← Book details Mijin Marigayiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 59

Sashe 9

Mijin Marigayiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana kwanciya hawaye ya fara bin idonta; wannan wace irin rayuwa ce? Wai dama haka ake aure ko kuwa itace bata dace ba? Shikenan shi da ‘yayansa ne kawai mutane? Kiri-kiri sai a kirkiri laifi a dora mata kuma a saka ta bada hakuri. Da ya barta da yaran tabbas tayi niyyar ta rikesu kamar ita ta haifesu, domin har addu'a takeyi kada Allah ya bata ikon cutar dasu. Sai dai zuwa yanzu gaba daya sun fice daga ranta, duk wata kauna da ta tanada don ta nuna musu bata jin zata iya tunda ga dukkan alamu ma ba zai barta ba. Shi ba so yake ta nuna musu kauna ba so yake kawai ta bauta musu, bata jin zata iya hakan kuwa.

………

A cikin wannan yanayin Khadeeja ta cigaba da lallabawa tana iya kokarinta wajen kulawa da yaran da gidan gaba daya.

Kwana biyar aka yi da lockdown aka bada wuni daya mutane su fita su dan yi sayayya, don haka a wannan ranar Khadija take sa ran dawowar Habi mai aikinsu tunda Mustapha yayi wa Yaya Jidda magana.
PAGE 35
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Tun safe take kiran Habi amma har azahar ba a daukan wayar sai bayan azahar sannan Habin ta dauka. Nan ta sanar da ita cewa mahaifiyarta ce bata da lafiya don haka wanen mai magani suka je, sai dai ko zuwa lokacin da za a sake bude gari shine zata samu ta taho idan mahaifiyar tata ta sami lafiya.

Kamar tayi kuka haka ta ji domin tana ganin kamar dawowar Baba Habi zai rage mata wata wahalar; gashi azumi saura abinda bai fi kwana goma ba.

A take dabara ta fado mata, ta dauki wayarta wadda ta juye; har ta nemo lambar Mommy zata kirawo sai kuma ta fasa ta kirawo lambar Baffa. Bayan sun gaisa ta sanar dashi tana so Nabila ta zo ta tayata zama zuwa lokacin da za a sake Bude gari in ya so sai ta tafi. Sai da ya Dan yi jim sannan yace ‘Kiyi hakuri Khadeeja,ba zata zo ba, haka aure yake. Kanwarki balagaggiya ba muharramar mijinki bace gashi gidanku ba wani Kato ba, ba zai yi ma'ana ba ana wannan zaman na wuni a gida na turo miki ita. Amma dai zuwa lokacin da za a sake Bude gari zan sa Mommy ta duba Miki dattijuwa wadda zata zo idan Kuma Mai aikin naki ta dawo ma shikenan. Kin gane ko?’

'Na gane Baffa.'

Sukayi sallama ta ajiye waya.

Wani malolo ne ya taho ya tokare mata makogoro saboda takaici; yanzu Baffa ba zai bata Nabila ba kenan yana wani zance? Take hawaye ya wanke mata fuska, ta dauki wayarta ta shige daki saboda kada yara su sameta tana kuka.

Tana ji tana gani aka sake mayar da garin aka kulle babu Baba Habi babu Nabila, haka ta cigaba da bautawa Mukhtar da ‘yayansa babu abinda ya sauya.

……….

Saura kwana biyu azumi aka sake bude garin na wuni daya saboda a dan yi sayayyar azumi. Tun da safe Mustapha ya sa ta shirya yaran ya kwashesu sai gidan Hajiya. Basu dade da fita ba aka buga mata kofa, kamar ba zata Bude ba da oda tana tunanin ko almajiri ne. Amma sai ta daure ta fito don ta bude da aka cigaba da bugawa.

Tana budewa ta ci karo da Mommy tare da Nabila, Ahmad ne ya ajiyesu ya juya sai da yamma zai dawo ya daukesu. Tun a bakin gate ta rungumo Mommy suka shigo gidan tare tana ta murna.

A nan parlor suka baje, ta sa Nabila ta dauko musu ruwa da lemon suna Sha suna hira.
PAGE 36

MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Daga baya Nabila ta tashi ta fara gyara mata gidan; ta barsu a zaune ita da Mommy suna hira.

Mommy tace ‘Baffa dai yace kada a bar Miki Nabila, Mai aiki Kuma Ina ta cigitawa. Kin san yanzu duk tsoro ake ji saboda wannan lockdown din.’

'Watakila ma yau Baba Habin zata dawo, zai iya yiwuwa ma tana can gidan Yayarsa tasa sai ya taho da ita idan zasu dawo.’

Mommy tace ‘To Allah yasa.’

'Ya jikin naki?’

'Da sauki Mommy, yawun nan ne bana so wallahi ga wani yawu da bana iya hadiyewa.’

'Wannan Kam hakuri Zaki yi, Allah ya raba lafiya.’

Jimawa kadan Mommy tace ‘’yayan naki basa baki matsala ko?’

'Babu matsala Mommy,shine ma yake sa mana Ido wallahi amma da zai barsu yaran basu da matsala.’

'Da sauki ma idan hakane, Shima a hankali Zaki dinga nuna masa in Sha Allah zai gane idan ya ga kun hade Kai.’

'Hmmm!’

Haka Mommy ta wuni a gidan nan tana kokarin ganowa ko da matsala, sai dai har ta tafi bata ga inda gagarumar matsalar take ba. Ta dai bawa Khadeeja shawarwari kuma da alkawarin sami mata mai aiki da zarar gari yayi lafi.

La'asar tana yi Ahmad ya zo ya daukesu suka tafi.

