← Book details Mijin Marigayiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 59

Sashe 11

Mijin Marigayiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka ta lallaba ta gama komai, zuwa magriba ta zubawa kowa aka sha ruwa.

Ta gaji iya gajiya don haka bata ma da kuzarin da zata iya wani musu da shi, ta dai riga ta gama yankewa kanta hukunci da zarar an bude gari zata tafi gidansu ba zata dawo ba sai ta haihu kuma ya dauki mai aiki.

…….
A haka aka cigaba da azumi, kullum cikin wannan yanayin Khadeeja take hadawa da hidimar gidan da ta yaran tayi ta fama.
Kullum sai ta yiwa Shukra da Nasreen wanka, tsarkin kashi tsarkin fitsari duk ita take musu. Duk wata fitinarsu itace me kulawa. Ga shi tana fama da Shukra wadda sai yanzu ne da suka kwana biyu ta fara hanata kashin wando.
PAGE 44
MIJIN MARIGAYIYA
A HAUSA NOVEL by Sakina Yazid (Innar su Amal)

'Don Allah kiyi mata a hankali, komai lokaci ne ai zata daina ne a yi mata hakuri.’ Ya fada yana shirin komawa dakin ya yiwo alwala.

Ta tsuguna zata dauketa taji kanta ya biyota kamar zai fado, ta dafe goshi ta koma ta tsaye tace ‘Kai! Ba zan iya ba fa.’

Ya juyo ya tsaya ‘Menene?’

‘Ba zan iya tsugunawa ba fa, jiri kwasa ta yake.’ ta karasa kan kujera ta zauna ta dafe goshi.

Ta dubi Afaf tace ‘Bani ruwa na Sha Afaf, ga kiran Sallah nan an fara.’

Nan da nan ta cika Kofi da ruwa ta mika mata, ta Sha kadan ta jingine kanta tana rike da ruwan.

Kukan Yusra ne ya katsesu tana cewa ‘Anti na daina ba zan Kuma ba, manatwa nayi daman.'

Ta yunkura zata mike Afaf tayi sauri ta dafeta. Abbansu ya dubi Khadija yace ‘Don Allah ki lallaba ki wanke mata kashin nan, Wannan wane irin abu ne? Yanzu wa kike so ya wanke mata kashin?’

Afaf ta aika Nasreen ta dauko fo a toilet ta cire wandon da yake cike da Kashi ta jefe a fo din sannan ta dauke Shukran ta nufi bandaki. Ta wanke mata sannan ta dawo ta gyara wajen, zuwa lokacin Abbansu ya fito daga alwala.

Ya zauna ya sha ruwa sannan ya mike zai tafi masallaci. A daidai lokacin itama Khadeeja ta dago kanta ‘A dawo lafiya.’

Yana jinta yayi banza da ita saboda yanda yake jin haushinta, Kuma tabbas sai ya kora mata bayani in an Sha ruwa. Daga yau ma ba zata sake yin azumin ba tunda dama Mai ciki tana da damar ajiyewa. Ta mike tana gatsina fuska, kawai sai gani yayi ta sulale zata fadi. Ya zabura zai tareta yayi fatali da casserole din dankali, a lokaci guda Habib ya saki jug din zobon da ya fito dashi daga kitchen ya tarwatse a wajen ya karasa kanta. Duka su biyun kafin su karaso ta zube.

Abbansu ya dago kanta yana jijjigawa ‘Khadeeja, Khadeeja, Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun, Khadeeja.'

Ko motsawa bata yi.

Ya sunkuceta ya kwantar da ita a kan three seater, ya kara gudun fanka sannan ya kunna AC. Ya cire mata dankwalin da yake kanta ya fara yi mata fifita.
Yaran gaba daya suka jeru a kanta suka yi tsuru-tsuru; Afaf ta leka fuskarta ta kafadar Abbansu tace ‘Abban itama mutuwa zata yi ta barmu ko?’
'Ke bana son rashin hankali, ba wanda zai mutu’
PAGE 45
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

A take yaran suka saka masa kuka mai ban tausayi. Afaf ta rungume Nasreen da Shukra suka hada Kai suna kuka.

Habib ya taba shi yace ‘Abba ka Kai ta asibiti kada ta mutu ta barmu.’

'Kai rufe mana baki.’

Gaba daya Shima ya rude, jikinsa har rawa yake yi. Ya janyo jug din ruwan sanyi ya jika hannunsa ya Shafa mata a fuska. Ta ja numfashi ta bude idonta, sai kuma ta mayar ta rufe.

'Khadeeja.' Ya kirawo sunanta da karfi yana jijjiga ta.

Da gudu su Afaf suka karasa kanta suna kira ‘Anti, Anti.’

‘Khadeeja.’ Ya kara kiran sunanta a firgice.

Ta bude ido ta sake rufewa.

Ya mike tsaye ya dan tura yaran yana cewa ‘Ku zauna na dauko mukullin mota, asibiti zan kaita yanzu, babu abinda zai sameta in sha Allahu.’

Ba tare da bata lokaci ba ya dauko mukulli ya fito, ya je ya bude kofar motar ya dawo ya dauketa bayan ya yafa mata mayafi ya wuce yaran suna biye da shi ya kwantar da ita a bayan motar. Bayan ya rufe kofar motar ya juyo ya kalli yaran yana tunani; to yanzu ya zai yi da su? Wa zai barwa su? Ya san shi kansa ma sai ya amsa tambayoyi a checkpoints gashi ma’aikatan asibitin ma kamar tsoron mutane suke balle ya kwashi yara su tafi. Ya shafa kai sannan ya sake kallonsu cike da damuwa; da ace gari a bude yake da sai ya wuce da su ya ajiyesu gidan Hajiya to amma ya san ba zai yiwu don zai yi ta bata lokaci a checkpoint. A take dabara ta fado masa.

