← Book details Mikiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 45

Sashe 32

Mikiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ayau daya kasance ranar lahadi 1 ga watan takwas na OGUSTA dangin salman suka kawo jibgin kayan akwatunansu gidan. Kayane iyaka kaya wanda mutanen gidanmu harma da yan anguwa zancen kayan ake, media kuwa babu inda zancen be zaga ba domin magana ake ta Ajebor irinsu salman.A lakacin dana budi ido naga yadda pisc nawa suke yawo a media Raina ba bakaramin baci yayi ba, domin abu na farko danafi tsana kenan yada photo's nawa ya media.
Martanin kowa wannan lokacin shine ashe dama shine dalilin daya sanya kullum nake makale a cikin nikaf.
Ashe nasan abinda nake ma kaina tanaji tunda gashi ata sanadiyar auren dan shahararre kuma tycoon isa manu empire pisc nawa sun gama karade ko ina.
Masu iya magana sukance ba iyaka yaudinka shike tabbar maka da nasarar goben kaba, haka zalika yau dinmu ba itane madubinmu goben mu itane madubinmu abin alfarinmu...
Nayi kuka, Nayi kuka Nayi kuka wanda ni kaina bansan iyakar shiba a wannan rana.
Karin wani abin mamakin kuma idan nace muku Anne sammm bata farin ciki da wannan auren karkuyi mamaki ko al'ajabin hakan.domin memakon kaga tarin farin cikinta saidai kaga akasin hakan, Ko yanzu ma kwance nake tarin abubuwa sunbi sun cunkushe a tsakiyar kirji. Ganin dumuwa na neman sanya ni a wani halin ne ya sanya ni bude DATA na, WhatsaAp nawa na fara lekawa bayan sakwannin mutane dana dan dudduba saina koma kallar status na mutane. Bear man shine status na karshe dana kalla wanda ya bani mugun haushi sosae, Pisc ne marasa kan gado yayi status dashi nace kunsan waye me wannan sunan Salman!.mutumin dake dab da zama mijina shine me wannan sunan, don ni a zahirin gaskiya idan na kalleshi da dan biri yake min kama karfa kuce wai don bana son shiba.
A ahh bawai don bana son shi bane har zuciyana da gwaggon biri yake min kama.
Fita nayi daga whatsaAp din na koma Facebook nan na dan dubba abubuwan da suke wakana a median kana nayi search na sabon littafin *SPECIAL*
_TA DABAN_
Na AMMEY LAYLERH da zata fara domin kullum saina duba amma haryau bata fara ba, tun akan litattafanta uku dana karanta na mato akanta Wato litafinta na.
*KAREN BANA*
*JALAAL AREEF*
*KAUNA BIYU*
Sai kuma wani dana fara karantashi amma be zama complete ba wato *PRINCE SAPWAN*
{Sanyi ya haifa wuta }.
Saidai kash yau din ma banyi dace ba har yanzun bata fara ba mebi domin tun daga dandanon kadan daga cikin labarin na gane zai bada fire sosae.
Haka na hakura na sauka tare da kashe data na ammafa ban sauka ba saida na ajje mata message a facebook dinta don bana da whatsaAp number nata.

Sallamar da Hajiya umma ta rafkone ya sanya ni tashi zaune ina amsata tare da kashe data na. Karasa shigowa tayi gaidata nay ta amsa ni tare da tambayar inda Anne take, ganin bata parlon kallonta na danyi sai kuma na sunkuyar da kaina da hannu na mata nuni da bedroom dinta.

