← Book details Mijin Marigayiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 59

Sashe 53

Mijin Marigayiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A nutse tace ‘Eh haka ne, amma ka ga bai karasa shekaru hudu ba ma. Ina ganin nan da zuwa ya gama primary in sha Allahu sai ya dawo cikin ‘yan uwansa tunda tabbasa ni na san kula da yaro akwai wahala, musamman da yake ka ga Antinsu ba zama take ba tana aikinta. Ina ganin ka bar min shi duk wani abu da yake bukata in sha Allahu zan sanar maka, idan ya iya kula da kansa sai ya dawo gida.’

So yake ya ce mata hakan ba zai yiwu ba ko don ma ya bata mata rai, amma ya kasa. Tabbas yana son ganin yaronsa a kusa da shi cikin ‘yanuwansa amma kuma idan ya karbeshi baya jin Naja zata iya hadawa da shi ta rike, don yanzun ma kullum cikin korafi take a kan yara suna gajiyar da ita. Gara ma ya bari ta rike shi in Allah yayi da ragowar zaman sa koma tare. ‘Um hakane, to babu damuwa. Sai goben kenan.’

‘Ok, Allah ya kai mu goben.’

……....
Bata taba tsammanin Mustapha zai bar mata Hammad da sauki ba, don haka ma da yayi saurin amincewa da maganarta sai ta ji wani dadi marar misaltuwa; domin ta hango wahalar da zai sha idan ya koma gidan; zama zai yi kamar maraya. Tunda su Shukra su hudu ne, Rukayya kuma uwarta tana gidan sai shi kadai wanda ba shi da uwa bashi da dan uwa a gidan.

A hankali ta mayar da wayar tata ta ajiye a kan teburinta. Ta sunkuyar da kanta ta share kwallar da ta taru a kwarmin idonta sannan ta zuba fuskarta a tafukan hannunta; ta tuno lokacin da suna soyayya da Mustapha kafin suyi aure. Wai ina soyayyar nan ta tafi ne? ya barta ita kadai tana ta dakon soyayyarsa har tsawon shekaru takwas?
PAGE 221
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Tabbas ta sha wahala a gidan Mustapha; ba wai wahalar jiki ba don wahalar jiki ta san abinda ta yi bai wuce abinda matar aure zata yi ba. Sai dai wahalar zuciya da ta sha; kulawa da tausaya tare da kauna da zuciyarta take bukata daga wajen Mustapha sune bata samu ba. Ko su din ma ta hakura da su tana zama haka tunda ko babu komai tana kallonsa a matsayin mijinta kuma suna kwana tare. Amma daga lokacin da ya auro wata kuma ya ke bata kulawa da kauna wanda ita ya kasa bata daga lokacin ta yanke kauna daga zaman gidan Mustapha.

Ba zata ce bata jin zafin rabuwa da shi ba domin tabbas ta san ko babu kauna akwai sabo, amma tabbas ba zata sake komawa gidan Mustapha ba. Domin tayi sujjada ta roki Allah kada ya sake hadata zaman aure da Mustapha. Da farko ta fara jin haushnsa amma daga baya sai taga jin haushin babu wani amfani; ko babu komai dole ta yiwa Hammad kara ta girmama mahaifinsa.

Ta sake share kwallar da ta taru a kwarmin idonta, ta kalli ruwan hawayen da ta lakata a hannun nata; to kukan me take a halin yanzu? Ta zata ta gama kuka a kan Mustapha. Tayi murmushi ta sake goge kwallarta; ta san ba zata iya goge Mustapha daga cikin tarihin rayuwarta ba amma tabbas bata fatan sake rayuwa irin wadda tayi a gidansa. Ta goge fuskarta ta fice ta nufi cikin studio inda zata gabatar da labarai.

......
Ba a fi sati daya da kwashe kayan Khadeeja ba Naja ta saka Mustapha a gaba sai da ya sake fentin saman aka gyara ta kwashe kayanta ta koma. Yaran kuma gaba daya ta tattarosu ta dawo da su kasa tare da masu aikinta guda biyu. Dakinta da parlor dinta nan ta mayar dakinsu Afaf, suna ji suna gani babu yanda suka iya. Shi kanshi Mustapha abun bai yi masa dadi ba amma ya kasa magana; yana matukar mamakin abinda ya sa baya iya hana Naja abinda take so a ‘ya kwanakin nan.

Cikinta yana cika wata tara ta sake haifar ‘yarta mace, haka ta dage ta shirya taron suna fiye ma da wanda ta shirya a haihuwar Rukayya. Aka sakawa yarinyar suna Maryam.
PAGE 222
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Washegarin suna su Anti Wiyya da sauran dangi suka soye naman suna suka gyara koma, sannan suka tafi suka bar Anti Wiyya ita kadai wadda zata kara kwana biyu saboda tayata jego.

Tana zaune a parlor din sama Anti Wiyya ta shigo da sallama, bayan ta amsa ta karasa ta zauna a kusa da ita sannan tace ‘Wannan mai wankin naki gaskiya ya iya wulakanci, sai da ya fuskanci ana taro sannan ya gudu. Ni dai wallahi ko kayan sakawa gobe bani da su duk sun yi datti, ga shi duk jikina ciwo yake balle na zage na wanke kuma ‘yar aikinki ma dai ta fini gajiya.’