‘Ku tsaya a nan ina zuwa.’ Ya basu umarni sannan ya fice daga gidan ya turo gate din.

Yana fitowa ya karasa gidan su Ummi, yayi sa’a yana tsayawa maigidan yana dawowa daga masallaci. Bayan sun gaisa ya sanar da shi so yake Ummi ta zo ta zauna masa da yara ya je ya kai Khadeeja asibiti. Ya janjanta masa sannan ya shige gidan ya turo masa Ummin.

Haka ya sako ta a gaba ya dawo gidan ya bar mata yaran ya ja motar ya nufi Aminu Kano Teaching Hospital dake Kano.
________

Yana zuwa asibitin aka nuna masa gynae emergency inda nan ne ake karbar masu ciki wadanda suke bukatar taimako na gaggawa, nan da nan suka karbet aka fara duba ta; duk da dai su kansu ma’aikatan zaka gane cewa suna cikin yanayi na tsoro saboda Covid19.
PAGE 46
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

A nan wajen aka nuna masa benchi ya zauna yayinda ita kuma aka turata a kan gadon marasa lafiya aka shige da ita dakin bincike.

Tana kwance a kan gadon yayinda take amsa tambayoyin ma’aikaciyar jinya sai wata ma’aikaciyar wadda taji suna kira matron ta shigo, ma’aiakciyar ta juya tana kallon matron tana cewa ‘Matron wannan fa sai an yi mata scaning, cikin nan na jikinta kamar ficewa zai yi duk da dai tace bata fara bleeding ba ama dai tana jin alamunsa.’

Matron din ta karaso ta tsaya a kanta, tace ‘Ah! Wannan ai Khadeeja ce, wa ya kawota?’

Jin an ambaci sunanta ya sa ta bude idonta a hankali, ta yi murmushi a gajiye lokacin da suka hada ido ta gane wadda ta ambaci sunan nata. Cikin sanyin murya tace ‘Anti Iyami.’

‘Na’am, Khadeeja. Wa ya kawoki?’

‘Muatapha ne.’

Ta juya ta kalli abokiyar aikin nata tace ‘’Yata ce ai, itace wadda mukayi biki kwanaki fa yarinyar Habiba wadda nace miki chiildhood friend dina ce.’

Da fara’a tace ‘Aaah! Allah sarki, to abun ya zo kenan haihuwa yakin mata.’

‘Ai kuwa. Bari na kirawo Dr. Jamil ya zo ya duban min ita sai muje na kaita scanning din muga ko za a iya sallamrta a daren nan.’

Har ta juya zata fice Khadeeja ta riko hannunta, ta juyo tana cewa ‘Akwai wani abu ne Khadeeja?’

Tayi murmushin yake ta goge kwallar da ta gangaro daga gefen idonta tace ‘Kada ki sallameni Anti Iyami, ki yiwa Mommy waya ta zo ta daukeni gida zan tafi.’

Ta dan rankwafo tana shafa kanta tana duban fuskarta tace ‘Ok, kada ki damu, ki samu ki huta tukunna likita ya duba ki. In sha Allahu yanzu zan kirawota ko bata zo ba da safe idan na tashi daga aiki sai na tafi da ke gidan Mommy din. Kada ki damu.’

Ta juya ta fice yayinda Khadijan ta mayar da idonta ta rufe.

Tare da likitan suka dawo, bayan ya duba Khaddej aka je aka yiwo scanning tare da Mustaphan aka dawo. Bayan likita ya duba scanning din yace cikin jikinta ya lalace fita zai yi, don haka za ayi mata wankin ciki sannan akwai allurai da ruwa da za a saka mata.

Da kansa yaje ya siyo komai ya kawo sannan suka koma wajen Khadeeja tare da matron; a nan Khadeejan take sanar da shi cewa martron kawar Mommy ce.
PAGE 47
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ya sake gaisheta cike da girmamawa, bayan ta amsa ta dubi Khadeejan tace ‘Likita ya ce cikin jikinki ya lalace don haka za a yi miki wankin ciki, ga magunguna kuma ya rubuta miki sannan ga drip idan an gama wankin cikin zan saka miki kinga yau a nan zamu kwana da ni da ke.’

Tayi murmushin yake, ta dubi Mustapha tace ‘Ka tafi, ka bar yara a gida. Anti Iyami zata kirawoka idan akwai wani abu tunda ka ga tare zamu kwana ma, zuwa da safe zamu yi waya in sha Allah.

Matron ta fice ta basu waje. Bayan ta fice ya matsa kan Khadeejan yana saha fuskarta yace ‘Sannu, kin bani tsoro fa.’

Tayi murmushi.

Ya cigaba ‘Kafin safiyar tayi sai ki samu ki yi mi message din duk abinda kike so na taho miki da shi, idan kuma Allah ya sa da safen zasu sallameki ma shike nan sai kawai na zo mu tafi. Na yi maganar abici ma Anti Iyami tace na bari zata kawo miki, but in ana son wani abu kiyi min magana sai na saka miki kudi a account dinki ko transfer ne sai kiyi musu.’
Ya sa hannu a aljihunsa ya zaro wayarta ya mika mata yana cewa ‘Ga wayarki, ba zan kirawoki ba don kada na dameki ko na tashe daga bacci, but please da kin farka ki kirawo ni.’

Ta karba tana murmushi tana cewa ‘Ok, ka gaishe min da su Yaya Afaf.’

Ya fice ya barta a kwance.

Yana fitowa ya sami Anti Iyami da abokan aikinta a station dinsu, yayi mata sallama bayan ta karbi lambar wayarsa sannan ya wuce.
Chapter 11 · 0% Book details