← Book details Mikiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 45

Sashe 29

Mikiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Misalin sha biyu da kusan rabi na dare wasu motoci guda uku suke tafiya akan shimfideden titin inda motocin suka fiti daga wajejen daji dajin gefen hanya, kai tsaye suka yanki hanyar dazai sada su da airport.
titin shiru sosai yake babu wasu motoci dake wucewa banda su haka babu motsin ko wanne rai me numfashi a cikin tsakiyar wannan dare, benz guda biyu ne suka saka wata black din jeep a tsakiyan su me tinted windows. kaman daga sama power bike din Ak ya yanko daga cikin wata siririyar hanya da wani irin fitinannen gudu, gaban wadan nan motoci ukun yasha rike hanun bike din yay da hannu daya ya janye dayan hanunshi daga dayan hanun bike din yakai hanun tabayan wandonshi ya ciro karaman bindigar shi daya saka mata silencer abakin sabida kar dai kara. A kuma daidai lokacin motocin su arms suka kayo wurin suma, domin satar hanya yayi su kuma dake ankare suke da duk wani motsin uban gidan nasu ne, ya sanya suka rufo mai baya ta cikin budaddiyar hanya.
Kallo daya yama motocin su arms ya dauke kai, be fasa ba ya saita bindigarshi tare da harbe tayan jeep din tsakiyar,
ya harbe na jeep.
Wani irin juyi motocin motan ta shiga yi sakamakon fashewan tayan a guje mutanen dake sauran motocin suka bubbude motocin suna fitowa a rude domin bama yan uwansu dauki.

Kai tsaye wajen motar Farouq audu bashasha suka nufa da suke protecting suna gyara bindigar su batare dasun damu da jinin da jikinsu ke yiba. Koda suka karasa gaban motar saidai me?, wayammmm ba farouq a cikin motar babu dalilinsa daga shi har yarinyar da zasu bar kasar da ita bisa umarnin mahaifinsa audu bashasha. Daya bukaci da yaron nasa ya taho masa da RIYYA din cennn kasar India inda yake jinyar kansa.wannan shine makasudin fitiwar su kenan a cikin motocin.

”wat is happening?” daya daga cikin yaran ya tambaya ya tambayi sauran waima me yake faruwa?. Hhhhhhh Ashe her boss in naku sleeping powder ya bade shegu dasu a lokacin da suka yunkuro da niyar kaima ogansu dauki. Kowa sai ya shiga waige waige sai kuma dukansu kusan a tare suka hade baki wajen furta
”WHAT?”
Da karfin masifa ganin hasken rana a akan idonsu, saurin kara mutsitstsike idanunsu suka shiga ganin dai tabbas hasken rana ne ya sanya daya daga cikin yaran furta.
”Impossible”
Da karfin gaske, in banda rainin hankalima taya za'a ce haka ta faru dash to waye ya musu wannan aikin?, *ÊÀGLÉ ÆK* Idon Sa yakai kan kan dan note din dake dauke da sunan ak din cikin salon burgewa akayi shi akansa rubutun.
Wani ihu ya sanya yana wawuro Dan sauran note din tare da kukuruwa yana matse note din akan tsakiyar kirjinsa.
Sai kuma ya ware ma yan uwansa note din Yana furta *ÆK* da karfin gaske.
Duka a tare suka dune shi ”Yeah wannan aikin bana kowa bane sai tantirin tantirai, nifa Wllh da zanyi ido hudu da wannan ak din ba abunda zai hanani rungumesa harma na furta masa *I LOBE YOU*”
Ya fadi yana kara nade note din a cikin duka hannuwansa biyun.

Gudu take sosae akan Pawer bike ride dinsa motocin su arms na mara mishi baya suma a mugun gujen. Suna kaiwa cikin hadadden mention dinsu kai tsaye samansa ya haura.
Arms ne da yake dauke da Riyya ya shimfideta akan sopar Palon tare da furta
”RIYYA? RIYYA!!! Weak off”
Shiru babu alamun ma tana jinsa ganin ko motsi taki yine ya arms yakai zaune kan sopar shima dago kanta yayi tare da tapping fuskarta adan rude yace
”RIYYA! Hey Riyya”
Sai kuma yayi saurin kallon axton tare da furta
”get me the water pleaseee”
Ya fada da karfi domin shi kadai yasan irin halin da yake ciki na tashin hankali.
Fesa mata ruwan sanyin da axton ya kawo masa yayi. Wani gauron numfashi ta kawo a wahale tare da bude kyawawan eyes nata.
Akan Armstrong ta fara sauke ganinta.
Ai da mugun gudu ta rungumeshi tare da fashewa da kuka tana fadin.
”YAYA!!!”
Da sauti me karfin gaske tana sake cusa kanta cikin kirjinsa.....

