatstsen takunsa mai cike da ƙasaita. Bayan ya mata wata halamar data gaza fashimtar kota miye.
______
       Shigar Isa Manu a zancen ya saka ƴan sanda sake ɗaukar zafi, Dan a yanzu D.c.o ɗin ne ma da kansa yake gudanar da binciken kidnapping ɗin Meerah ɗin tare da Inspector atya murail.
Al'amari kamar wasa akan ɓatan Meerah ƙaramar magana na neman zama babba. Dan ƴan sanda sun matuƙar zafafan bincike akan maganar duk inda ka wulla magana ɗaya ce, duk da kuwa shi kansa Isa Manun kidnapping yarinyar yaso yi.

*🦅 MIKIYA 🦅*
{Mai hangen nesa 👀}

*~We want an end to oppression💪~*

https://chat.whatsapp.com/DGIo9iiSjlgJPPqFHNtddH
*NA MARYAM NASEER*
~AMMEY LAYLERH ✍️~

✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~*
Page 13&14
#ROMANCE##
#BLACKMONEY
#KIDNAPPING
*DRUG TRAFFICKING
#AGGRAVATED ROBBERY##
#AMAZING W*w(☞ ಠ_ಠ)☞

https://www.aihausanovels.com.ng********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.
******* FOLLOW US ******
WhatsApp Number: 08104493215
Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.
Chapter 12 · 0% Book details