← Book details Mikiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 45

Sashe 18

Mikiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Gudu sosai bugaggun motocin suke akan kwaltar da zata sadaka da wannan rantsatstsen Company'n na *LIVESTOCK AND FEEDING INTERPRICESS* duk inda suka gilma mutane basu hanyar wucewa suke, dubada da irin uban gudun da motocinsu keyi na tashin hankali. dukkan hanyar da suka biyo kowani mai abun ha wa  ƙoƙari yake ya basu hanya kar a halakashi. Wasu na Allah wadai da su wasu kuma na musu fatan shiriya ne kawai.

Ahankali yabuɗe idanunshi jin motocin sun tsaya buɗemai motar Armstrong yayi da sauri, fitowa yayi yana bin parking space ɗin wajen da kallo dayaji flowers da kallo komi looking neat a perfect kaman a dubai,
wani guy ne fari dogo ya ƙara so wurin yana sanye da baƙin suit da necktie a wuyansa hannunsa riƙe da Ipad ƙirar apple. Cikin girmamawa ya sarama Ak ɗin da yake jingine da jikin motar yayi folding hannun sa a kan ƙirjinsa.
Duk da yasan bai zama lallai ya amsa shi ba, Drectly cikin tamfatsetsen Company'n suka shiga, Armstrong, Axton, miles, ne kaɗai suka mara musu baya, duk inda suka gilma sai kaga idanu caaaaaa akan Ak kasancewar ba sananneba duk kuwa da cewar shine mai Company'n, Kasancewar Ak wani irin mutum ne mai murɗaɗɗan hali na rashin bayyana kai ko sirrinshi.
Mutum ne da idan ba sanin shi kayi ba baka taba sanin shine mai amsa sunan Companonin dake zagaye da Nigeria.
Don be yarda da baza sirrinshi ba irin yadda sanannun keyi shi yasa wani loƙacin harya shiga wuri ya fita ba'a taɓà sanin shine wannan me campanins ɗin, baka taɓa sanin shine wannan babban criminals ɗin, baka taɓa sanin shine *AK*. Kuma *ABDOUL-MALEEK EMAAR KUWAIT* He's not a social media fan.

Restroom ɗin dake babban Company'n suka shige su biyar cifff, suna zama Kabeer ya matso tare da ɗan ranƙwafowa kan Ak ɗin, ɗan danna screen din ipad ɗin dayake riƙe da shi ya shiga masa bayani ta cikin ƙaton magazine ɗin dake room ɗin, A kan wani business daya taso musu da manyan tycon na ƙasashen woje. Bayan sun kammala tattaunawar ne Kabeer yace "Sai 5 marcopolo buses dazamuyi amfani dashi for excursion's"

"All right okay"

AK ya faɗa daga haka suka miƙe daga zaman tattaunawar, bayan sun biya ta breakroom sunyi ɗinner, daga nan *A MALEEK MEMORIAL ORPHANAGE HOUSE* ɗinsa suka nufa. Bayan ya gansu ya buƙaci a bashi list na abubuwan da suke buƙata,nan suka bashi ba tare da sunga fuskar saba kamar ko yaushe. Wasu mahaukatan kuɗi ya tura ta account ɗin Managern gidan.
Daga nan *TEXTILE FEED INDUSTRY* suka nufa nan ma yaga yadda komi ke tafiya haka dai suka ta zagaya wurare daban-daban ta har dare, daga ƙarshe a wani haɗaɗɗen Restaurant suka yada zango nan sukayi ɗinner amma banda boss ɗin da yaki cin koma, Dole Armstrong ya mashi takawey .

_WASHE GARI_

Yana kwance akan ƙayataccen Royal Italian bed nashi woyar shi da yay ƙara ya farkar dashi, kunne yakai woyar bayan yayi peak calling woyar. "Boss anyi arresting ɗin Armstrong a hanyarsa ta maida Meerah ga iyayenta."
Wani ɗan banzan murmushi ne ya kuɓce mishi a bazata.
(Aikin ka nakyau Lion)
Ya faɗa acikin zuciyarsa a bayyane kuwa ajiyar zuciya ya sauƙe tare da datse ƙiran.