*BY AMMEY LAYLERH*

*🦅 MIKIYA 🦅*

*~We want an end to oppression💪~*

https://chat.whatsapp.com/GiLzmY90dz17bRbw5yMYBg
____________________

*MARYAM NASEER*
~AMMEY LAYLERH ✍️~

✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~*

Page 35&36

#AK POV
#MEERAH RIYYA join
#kamal R
#Curruption
#POVERTY's
#Deep friendship
#playful

_______________

*Kano*

____”Baban Mariya har yanzu ba'a dace ba ko?”
Yar matsakaiciyar matar ta jefawa mijinta tambayar cikin nuna alhini karara. Ijiyar zuciya ya sauke tare da fadin.
”Ban samu ba su'ada” ya fada cikin rashin jin dadi da mutuwar jiki. Kallonshi tayi cikin tsananin tausayawa itama, kallonta yayi ganin yadda take kokarin maida kwallar da suka mata ido. Cikin tsananin tausayinta dake cike a ranshi ya furta.
”Na tambayi duk wanda na sani amma ga baki daya kowa yaki taimakona!, damuwata itace abinda ka Iya faruwa da kuma me gobenmu zata haifar mana”
Hannuwanta da suke manne a cikin juna ta matse sosai tana son hana rauninta bayyanuwa a gaban adalin mijinta, domin karya ga rauninta hankalinsa ya sake tashi fiye da yanxun. Sama ta kalla cikin raunin murya da nuna jarumta tace.
”Àduk lokacin da Ubangi ya jarabceka ka mika al'amurranka gareshi kawai. Anan ne zaka gane cewa lallai da akwai dalilin daya sanya ya jarabcekan”
Wasu hawayene masu zafin gaske suka sakkomai
"makomar mariya shine abinda yafi komi tsaya min a cikin rai da rayuwana!, ina tsoron a karo na uku aurenta ya fasu akan rashin kayan daki umayma"
malam yusufa ya fadi cikin nasa hawayen daya gaza boyuwa a garesa.
murya a tausashe wacce ya kira da umayma ta furta . "kada ka samu damuwa malam insha allah allah shine zai kayo mana dauki lokacin da bamuyi zata ko tsammata ba bi'izinillahi"

"amma ke ina iya ganin damuwa akan fuskarki umaymatu, kuma kinsan bazan iya juriyar hakan ba"
da sauri ta juya tana barin wurin domin kada ta raunatawa mijin nata zuciya.....
kanta ta hade da jikin bakin kofar da take tsaye hawaye masu zafin gaske na zubo mata. tana tsananin umminta da babanta, wai sai zuwa yaushe rayuwa zataji kansu su fita a halin kani kayin da suke a ciki na halin rayuwa? sai zuwa yaushe suma zasu dandani irin yadda zakin rayuwa yake?.
"Ya Allah!"
mariya ta furta cikin wata iriyar raunatacciyar murya. sallan magriba da aka kira ne ya fitar da baban mariya cikin tawakkali da karfin zuciya.
Cikin sanyin halinta kamar koda yaushe anutse ta mike kanta duke a kasa, saidai ahankali take matse lips dinta da kyawawan teeth dinta. kai tsaye gaban dan karamin fanfom dake gaban bishiyar mangoron gidan ta nufa....alwala ta daura tana jin duk ma yanayin baya mata dadi baki daya.

shi kuwa malam auwalu da mutanen anguwa ke kiransa da baban mariya bayan idar da sallar isha'i, dake shine lilaman masallacin anguwar yana zaune har saida kowa ya gama fita kana ya mike da zimmar fita. wata farar embulons ce ta fado daga saman jikinsa cikin rawar jiki ya shiga waige2 saidai baiga kowa ba....
saurin fitowa yayi a masallacin da shi ya fara cin karo,wani irin dafe kansa malam yusufa yay. me yasa aduk lokacin da yake da bukatar taimako sai shine kadai me taimakonsa.
jiki a sanyaye ya karasa xuwa gaban farar motarshi da yake tsaye, sanye yake cikin kakin yan sandan shi kamar kullum. "Na rasa wanda zai taimakeni amma ba wanda ya taimakamin, duka na tambaya haka ban samuba! amma kai bamma tambayeka!" ya kasa karasa maganar shi sabo da kukan da yaci karfinsa.
"Aina riga na fashimci komai dana kalli cikin idanuwanka. wannan ba komai bane"
inspector KAMAL RANO ya fadi
"bansan ta yayene zanyi wani abu game da yata ba. ban kuma san da wanne irin idon zan dubesu ita da mahaifiyarta na fada musu cewar auren ya fasaya!. bayan fitowana daga cikin gida zuwa masaaci. KAMAAL?"
Malam yusufa ya kurayi sunan shi cikin karyewar zuciya. cikin tsananin.zafin dake narka kirjinsa ya furta.
"A yau da kai danane dana zartar maka da wani hukunci kai tsaye! ko kuma in baka umarnin aikata min wani abu"
idonsa daya tara kwalla ya dago yana kallom baban mariyan. kafin cikin muryan da kai tsaye ba zaka iya tantance taba yace.

"Ya kuma zakace haka baba? kenan niba danka bane kome?. matsayinka a wurina ya wuce makwabtaka ni KAMAAL IDREES RANO A MATSAYIN MAHAIFI NAKE KALLONKA, ka bani ko wanne irin umarnine ni kuma in aiwatar maka shi cikin sauri da tsananin biyayya"
hawaye da kuka ne suka zowa baban mariya lokaci daya, cikin jin yakini da kuma karfin zuciya ya furta..............
Chapter 29 · 0% Book details