Suna tafiya ta dauki waya zata kirawo Mustapha taji ko Habi ta dawo, sai dai kafin wayar ta shiga ta jiyo motsinsu yana Bude gate don haka ta mayar da wayar ta ajiye.

Tun kafin ya zauna ta kula kowa ya shigo bata ga Baba Habi ba, tace ‘Ina Baba Habi? Na zata tare zaku taho.’

'Hm! Wai mahaifiyarta ta rasu jiya don haka ba zata dawo ba sai bayan Sallah, lokacin an yi 40 days.’

Tace ‘Subhanallahi. To don Allah kace da Yaya Jiddan ta sami mana wata saboda azumi, wallahi hidiman da yawa ga lockdown.’

Ya karaso ya a zauna sannan yace ‘Na gaya mata, ta dai ce wai wahala suke saboda lockdown tsoron baro gidajensu suke yi.’

'To ga mu ga Allah, Mommy ma ta zo bayan kun fita itama na ce ta cigita mana.’

A ranar haka Khadeeja ta kwana cikin zulumi saboda fargabar yanda zata yi da aikin azumi. Kafin gari ya waye dabara ta fado mata, tana fatan Allah ya sa kada wani abu ya kawo matsalar.
PAGE 37

MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ko da gari ya waye sai wajen 10am sannan ta yiwa Mustapha bayani wanda ya bata dama sannan ta tafi gidan su Ummi; makotansu inda a nan ake yiwa su Afaf kitso.

Ta samu ta roki arziki a wajen mahaifiyar Ummi a kan ta dinga zuwa tana tayata aiki zuwa bayan Sallah. Ba tare da wata matsala ba ta amince mata tunda dama ita kewa yaran kitso.

Tun a ranar Umminta fara taya Khadeeja aiki, gashi bata da kuwa don haka cikin walwala suka wuni. Kullum haka zata bata abinci ta ce ta koshi sannan Kuma idan zata tafi ta zuba mata a falsak; ga alkhairi Kuma kullum tana yi mata.

—----
Ranar da aka tashi da azumi Alhaji wato mahaifin Mustapha ya kirawoshi da safe ya sanar da shi rasuwar abokinsa Alhaji Rilwanu; nan yayi masa bayani cewa ai Covid 19 ce ta kashe shi don haka mutane kadan ne ma suka je jana'iza. Matarsa ma tana kwance Kuma itama COVID 19 din ake tunani don har an kaita isolation center.

Khadeeja tana shiga dakin ya bata labari, tace ‘Allah ya sa ya huta. Ashe Corona din nan gaske ce.’

Da mamaki ya kalleta yace ‘Oh, ke da baki ma yarda ba kenan? To wallahi ki kula sosai don babu wahala an dauka. Ai shi yasa ma aka saka lockdown don idan dai mutane suna yawo to zasu yi ta rabata a junansu. Kina ji dai Baba Rilwanu ya rasu kuma an saka matarsa a isolation. Garama ki San wa kike bari yana shigowa gidan nan kada ki kwaso mana, especially ke da kike da ciki.’

Ta Dan zaro ido ‘Allah ma ya kiyaye, in Sha Allah we are safe.’

Suna nan zaune ya daga waya ya kirawo Alhaji yayi masa gaisuwar abokinsa, suka dauki lokaci suna waya tana jinsa yana ta amsawa da eh, ava, toh, haka har suka gama wayar.

Yana ajiye wayar ya dubeta yace ‘Ai muna da Dettol ko?’

'Eh akwai babbar roba ma kuwa.’

'Don Allah a dinga goge duk wani surface na gidan nan da ruwan Dettol, musamman hannuwana kofa da guraren da mutane suke tabawa. Duk wani shige da fice ma a hakura da shi don wallahi corona Dina nan da gaske take, sai mutuwa ake. Gara a daina shigowa gidan kada a kwasawa yara muna zamanmu lafiya.’

Ta gyada kai ‘Hakane, ai da yake ma babu wanda yake shigowa gidan sai Ummi, itama da ta gama aikinta take fita.’
PAGE 38
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ta gyada kai ‘Hakane, ai da yake ma babu wanda yake shigowa gidan sai Ummi, itama da ta gama aikinta take fita sai dai da yamma kuma nace ta dawo ta tayani girkin Sha ruwa ta tafi.’

'To sai kun yi taka tsan-tsan.’

………

Har azahar tana ta jiran Umminta zo ta gyara gidan amma bata zo ba.

Can wajen 2pm suna zaune a parlor gaba dayansu aka buga gate. Da kansa ya tashi yake ya bude, jimawa kadan ya shigo Ummin tana biye da shi.

Ya koma ya zauna a inda ya tashi.

Ummi na shiga gidan Shukra ta tashi da gudu ta rungumeta tana cewa ‘Ummi na tsefewa Baby na kanta yau ita Zaki yiwa kitso.’

Ta dauketa ta mika mata hannu suka tafa tana cewa ‘Yauwa kawas, bari nayi sauri na gama shara mu zauna kitso don babynki anti yalash ce.’

Ta sauketa tana ta murna.

Ta rage tsawo ta gaida Khadeeja, har zata shige kitchen Khadeejan tace ‘Shine baki zo da wuri ba yau Ummi? Gashi annfara azumi.’

'Wallahi Anti cikin gari muka shiga.’

Da mamaki tace ‘Ke Ummi ana lockdown din kike fita.’

'Yo Anti ai mu a kasa muke yawonmu, babu inda bam zuwa.’

'Ai kuwa za a kamaku Ummi ko ku kwaso cutar da ake gudu.’

'Ta masu kudi ce Anti.'

Ta shige kitchen tana dariya.

Bata dade da shiga kitchen din ba Shukra ta dubi Khadeeja tace ‘Anti zan Sha ruwa.’
Chapter 9 · 0% Book details