← Book details Mikiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 45

Sashe 39

Mikiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

A nutse ya fada cikin motar kana sauran suka shishshiga, saida fadawan suka tabbatar da cewar ya rigada ya shiga kafin su shiga wani irin busa sarewar dake ma duk wani mahaluki cewar GAGALION ne a wurin. Domin busar da ake may ta daban ne irin me sanyin nance dake ratsa zuciya ya tsuma namomin jikin dan adam.
Wani irin lumshe ido yayi tare da budesu a firgice wata sabuwar izza da kasaita na zuwar masa.nan fa hankalin duk wani dake cikin airpot din yayo kansu duk da kasancewar tsakar dare na, amma sukam babu ruwansu wasun suma su yanzun shine rana a garesu.
Mandood dake daya daga cikin jama'ar airpot dim shima hankalinsa ba karamin tashi yayi ba. Su kuwa jama'ar sauran airpot din kowa kokarin gani yakai wurin tarin car's din, saidai security's sun hana hakan ta hanyar bashi garkuwa.
Mirza kan lafiyayyun motocin suka yi kyakykywan kwaltan airport din har zuwa EMAAR's MENTION.
Cikin tafiyar da bai wuce 50 minutes ba suka iso gaban katon get din masarautar, katon screen welpaper odysss na mention din na welcome nashi. Dauke da full name nashi shudaye da jajayen da blue din abubuwan ke zana sunan ak din. A get na farko, nu'urar dake tantance mutane ce ta tantance motar kana suka danna get na gana duk inda suka gilma sai kaga kowa a yanayi na kamewa da zuke numfashinsu na dan wani lokaci. Da wannan kaifaffan eyes din nashi yake bin ilahirin masarautar din da kallo.
Haka suka dunga shige get get ko wanne da kalan nashi tarban da sukema Ak din. Shi kuwa yana hakimce cikin tsumammiyar lafiyayyar kujerar motar ya nutse, sanyi da mayen kamshim sa na dada sanyi shi yin relax acikn kujerar mortar.
Gefe guda kuma daddadar kira'ar Afif muhd taj na tashi.
Nan din ma daya daga cikin bafadawan ne ya fito yana bude mai motar tamkar mai gudun tashin yaro a barci.A kalla saida aka kwashe sama da awanni goma ciff be fito ba, kana aka sake dibar wata gomar kafin almurin bakin takalmin shoe combat dinsa mai adon golden ya sauka saman maroon carpet din da aka shimfede masa ahankali. Sai da aka sake jan wasu sakannin kamar uku kana dayar kafar ma ta sauka sky blue din wandon cashmere nashi ya bayyana. Sannu a hankali sauran gangar jikin ma ta fito. Kaf wajen ya dauki wani irin tsitttt na bayyanuyar AK din tsaye akan diga digansa.
Tsaye yake kam akan tsahonsa na tsayayyen namiji da babu ko rankwafawa. Lallausan cashmere din jikinsa da ba sai an zauna bata lokacin lissafin kudin da suka lashe ba. sun masifar zauna masa da tabbatar da Ak din a matsayin jaruminsa mai gwara kan naira ta yanda duk yaso bisa damar da Allah ya bashi. Kamilalliyar fuskar san nan ma'abociyar kamewa da tsare gida kamar kullum a tsuke,
Saidai yau din ma dai akwai ring diamont barima manne da kunensa, hakama zanen tattoo dinsa mai fuskar lion na nan zaune daram. gashin nan daure daga kasan keyarsa ya dauresa har yana dan sauka jikinsa. Kai tsaye saiya fiti a hasalin balarabensa. Babu mai ganin idanunsa kasancewar toshe yake da shade mai duhu sosai. Wanda hakan shine ya sake bayyanar da taswurar halittar kyawun hancinsa daya zauna daram kan fuskarsa. Kafin kace mi tuni kamshinsa ya baje wajen, Gaba daya securityn ne suka sake kamewa kansu sukai cikin nuna tsantsar girmamawa a garesa. Wani irin dakune fuskansa yayi daidaj lokacin da fadawan ke zunewa akan gwawowinsu.
Sassanyan iskan dake kadawa da kamshin furanni ya sake shaka. Kafin ya fara takawa a hankali cikin yanayin izza da zallar sarautar dake ratsa shi gaba da baya. Kai tsaye part dinsa dake tsakiyar masarautar ya nufa dake dama zaid da kanshi ya gyara may tare da jesra sukai aikin.
Wohoho anan fa akeyinta mutanena Ni naga ikon Allah a wurin nan.
Tashin kai tashin gari kenan, na tabbata idan mutum karamar kwakwalwa gareahi babu abinda zai hanata juyewa a wannan lokacin, zanso ace kunga yadda Nera da nera ke kuka a cikin bangaren Ak. Luxury da luxury life ake magana malam, komai dake Cikin bangaren luxury da luxury ne ka iya siyansa sa, wani irin mahaukacin passage ne me kayatarwa, a nutsetstsen lafiyayyen parlounshi na farko oummey'nshi sai jesra ne a zaune domin gani suke tamkar kafin goben abinda suke son gani ga gudan jinin nasu ya disashe.
Wani irin murmushin bazatane ya bayyana a saman kyakykyawan farar fuskan shi da gudu jesra ta fada jikinsa tana saki kuka mara dalili. "Trouble meker har yanxun baki girma yhuyhu gurl"
Sai kuma yadan yi jimmmm tuno waccen yarinyan da yayi. Oummey ce ta karaso itama tare da hugging yaronta tana sama lallausan gashin kansa. Gashin kansa tadan ja tare da balla masa harara irinta uwa da dan nan.
"Ouchhhhh Ommu!"
Ya fadi yana kaiwa durkushe gabanta.....

*BY AMMEY LAYLERH*

*🦅 MIKIYA 🦅*

*~We want an end to oppression💪~*

https://chat.whatsapp.com/GiLzmY90dz17bRbw5yMYBg
____________________

*MARYAM NASEER*
~AMMEY LAYLERH ✍️~

✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~*

Page 45&46

# ROMANCE
# BLACK MONEY
# DEEP
# Hope
# courage
# Survival
# Humanity
# Inspiration
Chapter 39 · 0% Book details