← Book details Mijin Marigayiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 59

Sashe 8

Mijin Marigayiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya juya kan Khadeejan wadda take cigaba da wanke-wankenta yace ‘Wai me kika mayar da yaran nan ne? Habib ne zai iya share wannan tsakar gidan ga kura ga komai. Itama Afaf din wannan uban ruwan ai sai tayi mura. Ke kika ce a bar mai aikinki ta tafi gida, da kin bari ai da yanzu tana nan; sannan kuma ki dinga basu aikin da ya fi karfinsu? Bana son irin wannan; bana son ki dinga yiwa yaran nan kallon wasu manya, ki dauke su kamar ke kika haifsu shine zaki iya yi musu adalci. Idan an ji wani almajirin yana bara sai a kirawoshi ya karasa wannan aikin ko kuma tunda kun kusan gamawa ki karasa zuwa gobe a sami wani almajirin.’

Ko kallonsa bata yi ba ta cigaba da wanke-wankenta, ya ja tsaki ya juya ya nufi cikin gidan. Ta share hawayenta ta cigaba da wanke-wankenta.

Ba zata iya dogon surutu ba sannan kuma bata son tana biye masa suna fada a gaban yara, ita yanzu duk wani abu da zai sa ayi magana ma bata so; shi yasa ta gwammace tayi masa shiru.
PAGE 31
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Sai da ta gama wanke-wanken nan tsaf sannan ta kwashe sharar, ta debi kwanukan ta shigar cikin gida.

Suna zaune a parlor suna kallon TV.
Tana kitchen din tana kife kwanukan Afaf ta shigo ta sameta, ta dauki kwanukan ta fara kifewa. Ta dubeta tace ‘Afaf je ki zauna ai na kusa gamawa.’
Tace ‘Bari na tayaki Anti, ai nan babu ruwa.’
Ba don ta so ba ta kyaleta sai da suka kife kwanukan gaba daya ta mayar da komai inda yake sannan ta wuce daki su kuma suka cigaba da kallonsu.
Can wajen 1pm bayan sun yi sallar azahar ta fito daga daki ta shiga kitchen; tuwon alkama da miyar danyen kubewa ta dafa jiya da daddare amma duk sai suka ki ci. Da yake akwai biscuits da cake sai kowa ya ci ya sha lemo, ita da abbansu ne kawai suka ci tuwon gashi ta dafa shi da yawa. Da safe kuma da kwadayi ta tashi don haka wainar fulawa ta soya kowa yaci. Wannan ragowar tuwon shi ta dauko daga fridge ta dumama shi, ta dumama miyar wadda ta sha kaza da nama. Ta zubawa kowa abincinsa sannan ta kirawosu kowa ya dauki nasa suka zauna a table.
Kallon tuwon kawai Habib yakeyi yana juyashi amma yaki ya fara ci, tana kallonsa tayi banza da shi ta cigaba da kai lomarta tana bawa Shukra don ita tuwon yayi mata dadi. Jimawa kadan ya dubeta yace ‘Anti tuwon jiya ne fa?’
'Eh, shine, ko ci ko bari.’ ta fada a gajarce ta ci gaba da cin abincinta.
Daidai nan Abbansu ya fito ya zauna a table din, ta tura masa flask da plate. Ya bude flask din ya kalli fuskokin yaran sannan ya kalleta yace ‘Wannan ai tuwon jiyane, ba a yi abincin ranar bane?’
‘Shine abincin ranar ai, dumamawa aka yi tunda babu abinda yayi.’
Nasreen wadda itama take ta juya nata tuwon tace ‘Abba wallahi tuwon ba dadi, ni bana son bakin tuwo gaskiya.’
Shi din yana son tuwon alkama don shine ma ya sa aka yi tuwon da daddare, don haka ya zuba malmala guda ya fara ci. Ya sake duban fuskokin yaran, bayan ya hadiye lomar da take bakinsa yace ‘Yanzu ba wani abu da za a iya dafawa yaran nan, Afaf ce kawai take cin tuwon nan.’
Ba tare da ta kalleshi ba tace ‘Babu.’
Ta cigaba da cin tuwonta kamar bata san da su ba a wajen.
Jimawa kadan Nasreen tace ‘Abba ni a hada min cornflakes.
PAGE 32

MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ya dubi Khadeeja yace ‘Akwai cornflakes ko?’

Cikin halin ki in kika tace ‘Akwai.’

'Da Allah a hada mata ta samu ta ci kafin ayi abincin dare.’

Tace ‘To.’

Ta ci gaba da cin tuwonta tana bawa Shukra a baki, yayinda ita kuma Nasreen ta tashi ta koma gaban TV. Jimawa kadan Habib ma ya mike, ya dauki kwanonsa da na Nasreen yana cewa ‘Abba nima na sha cornflakes din kawai.’

Ya wuce ya kai kwanukan kitchen ya dawo shima ya zauna a gaban TV.

Bai dade da tashi ba kuma itama Khadeejan ta gama cin nata tuwon, ta dauke kwanonta ta kai kitchen. Ta fito daga kitchen din ta wuce daki ba tare da ta kallesu ba. Tana shiga ta saka pillow ta kwanta a tsakiyar gadonta, da yake ta gaji sannan kuma ta koshi tana rufe ido bacci ya kwasheta.

Bata sani ba ko ta dade da kwanciya ko bata dade ba, kamar a mafarki taji Mustapha yana dan buga kafarta yana cewa ‘Khadeeja, Khadeeja, barci ma kike yi? Kin bar yara da yunwa fa ki zo ki hada musu cornflakes ko ki dafa musu indomie.’

