← Book details Mikiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 45

Sashe 41

Mikiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

"Ka sani HAU'WA KULU bata yafiya haka bata daukar kuskure koda kadan ne bare kuma me girma irin naka, ka sakar min da hannun yaro daka rike shi da kazamin hannunka da bashu da tsarki!. Ka sani taba hannun mutum irinsu Al-hussien sai hannun daya cika duka sharrudan musulinci, ba kazami irin naka ba daya gama cakuduwa da dattin zina"
Atare Oum, Adeenerh, jesra, al-mustapha suka wani irin kulle idonsu da karfin masifa.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!"
Oum ta furta tare da RAZEENERH da suke kira da MAH. Mahaifiya Almustapha sai kuma yarta ta fari wacce tayi batan dabi sama kasa aka nemeta aka rasa.
Shi kuwa boss din wani irin tsuma jinin jikinsa ya dauka.
A fusace zaid da bazai iya jurema cin mutumcin da ake ba biyuninsa bane ya mike.yana toshe kunnuwansa tare da furta
"STOP"
Mandood ne ya mike tsayen shima ta hanyar tarar zaid din yana jefa masa wani shegen kallo tare da fadin.
"Me yasa kake da taurin kaine?, Idan ba'a kasa dakai ba baka gaggawar dauka domin gudun abin fada ko martanin da za'a iya maida maka"
Wani shegen kallo ya wurgama mandood din tare da cewa.
"Niba rago bane da zan zauna a gaban idona naga ana aibanta jinina na kyale haka! Taurin kaine dani! Ni mutum ne da ako da yaushe yake cin nama da nama karya kasuwan nake nabi ta kansu na mitsitstsikesu domin na gama amfana da tsokar jikinsa"
Luuuuuu Ak yaja idonsa dayabi zaid dashi kamad zai kulle su gaba daya sai kuma ya budesu war akan twins dinsa gudan jininsa zaid.
Wani irin fashewa da kuka Moh tayi tana mikewa tsaye tare da fadin.
"Tabbas jinin Maryam masifa ce a garemu, ni dama tun farko banso hassan ya aurita ba wllh! Har iyaka na ketara masa akan auren wannan me bakin jinin, na rantse ba zata shigo cikin gidan a matsayin matar aure amma saida ta shigo tazo ta haifa mana jaraba da masifa a masarauta"

"Ashe kinga kenan baki da matsayi da iko akan dan da kike ikirarin naki ne, duk da kin yankamar iyaka amma saida ta ketara, kince ba zata shigo ta shigo! Ko wanne mutum yana da gari kana yana da iki a inda yake. Ba tare da kin tare ta daga shigowarma kuma ta shigo harta haifa miki magadan masarautar EMAAR's kina ji kina gani wannan masarautar ta zama tata. Wannan garin ya zama nata bayan wannan mene bakyason ta sake tsallaka miki, wannan masarautar tamu ce garin ma namu ne a gaban idonki zamu mulki masarautar dama kasar da kike ikirarin Oum bazara shigo ba. Saidai masu hadiyar zuciya su hadiya in yaso ta buga su mutu"
Ak ya yaboma Moh maganfanun da tunda uwarta ta haifeta ba'a yaba mata koda kwatancinsu ba.
"ABDOUL-MALEEK"
Muryan Oum ya katse shi daga wata maganar da yake shirin sake yanko mata.
Hatsaniyace sosai ta kaure a cikin dakin kowa yaki ya rusuna kowa ji yake da nasa zafin kan. Abinda ya rusunar da rigimar nasu faduwar da Oum tayi. Wannan shine dalilin lafawar komi haka Ak yama Oum dinsa daukar jarirai ya fice da abarsa zuwa clinic din masarautar, Shine da kansa ya duba Oum nashi kasancewarsa dactor, kana pilot ne idan yaso babu inda baya ketawa a kasashen duniya. Kana gashi Babban soldiers wanda matakin farko ma da Marshal ya soma.....

