← Book details Mikiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 45

Sashe 11

Mikiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Baifi 10 minute da fitar motar ba baffan meerah ya shigo station ɗin, sosae hankalin sa yayi wani kalan masifar tashi, jin wai mahaifin meerah ɗin yazo yayi belin meerah ɗin. To waye mahaifin meerah kuma wanda ya wuce shi?, Kodai hankali ne kawai suke neman rena masa. Amma saiya danni zuciyarsa cikin tsanako da dattako irin nasa yabar station ɗin ya barma zuwa an jima kaɗan, wai a ganin sa kawai yau ɗin ma basa da ra'ayin barin sa ya ganta ne kawai shi yasa suka ɓullo masa da wannan zancen.
★★★
Wani kalar furzar da iska yayi yana maida kansa jikin saman sopa ya kwanta tare da lumshe idanunsa a hankali. Shi kaɗai yasan abinda yake ji game da taurin kan yarinyar data zaba buga game dashi. Ya fahimci lallai bata fahimci a ramin da take neman jefa ƙafarta bane. Amma zai bata loƙaci ta gama nata kalar ɗan ƙaramin wasan kafin ya fara buga babban game da sai tayi dana sanin sanin AK a rayuwarta da tayi. Idan ita ƙaramar ƴar iskar layi ce, zai tabbatar mata shi na duniya ne baki ɗaya, dan ba zubar da jini kawai ya iya ba harda cin uban duk wanda ya shiga sabgarsa. Lallai ta ɗaukarma kanta Dala ba gammo tunda tayi kuskuren zana fuskar sa, ya fahimci ita ɗin ƴar zafin kaice tun daga yanayin yadda ta mu'amulance shi a gidan jaridar su, amma ba komi tayi nata zafin kan ta gama duk zai sauƙe mata su kuwa nan bada jimawa ba.
      Ya jima a wajen zaune har su Axton suka dawo ɗauke da abincin da Vincent ya sasu suka yo order. Amma shi boss ɗin sai yace bazai ci ba. Ya haɗa coffee kawai da biscuits mai daɗi. yana shan coffee ɗinsa da biscuit tare da nazartar yarinyar. Koda ya kammala shan coffee ɗin bedroom ya wuce kai tsaye Maimakon kwanciya bathroom ya faɗa, ya haɗa ruwa mai ɗumi cikin bathtub tare da haɗa kayan ƙamshi kala-kala a ruwan sannan ya shiga ciki. Sai da ya kashi mituna a cikin ruwan na ratsashi da miƙar masa da kowace gaɓa sannan ya fito ya shiga wajen wanka ya ɗauraye jikinsa. Bayan ya fito salla ya fara gabatarwa tare da shafa'i da wutiri sannan ya shiga shiri. Yayi ƙyau sosai cikin shigar tasa tamkar ka sacesa ka gudu. Ga wani uban ƙamshi na tashi tamkar duka Company'n haɗa turaren ne a jikin sa. Sumar nan tasha gyara daka gansa kasan ya haɗa jini da masu jajayen kunnuwa. Hakama kwantaccen gashin sajensa sai walƙiya yake gashi kwance luf-luf ya sake fidda taswurar doguwar fuskarsa. Sai da ya tabbatar komai ya masa yanda yake buƙata sannan ya fito cikin nutsuwarsa da takunsa na tsayayyen namiji.

National Hospital atarubus
3:45pm

Accidents and Emergency aka shiga da wannan farin dattijon dake sananne ne shi babu wanda bai san waye Isa Manu ba, A kaff cikin Lagos harma da zagaye ta cikin ƙanƙanin loƙaci aka shiga bashi taimakon gaggawa.
Chapter 11 · 0% Book details