Meeting room

Wani irin hadadden parlon ne mai mahaukacin girman gaske parlon ne mai kamada wata fadar kana ganinsa kasan wasu ishasshun mutanene ke rayuwa a ciki, akalla mutanen dake zaune a cikin parlon sunkai wajen su ashirin da biyu, ko wannensy zaune yake akan street table din gaban ko wannensu dauke da juice da gorar ruwa sai dangin su snack.
Manyan masu kuɗin mu kenan manyan kuma yan siyasarmu ne ake magana. A tsakiyarsu ga system jone da dukkan alamu video call suke, wani babban mutum ne kwance jikinsa sanye da uniform irin na marasa lafiyar nan. Zaune ya tashi cikin tsananin fushi kafin cikin miryan fusata ya ce.
"Na rasa mema kuka tsaya yi dahar yanzu baku kawar da wannan shegen yaron ba, tsananin fusata kukeson ta bayyanane kawai manu!, in banda haka ace yarona yana wurinsa duk kaninku babu wanda yayi wani yunkurin kwatar shi daga cikinku Right?"
Tambuwal ne ya dube shi shima cikin nashi kalan bacin ran ya furta

"Kafi kowa sanin wanene wannan yaron bashasha kai a tunaninka zuba ido mukay kenan kome, toba shiru mukay ba karka manta cewar governor da minister da kyar suka sha, zafin kan yaron ni kaina na bani tsoro
ɗan zafin kaine dabi'arsa kuma kan firgitar dani sammm baka taba gane alkiblarsa baka taba sanin koshi ainihin wanene shi!?”
" Saime! Nace saime dan dabi'arsa na firkita zafin kansa kuma kan baka tsoro toni sammm kwata² bana tsoron haka, nima dan zafin kanne aiiiii ko ka manta waye Audu bashasha na tuna maka"
Ya fada a fusace cikin fusatar kanta.
"Duk ba wannan bane ya taramu muyi zaman daya taramu kowa ya kama gabansa, yanzu abu tsaye a raina shine bikin yarona idan an gama komai ya biyo baya. Kuma idan baku manta ba ji ina mun kashe wancen maganar tunda ita kanta yarinyar tana dab da zama tamu ne"
Ijiyar zuciya duka suke saukewa kafin ya dago kaida ganinsa kaga wanda baya cikin hayyacinsa, "To wai ma bikin saura kwana nawa ya rage mana ne ma?" Ya tambaya yana komawa kwance domin yar hayaniyar nan harya fara hawar masa kai.
Daga nan suka shiga tattauna manyan maganganunsu na sirri daga haka zaman nasu ya tashi. Domin tanbuwal har Allah Allah yake su tashi domin yana da wajen zuwa karfe taran dare.
A slowly katuwar bakar jeep din ya parker a wurin adana motoci na cikin Park din, Sanye ta fito cikin riga da wando bakake sai wata falmaran Ash color data dora saman riga sa wandon. Idonta toshe cikin bakin glass tayi rolling da siririn vail din riga da wandon wanda suka kasance disigners ne.
A hankali ta shiga karema wurin kallo, Kallon wajen kawai Riyya keyi lik kamar irin bata san wurin nan ba. iyaka haɗuwa wajen ya haɗu park ne mai girman gaske ko wanne passege yana da nashi kalan kyaun, basarwa tayi tana jingina da jikin motornta babu dadewa kuwa wata arniyar Rolls {R} Rayce blue black ta sanyo kanta cikin park din. Har dab da idan take tsaye motorn ya faka kafin matashin alhajin dake zaune cikin motar ya fito.
Jikinsa sanye cikin wasu shegun Cashmere me laushin tsiya da tsadar gaske wanda kai tsaye bazaka taba iya zartarma da kayan kudin da suka lashe ba.
Tun daga kan motarn ta fara kallon shigar shi da irin makudan kudaden da suka lasa.

Bvl $15, 000
Cartier $5, 000
Rolex $35, 000
Rolls {r} Rayce $250, 000

Wani irin numfashi ta sauke tana dauke kanta a kallonsa, yana karasowa dab da ita ya sakar mata wani tsadadden murmushi yana mata nuni data biyo shi.