‘Ai mai wankin nan yayi wa kansa, in sha Allahu gobe Abban Rukayya zai samo mana wani mai wankin kowa ya huta.’ Ta fada tana gyara zama.

Anti Wiyya tace ‘Don ma dai ‘yayanki basa moruwa ne in banda haka ga Habib can a kasa yana wanki ai da ko kala daya ne ya wanke min.’

Ta gyara zama ‘Au ai ban san ma yana gidan ba kwaso kayan duka bari na kirawoshi zai wanke miki yanzu.’

Ba tare da bata lokaci ba ta juya ta koma kasa inda ta kwaso kayan nata yayinda ita kuma Naja ta kwalawa Afaf kira ta sakata ta turo Habib.

Kusan a lokaci guda suka isa parlor din, shi ya tsaya daga bkin kofa yayinda ita kuma ta karasa ta zube kayan a gaban Naja.

Yana daga tsaye a bakin kofa yace ‘Anti gani.’

Tace ‘Mai wanki ya kwana biyu baya zuwa, ka kwashi kayan nan ka wankewa Anti.’

Ya kalli kayan ya kalleta yanda take muzurai; ba wai bata saba yi masa hakan bane, ta riga ta saba musamman tun bayan da khadeeja ta bar gidan. Kawai dai ya kan yi mata binda zai iya wanda ba zai yi ba kuma ya bar mata kayanta. Ya sake kallon kayan yace ‘Ah ku barshi dai yanzu zan fita sai na samo muku wanda zai wanke ku biya shi.’

Har ya juya ya fara tafiya tace ‘Kana nufin ba zaka wanke ba ko me.’

Ya dan dawo ya kalleta ya kalli kayan, har ya bude baki zai yi magana kuma sai ya fasa, ya fice ya barta nan a zaune da kayan.

A fusace ta mike tana huci, kafin tayi magana Anti Wiyya tace ‘Ai na gaya miki wadannan yaran basa moruwa.’
PAGE 223
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

‘Ni ka tafi ka bari ina magana ko Habib? Saboda ka ga ni ba uwarka bace kuma ba khadeeja bace ko? Saboda ba a isa a saka aiki kayi ba ko? To wallahi bari Abban naku ya dawo, sai dai ko ni ko kai a gidan nan don idan dai ba zan moreka ba sai dai ka bar gidan wallahi.’

Wiyya tace ‘Ah to, yaron da bana jin ya haura sha takwas ya dinga yi miki irin wannan rainin, wannan nan da ‘yan shekaru ai sai ya kai miki duka.’

‘Wallahi bari ubanshi ya dawo, dole ya bar min gidan nan idan ba haka ba ni na bar masa gidan. Idan ma Khadeejan ce take zuga shi ta janyo masa.’

Haka Wiyya ta skaata a gaba ta kara zugeta kafin ya dawo.
PAGE 224
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ana idar da sallar Magriba ya shiga gidan, Habib ne ya bude masa gate tare da Baba maigadi yayi masa sannu da zuwa sai dai bai rakashi har cikin gidan ba. Kamar yanda ya saba a parlor din kasa ya sami yaran suna zaune suna kallon TV, bayan ya amsa sannu da zuwansu ya wuce sama. Da da ne Nasreen da Shukra sai sun rakashi har dakinsa, sai dai yanzu saboda yanda Naja take yawan korarsu tana nuna musu su dinga tsayawa a kasa ya sa sun hakura, haka ya haye shi kadai zuciyarsa babu dadi; saboda shima yana kewar wannan rakiyar.

A dakinsa ya sameta tana ta cika tana batsewa, domin ko sannu da zuwa haka tayi masa tana ta faman zumbura baki. Bayan ya amsa yace ‘Me ya faru ne naga kina ta wani bata rai?’

Ta sake hade rai sannan tace ‘Ya za ayi a gidan nan ace ban isa na saka Habib aiki yayi ba? A gaba kowa zan ce Habib yayi aiki amma kai tsaye ya ce min ba zai yi ba? Ai ba haka yake yiwa Maman Hammad ba, ko da yake na ji suna cewa yana zuwa wajenta ban sani ba ko itace take zugashi ya dinga yi min rashin kunya.’

Ya ajiye jakarsa ya zauna a kan kujerar gaba mudubi ya fara cire takalmansa yana cewa ‘Kada ki saka Khadeeja a cikin wannan maganar, da zata sa wani yayi miki rashin kunya da tun tana nan zata saka su. Habib din me kika ce yayi ya ki yi?’

‘Wankin kayansa yake yi shine na kirawoshi na bashi kayan Anti Wiyya kala daya nace ya taimaka ya wanke mata amma yaron nan ya ki, kuma yana kallo mai wankin namu ya gudu. Itace ta ke ta fama kula da gidan kayanta duk sun yi datti amma a gabanta Habib ya ce ba zai wanke mata kala daya ba don wulakanci don ya nuna mata ban isa ba.’

Ya mike ya cire kayansa yana cewa ‘Ki dauko kayan idan na fito zan bashi ya wanke in ya so zan gayawa Baba Maigadi ya zagaya nan makarantar almajirai ya samo yaro a wajen malaminsu wanda zai dinga zuwa yana wankin.’
PAGE 225
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Chapter 53 · 0% Book details