Ta dan janye kafarta tana kokarin tashi; kafin aurensu fa baya kiran sunanta sai dai yace ‘yan mata, mekyau ko kuma yace babe. Tayi zaton idan sun yi aure next level zasu shiga a kara mata matsayi amma zata iya cewa tunda ta shigo gidan nan sau daya ya kirawota da babe a daren da suka tare. Yanzu kam yaci duba sai ceto don gatsal yake kiranta Khadeeja.

Ta gyara zama tace ‘Me kake cewa?’

'Baki bawa yara abinci ba kin zo kin kama bacci.’

Tana jijjiga kai tace ‘Kowa fa na bashi abinci baka gani bane?’

'Habib da Nasreen nake magana fa.’

'Oh, ba sun ce cornflakes zasu sha ba, ai akwai a kitchen din.’ ta fada tana kokarin kwanciya.

'To ai sai ki zo ki hada musu ko?’

Ta gyara kwanciyarta a cewa ‘Wallahi babe na gaji, idan ban yi baccin nan ba ko abincin dare ba lallai na iya dafawa ba. Suje su hada cornflakes din mana ko su ci tuwon da kowa ya ci.’

'Ya ina miki magana kina kwanciya Khadeeja, haka zaki bar min yara da yunwa.’ ya fada a fusace.

Ta gyara kwanciyarta tayi banza da shi.

'Ina miki magana kina ji na fa Khadeeja bana son wulakanci.’

Ta tashi zaune, lokacin ya riga ya mike tsaye. Ta gyara zama tace ‘To me zan ce maka?’
PAGE 33

MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

'Ba zaki zo ki hada musu cornflakes din ba kenan?’

'Hada cornflakes din ba wani aiki bane shi yasa nace su hada kawai, wallahi kaina ciwo yake.’ Ta ture abinda ta rufa da shi ta sauko daga kan gadon ta wuce bandaki saboda yanda bakinta ya cika da yawu, ta mako kofar bandakin ta tsaya a gaban sink; wallahi babu wani abinci da zata hada sai dai yayi duk abinda zai yi.

Tana ji Nasreen ta leko tace ‘Abba yunwa nake ji.’

Ya ja tsaki ya kama hannun Nasreen suka fice daga dakin bayan ya maka mata kofar a fusace.

Haka ya je ya hadawa yaran cornflakes din suka zauna suka ci.

………..

Tun da ya hada musu cornflakes din nan kuma sai ya shiga share Khadeeja, gaba daya ya ki kulata ko zama inda take. Ta kula da hakan don haka ita ma sai ta ja jikinta, domin bata cikin yanayin ma da zata iya saurarensa.

Ko da dare yayi ma har ta kwanta a dakinta sai kuma taga rashin dacewar hakan, tunda dai bai koreta ba kuma ita ba fushi takeyi da shi ba shi kadai yake fushinsa. Don haka bayan ta kwantar da yara sai ta shirya ta wuce dakinsa ta kwanta.

Can wajen sha biyun dare motsin shigowarsa ya tasheta, yana tsaye a gaban wardrobe yana saka kayan bacci. Ta sauko daga kan gadon ta wuce bandaki don tayi fitsari ta kuskure baki. Tana fitowa ta wuce ta kwanta, ta kalleshi yana zaune a gefen gadon yana dannan waya; so take ta ce masa “good night Babe” kamar yanda ta saba amma bakinta ya ki furtawa saboda yanda take cike da haushinsa. Don haka sai kawai ta juya masa baya ta kwanta.

Kamar wanda yake jira ta kwanta sai ya gyara zama a kan gadon yace ‘Tashi muyi magana Khadeeja.’

Ta juyo ta kalleshi sannan ta tashi zaune ta jingine da jikin gadon; tana bakin cikin yanda yake kiranta Khadeeja gatsal sai kace shi ya yanka mata ragon suna.

Bayan ta zauna ya kara tsuke fuska sannan yace ‘Bana son yanda kike yi min taurin kai da neman kawo min raini a gaban yara, idan ma wani abu ne a ranki gara ki fito ki gaya min.’
PAGE 34

MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Tayi murmushin yake tace ‘To, sai dai ban san lokacin da nayi maka taurin kan ba.’

'Dazu nace ki hadawa Habib da Nasreen cornflakes kin ki, nan kika shige bandaki kika barni a tsaye ina miki magana.’

Ta kalleshi suka hada ido ta kura masa ido har sai da shi ya kawar da kansa, ta bude bakinta wanda ya fara tara yawu tace ‘To in sha Allah zan kiyaye, amma nima don Allah ka dinga saukaka min rayuwa a gidan nan. Idan baka yi min saboda kauna ba to kayi min saboda yanayin da nake ciki tunda nima ba lafiya ce ta isheni ba duk abinda ka ga ina yi daurewa nake yi.’

Ya dan fara saukowa yace ‘Duk don na nema miki saukin ne ai nace a kawo mai aiki, kuma da ta dawo zata cigaba da tayaki. Itama mahaifiyarsu haka take kula da su ko da kuwa tana da ciki don wannan ba wani abu bane a wajen macen da ta san me take yi. Bana son ki dinga yi musu abubuwan da zasu ji maraicin uwarsu, ki rike su kamar ke kika haifesu. Shine abinda zai samar da zaman lafiya tsakanin mu.’

Ta gyada kai tana kallonsa cike da tsananin mamaki tace ‘To.’

Ta sauka daga kan gadon ta shiga bandaki ta tofar da yawun bakinta ta daurayo bakinta ta fito ta kwanta bayan ta kashe fitila.
Chapter 8 · 0% Book details