Bayanshi tabi suka bi wata hanya cikin wani kayataccen special gun shan iska suka tsinci kansu, kan wasu kujeru wanda suke zagaye da wajen suka karasa zama yayi tare da mata nuni data zauna itama.
Kujerar dake facing dashi ta zaune suna zama wata waiter ta iso wuin tana basu jotter na jerin abubuwan da suke dashi. Shine ya zabi tarin abubuwan da yake so tare da bata umarnin taje ta kawo, babh jimawa ta kawo katon nrey tray xuwa kan table din dake gabansu.
kallon ice-cream ɗin merrah ta yi amma bata ɗauka ba saima wayarnta da take famar latsawa, Dan gyaran murya yayi tare da fadin "Baby ya kamata ace kinsha ko wani abune"
Ya fada cikin Kasa da murya sosae ba karya kamm jijinsa sai fidda daddan kamshi yake.
Ajje woyanta gefen tray din tayi sannan ta ɗauki ice-cream ɗin guda ɗaya ta fara sha. Har wani lumshe ido take saboda daɗin da ice-cream ɗin ya mata, hakan yasa tambuwal binta da wani shu'umin kallo kana ya sanya hannunsa ze ɗauki ɗayan, dan buge hannunsa tayi kamar irin bata sani din nan ba. Dan kadan ne ya zube a jikinsa dan sunkuyawa yayi da nufin daukar tishu tayi saurin jefa masa kwayar dake dunkule a hannunta. Dan turo baki ta yi iri cikin shagwaɓar nan ta ce
"Ayya beby ban kula bane sorryy" tayi maganar tana tura masa robar Ice cream din gabansa. Dauka yayi tare da fara sipping a nutse har wani dan lumshe ido yake domin gardinta na kai may har inda ya dace.
Cikin abinda bai wuce 5 mint ba ya tafi luuuuuuu, Arms dake tsaye bayansa ya taroshi zuwa jikinsa hannunsa ya sanya ya sakali kafadar tanbuwal din tare da ziro hannuwan tanbuwal ta cikin wuyansa. Dashi ya fara tafiya a jikinsa Riyya ta mara musu baya tamkar dama cen a taren suke.
Har bakin motarsu sukaje ba tare da kowa ya farga da abinda yake faruwa ba. Shigowarsu kenan cikin park din idonta ya sauke akansu kasancewarta mutum me tsananin karantar yanayin halayyar dan adam ya sanya kai tsaye ta gane cewar kidnapping ne sukayi, Duka sauran yan tafiyar nasu babu wanda ya lura da hakan sai ita kadai, "xcuse mee!"
Ta na fadar hakan tayi kamar mantuwa tayi ta jikin motar tawuce tare da manna musu wani abu dake hannunta, A kuma daidai lokacin suka tayar da motar suna barin wurin.
Ciki ta koma tana sake gyara zaman jakarta da daidaita nikaf dinta da taji kamar yana kokarin sarkafe numfashinta.

Kano

National Police Headquarters.
_Criminal Investigation Department (CID

Inspector kamal ne dake tsaye yaci gaba da kwararo bayanai yana mai nuni da welpaper screen din.
Hoton wani farin wani dattijone ne na'urar ta haske. Cikin tsananin sanin makamar aikinsa yaci gaba da fadin.
"wannan al'amari ba abinda za'aji ai shiru bane, tunda harya cutar da daruruwan mutane ta hanyar amfani da karfin iko hakan babban zunubi ne yallabai!. Be kamata mutum irin wannan yaci gaba da shakar yantacciyar iskar duniya ba.
Kamata yayi ace zuwa yanzu numfashinsa baya tare da gangar jikinsa, ko ace yana cen prison yana girbar abinda ya shuka! Yana yin duk wasu haramtattun harkalloli kwatsam kuma ace ya zama babban commondi of soldier's?"
Wata iskar bacin rai ya fesar tare da dora hannuwansa biyu saman desk din dake gaban yallabai din yaci gaba da fadin. " A koda yaushe damar shan iska muke basu!, shine babban kuskuren da mukeyi yallaabai a koda yaushe tazarar itace zarrarsu a garemu"
Chapter 32 · 0% Book details