A cennn station kuwa tunda suka samu damar arresting na Armstrong suka kulleshi a wani matsiyacin ɗakin kulle masu aika mugwayen lefuka.
Kai tsaye hospital aka nufa da meerah bisa jagorancin Isa Manu daya samu damar ganawa da mahaifin meerah A safiyar jiya dan gane da neman aurenta ga babban ɗansa Salman. Kai tsaye dake Isa Manu sananne ne kasancewar shi Father's na manyan ƴan siyasa yasa malam Abdullahi amincewa da batun da yazo may.
Daɗi da ƙari kuma duba da yadda yayi ruwa yayi tsaƙi akan ɓacewar Meerah.
Saida lilitoci sukayi checking up nata suka tabbatar da babu wata matsalar bayan ta sleeping pawdern da suka shaƙa mata.
Amma ce ta kwana wurinta wacce take tama Allah godiyar bayyana mata DIDI'ƊINTA da yayi cikin amincinsa.

Tana zaune gaban gadon da MEERAH take kwance wacce tayi ƴar rama kaɗan wasu abubuwa ne suke mata kai da komo a tsakar kanta, Har bata ga sanda meerah ɗin ta farka ba sai ji tayi ta riƙo hannunta.... A hankali cikin muryan da yayi low sosae ta furta.
"Anne na yauma mafarkin nake yi ko kamar yadda na saba?".
Cikin maɗaukakin farin ciki Anne'n ta rumgume ƴarta cikin muryan kuka ta shiga faɗin. "Wannan ma mafarki bane DIDINA, wannan zahiri ne a zahirance Allah ya tseratar mana dake cikin amincinsa"
Kanta ta ɗora a kan ƙafafun Anne'n tanaji inama itace ta samu damar da hawayenta yake zuba kamar yadda na Anne'nta ke zuba, ƙara cusa kanta tayi a wuyan Anne dake sheshsheƙar kuka ta lumshe. ido tana sauraren kukan Anne'n.
Tana jin dama ita Allah zaiba damar yin irin wannan kukan, koba komai hawayenta zai wanko kaɗan daga cikin raunin dake danƙare a cikin zuciyarta. Saida Anne ta share hawayenta da bayan hannu kana ta ɗago fuskarta, ɗago MEERAH daga jikinta tayi cupping
fuskarta a raunace cikin muryan kukan ta furta.
"Yi kuka! Kiyi kuka MARYAM yi kuka!!!. Kana ki ɗauki hakan kamar haɗuwar hadarin kakane ya haɗa ,kuma ya baje ya ɓace ɓatt kamar komai ba'aiba. Karki bari abinda ya faru dake yayi tasiri a ranki dahar zai yi pinning ɗinki down. FIGHT DIDINA fight the feeling and move on!" Ai kuwa Atake ta fashe wani irin kuka me ƙona zuciya. Ɗauke guntuwar kwallar data saƙƙo masa malam Abdullahi yayi wanda yake tare da Isa Manu tare da Salman. Wanda ya kafe MEERAH da masifaffun idonsa ko kyaftawa babu, kaddai ace wannan zazzabar beb ɗin itace yarinyar da zasu yi Auren manufa da ita. Wllh Idan itace kuwa idan har aka aura masa ita babu shegen daya isa ya raba shi da wannan zazzafar bebyn.

_DOWN_

_catafares_

_Slow motions_

_AK K he's going to shikenan

*BY AMMEY LAYLERH

08104493215

*🦅 MIKIYA 🦅*

*~We want an end to oppression💪~*

https://chat.whatsapp.com/GiLzmY90dz17bRbw5yMYBg
____________________

*NA MARYAM NASEER*
~AMMEY LAYLERH ✍️~

✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~*

Page23&24

# ROMANCE
# BLACK MONEY
# Treason
# Strong love
# Right
# Women's travel
# The Secret Society
# Oppression

# KIDNAPPER'S
# Informants
# DEEP
# BEST LOVE

🤍🔥✅

★★★★
Chapter 18 · 0% Book details