← Book details Mijin Marigayiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 59

Sashe 10

Mijin Marigayiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga nana ta kwalawa Ummi kira ta debo ruwa ta mikowa Shukra. Kadan ta kurba har Ummin ta juya zata koma kitchen din Shukra ta kurbi ruwan ta mika kofim tana cewa ‘Na Sha Ummi tafi da shi.’

Ta karbi ruwan a Kofi ta juya ta nufi kitchen din, tana juyawa ta kafa kai ta shanye ragowar ruwan sannan ta wuce kitchen din.

Mustapha ya kalli Khadeeja yace ‘Wannan yarinyar kuwa ta san me take yi? Ana maganar Corona tana abubuwa anyhow. Ta gama yawonta a gari Kuma ta zo tana daddumar abubuwa kuma har tana using utensils din yara? Corona din nan fa is real.’

Khadeeja ta kalleshi ta langabar da Kai tace ‘Kayi hakuri zan yi mata magana.’

'To Allah ya kiyaye.’
PAGE 39
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Nan da nan Ummi ta gama aikin gidan ba tare da wata matsala ba. Bayan la'asar Kuma ta dawo. Itace tayi komai don Khadeeja kujera ta saka ta zauna a kitchen din tana gaya mata abinda zata yi, shi kuma Mustapha yana zaune a parlor shi da yaransa suna kallon TV.

Kafin magriba sun gama komai Khadija ta kawo ta jera a kan carpet domin Mai gidan ya ce yau a kasa zasu Sha ruwa ba a table ba. Zobo ne mai sanyi, sai dankali da kwai, daga gefe kuma ga farfesun kaza da kuma couscous da sauce. Kafin a fara kiran Magriba ta zubawa Ummi komai ta sallameta ta tafi.

Sai da aka idar da sallar Magriba sannan suka zauna shan ruwa; kowa da plate dinsa wanda Khadeeja ta zuba masa abinci ga soup bowl a gefe, ita kuma Shukra kwanonsu daya da Khadeejan. Bayan ta gama zuzzuba abincin kuma ta fara kokarin hada musu shayi. Bayan ta gama ta hada nata sannan ta dauki karamin kofi zata zubawa Shukra daga nata login, Mustapha ya dubi kofin yace ‘Wannan ba kofin da yarinyar nan ta sha ruwa da shi dazu bane?’

Ta cigaba da juyewa tana cewa ‘Shine, ai ta wanke shi.’

'Kika sani? Bayan ruwa kawai aka Sha da kofin kuma kina zaune a nan tayi wanke-wanken, idan fa kifewa kawai fayu bayan ta gama dambara baki a jiki?’

Ta gyara zama zata mikawa Shukra shayin yace ‘Ya zaki bata, ki canza mata cup mana. Ba kya jin me nake fada ne.’

Ta kalleshi kamar zata yi magana sai kuma ta fasa; ba zata iya fara musu da shi yanzu ba domin bata ma da kwarin da zata iya doguwar magana don kishiruwa ta galabaitar da ita a wunin yau. Ta tashi ba tare da tace komai ba ta wuce kitchen, ta zubar da shayin ta dauko wani kofin ta dawo ta sake hadawa Shukra wani shayin. Haka suka gama shan ruwan ba tare da ta kula kowa ba sai Shukra da suke cin abinci daga kwano daya.

…….

A kwance ya sameta a daki, ba wai bacci take yi ba kawai rufe ido tayi tana hutawa saboda yanda jikinta yake ciwo. Duk da babita tayi aikin gidan ba yau amma ta gaji, musamman da yake an yi kishiruwa. Gashi bata son ta ajiye azumin saboda ko bata yi ba ma bata iya cin abincin kirki; garama da tayi azumin ta samu bayan shan ruwa ta ci couscou ta koshi.
PAGE 40

MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Da sallama ya shigo dakin, ta dan juyo ta amsa sallamarsa, bayan ya zauna yace ‘Sai yaushe zaki shirya yaran su kwanta ne?’

Tace ‘Barinsu nayi da yake daren na azumi ne kuma gobe ba fita za ayi da safe ba, zuwa 10pm sai a kwanta.’

'Ok, haka ne kam.’

Suka yi shiru na dan lokaci, jimawa kadan yace ‘Ina ga kiyi hakuri da aikin nan wannan yarinyar ta daina shigowa gidan nan. Ki bari a sami saukin cutar nan tunda kina ji tace cutar ma ta masu kudi ce don haka ba zata daina yawonta ba.’

Ta tashi zaune takalleshi sosai tace ‘Don Allah ka bari, wallahi nayiata magana kuma gobe ma zan sake mata magana. Ka ga ga azumi wallahi abincin shan ruwa kawai ya isheni balle ga su wanke-wanke da shara, zan mata magana na san in sha…’

Kafin ta karasa ya katseta yace ‘Ki fahimceni ba wai don bana son ta tayaki aiki bane, nima na fi so a tayaki. But she's putting all of us at risk, tunda zata ke ta gama yawonta a gari sannan ta dawo ta shigo mana gida tana mu'amala da yara da kuma ke anyhow. Bana son a sami matsala please ki sallameta kawai, idan pandemic din nan ya wuce zata iya dawowa ai.’

‘To ya zan yi da aikin? Gashi ba dadi nake ji ba, kamar kana mantawa da cikin jikina.’