⭐Washe gari ⭐
A nutse yake Sakkowa daga matakalar benen zuwa entrance din da zai sada shi da bangaren oum dinsa. yana sanye cikin wasu fitinannun lallausan farin yadi. yayin da kuma ƙkafarsa ke sanye cikin wani black combat toms mai kyau irin na yayan sarakunan nan, Sai wata mini jacket din daya dora saman kayan yar filic da ita.
babu abinda ke tashi ajikinsa sai wannan fitinannen kamshin turaren nan nasa me azabar tsada da bama wanda yake shakarsa cikakkiyar nutsuwa ta musamman.
Tamkar wanda akema wanka da madara haka farar fatar jikinsa ke daukar idon me kallonsa. Cikin cikakkiyar takun da kallo daya zakayi masa ka gane cewar kakkarfa ne sabo da motsa jikin da yake aduk kwanan duniya ta hanyar machine gams.
Blue eyes din nan rufe cikin wani luxury sun glasses wanda ya sake bayyana taswirar karan hancinsa da yake mike ziyat tamkar da biro aka zama masa shi daram. pink lips din nan nashi sai wani kalan glowing yake tsananin taushin na bayyanuwa wa me kallonsa, kallo daya zakama Ak ka gane shi din me kyau ne kana na musamman masha Allah,domin allah ya wadatashi da komi najin dadin rayuwa. cike da kwanciyar hankali da nutsuwa yake takawa irin takun dake nuna shidin kakkarfan namiji ne kana tsayayye. Marar daukan wargi da in Manners din nan.
Kai tsaye babban katafaren parlourn Oum dinsa yama tsinke wanda girmansa yake dauke da wasu tsadaddun furnitures, parlour ne mara tarkace amma yana da kyau na fita daga hayyaci. Kayatattun royal cushion din dake zagaye da parlourn sunyi may kawanya, daga tsakiya kuma akwai wani shimfiɗaɗdiyar red carpet da throw pillows akai, sai wani ƙkaramin round table daga gaban wani kebantaccen rug, sai babban plat screen plasma din da ya kusa cinye bango guda na parloirn don girman shi. iskan A/cn dake kasawa kai tsaye yake fidda wani irin daddan yanayi a cikin parlourn, dubansa ya kai ga ƙkaton agogon dake manne a bango wanda yake ƙkawace da zanen pop, tare da pisc na Oum shi tare dame martaba.
⭐10:25am agogon ya buga cire pcarp din kansa yayi yana kallon ƙyakkyawar fuskan Oummey'nshi dake zaune kan caution mug ne a hannunta me dauke da zazzafan ruwan bunu marar madara.
Kallo daya zaka mata kagane ita din mahaifiyarsa ce saboda kamar dake tsakaninsu, lumshe idanunsa yayi hadi da dan sauke numfashin ganin zaune cikin koshin lafiya da yayi.
Cikin amon muryansa mai dadi da nutsuwa yace
"Takabbalallahu minna wamin kum alaina wa'alaiki ya Oummey! ". Shafa tulin sumar kansa tayi wanda yasha gyara mai kyau da sheki yayin da yake durkushe agabanta ya dafa hannayensa duka biyu a ƙkafarta, cike da kulawa tace
"Amin barkan mu da wayewar garin Alhamis lafiya habeebty"

Jesra dake tsaye hannuwanta sarke akan kirjintane ta dan turo baki gaba tare da fadin.
"Aifa shikenan nikam tawa ta kare tun da nakan gaban goshin ya dawo"

Cikin yanayinsa na rashin son magana yayi dan murmushi yana faɗin
"Kina kishi da hakan ne jes?”
ya fadi hakan yana maida kallonsa ga mahaifiyar tasa yana faɗin
"Ya Oummey nah ya saukin jikin ki?".
" Alhamdulillah naji sauki tun da ka dubani HABEEBT?,kaje ga Me martaba ya kamata ka sake auna yanayinsa Garga"
Kansa yayi noding yana mikewa tare sa barin shahin......

*BY AMMEY LAYLERH*

*🦅 MIKIYA 🦅*

*~We want an end to oppression💪~*

https://chat.whatsapp.com/GiLzmY90dz17bRbw5yMYBg
____________________

*MARYAM NASEER*
~AMMEY LAYLERH ✍️~

✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~*

Page 47&48

# ROMANCE
# BLACK MONEY
# DEEP
# Hope
# courage
# Survival
# Humanity
# Inspiration

🤍🔥✅✅✔

⭐ NIGERIA ⭐

A kullum duniya canjama bawa ajin karatu take yau din kace kawai zata tabbatar maka da hakan, musamman idan kaga ta banbanta da ƙkaddarar jiyanka!. Rayuwa mataki biyu ce Acikin kowacce duniya duk wacce kaddararka ta zabar maka zata kaika ne zuwa makomarta, sabanin shine kawai dace wajen banbance nagartacciya ko gurbatacciya.
A yau dai ga merrah wacce take dab da amsa sunan mrs Salma isa manu, wanda komi da komai ya gama kammala kansa daya danganci bikin aurensu wanda ya rage kwanaki biyu takkk.
Chapter 41 · 0% Book details