'Ni ban ce miki na manta na, Amma aikin gidan nawa yake? Duka ba wani abu ne da zai gagareki ba fa, kina ma fa da damar ki ajiye azumin idan yana wahalar dake ba wani abu bane. Amma aikin gida ai ba abinda zai gagareki bane, itama Ma'un haka take hadawa da ciki da goyo kuma da aikin gaba daya. Amma gaskiya a hakura da shigo da kowa gidan nan for now, gaskiya. Da safe ma idan ta zo daga gate zan ce ta koma. Kiyi hakuri ki fahimceni, ke kanki you are at risk idan ta kwaso cutar nan ta shigo mana da ita gidan nan.’

Cike da takaici ta sunkuyar da kai tace ‘Shikenan, duk yanda kayi.’ Ta zame ta kwanta.

Ya bude baki zai yi magana sai kuma ya ga gara ya kyaleta ta huce zuwa an jima ya sake yi mata bayani, amma ba zai iya bari ba ga halin da ake ciki kuma a dinga shige da fice a gida. Idan cutar nan ta shigo gidan ya zai yi da ita? Ya mike ya fice ya turo mata kofar.
PAGE 41

MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ta juyo ta kalli kofar ta harareta kamar shine a wajen sannan ta ja tsaki ta juya. Ta San akwai cutar to amma ai ta yiwa Ummin magana, yanzu ya yake so tayi da aikin gidan nan ga azumi? Da ma ace zai tayata aikin me ko kuma ya bari yaranshi su dinga tayata to da sauki. Amma haka zai zuba yaranshi a gaba suna zaune suna kallon TV ita kuma tana kitchen ita kadai. Ta share kwallar da ta gangaro a idonta ta gyara kwanciya; bata san yanda zata kasance ba sai dai kawai ta bari taga yanda hali zai yi goben.

……..

Ko da gari ya waye Khadeeja bata ma San lokacin da Ummi ta zo ba don tun daga bakin gate ya tareta yace ta koma kada ta sake zuwa sai bayan Sallah.

Sai wajen Sha daya sannan ta fito ta dan gayggyara gidan, wanke-wanke ne ma ya bata mata lokaci don yana da yawa sosai. Haka ta wankesu gaba daya a famfon waje sai da shigo kifewa sannan Afaf ta tayata.

Tana gamawa ta shige dakinta ta kwanta; bata taba jin gajiya irin wannan ba a rayuwarta, gashi duk wata gaba da take jikinta ciwo take yi.

Tun 3pm ta shiga kitchen ta fara kokarin hada kayan Shan ruwa; dankali da kwai zata soya sai jollof sphagetti sannan ga peppersoup din nama. Da akwai ragowar zobo na jiya don haka ba zata sake hada wani ba.

Yaran suna zaune a parlor ta zo ta wuce ta shiga kitchen, tana wucewa Afaf ta bi bayanta. Ta so ta Koro Afaf din daga kitchen amma dai ta hakura ta barta, suna yin aikin. Basu dade da farawa ba Habib ya shigo kitchen din, ya kalli dankalin da aka ajiye a tsakiyar kitchen din yace ‘Anti wannan ferayewa za ayi?’

Tace ‘Eh, so nake na dora kifin nan sai na zauna na feraye shi.’

'Kawo wuka na feraye Anti.' Ya fada yana Bude cabinet, ya zaro roba ya tara ya debu ruwa.

Tace ‘Ka barshi Habib zan feraye.’

Ya sa hannu ya dauki wuka a kan sink yana cewa ‘Na iya feraye dankali fa Anti, idan na feraye miki sai ki yanka.’

Bai saurari amsarta ba ya tsuguna ya fara feraye dankalin.

Afaf ta ajiye kayan miyan da ta gama wankewa a kusa da Khadeejan tace ‘Anti na wanke kayan miyan.’

'To ki yanka mana albasar nan, Rabi slicing za ki yi rabi Kuma ki yanka kanana sai a saka a soup da fried egg.’
PAGE 42
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ta dauki albasar ta wanke ta zuba a chopping board ta fara yankawa.

Ba su ji lokacin da Mustapha ya karaso bakin kofar kitchen din ba; a dai-dai lokacin nan wukar da Afaf take yanka albasa ta goce ta Yanke mata hannu. Ta dire albasar ta make murya tana cewa ‘Waiyo Anti na yake.’

Da sauri ta saki abinda yake hannunta ta nufi wajen Afaf din tana murmushi cike da kulawa tana cewa ‘Sorry, garin yaya Afaf. Ki…’

Da sauri ya karasa ya kama hannun Afaf din yana cewa ‘Garin Yaya kika yanke, me ya sa kika dauki wuka?’ Ya juya ya dubi Khadijan yana cewa ‘Na gaya miki sai kin san aikin da Zaki dinga sa yaran nan Amma ke gani kike kamar kawai bana son su taya ki aiki ne. Yaushe Afaf zata iya wani yanka albasa.’

Afaf ta zare hannunta daga nashi hannun ta juya ta wanke a sink, ta dubeshi tace ‘Ya ma daina jinin Abba bari naje na daure.’

Yana juyawa ya dubi Habib wanda yake ta ferayar dankali ya daka masa tsawa ‘Ka ajiye wukar nan ka tashi, namiji da kai kana wani feraye dankali. Tashi ka bani waje.’

Ya juya kan Khadeeja wadda ta riga ta cigaba da aikinta kamar ba da ita yake magana ba, yace ‘Na gaya miki ki daina sa yaran nan aikin da ya fi karfinsu, bana so. Shi Habib ma da yake namiji me ya hadashi da wani harkar girki? Bana so.’

Bai ga alamar zata bashi amsa ba don haka ya juya shima ya fice suka barta ita kadai a kitchen din.

Ta rasa me ma zata yi, ta goge fuskarta ta cigaba da aikinta.
Chapter 10 · 0% Book details