Sashe 3
Mijin Marigayiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
'Tace wai a bari ta huta zuwa next week, don ni da yau ma na so a daukosu. Yanzu ma idan na fita zan je na kai musu biscuits din da na saya musu.’
Yaya Jidda tace ‘Wai wacece tace a bari ta huta? Khadijan?’
Yace ‘Eh, tace wai a bari ta huta ta gama ware kayanta kafin a kawo su.’
'Kai Musty! Yanzu kai har ka bata dama su da gidan ubansu sai ta ga dama za a kawosu, to me tayi ya gajiyar da ita har take bukatar hutu.'
'To nima dai haka na gani, amma dai zan ga yanda zamu yi.’ Ya fada yana kauda kai.
Hajiya tace ‘To ka dai dinga kula sosai don kada ta dinga cutar da su, ka sa ido sosai don yanzu mata ba tausayi ne da su ba.’
Yaya Jidda tace ‘Musamman gashi tun yanzu ta fara iyayi da kafa dokoki, a jira ta huta kafin a kawosu gidan ubansu.’
Haka suka gama hirarrakinsu suna jaddada masa ya sa ido sosai kada Khadija ta cutar da yaransa; yayi musu sallama ya wuce gidan iyayen Ma’u wajen yara. Sai da ya tsaya a hanya ya saya musu yoghurt da gasasshiyar kaza sannan ya wuce.
Yana shiga bayan sun gaisa da Mama ta turo masa yaran suka sameshi a guest room. Suka karbi kajin da yoghurt suka kaiwa Mama; wadda ta riga ta saba idan ya kawowa yaran abu to ba zai bata ba sai dai ya bawa yaran a hannunsu su su kai mata; sannan suka dawo wajensa suna ta murna don su sun shirya kayansu tsaf yau zasu tafi wajen Anti Khadija.
Hakan yayi masa dadi don dama hakan yaso. Nan da nan suka sheka cikin gida suka fara fitowa da kayansu, Anti Nihla kanwar Ma'u ta taya su duk suka fito da akwatunansu. Mama ta fito ta sameshi, bayan ta zauna tace ‘Ga mutanena nan tunda suka ji uwarsu ta tare sun kasa zaune sun kasa tsaye fa, ni da mukayi da su sai an kwana biyu amma ka ga suna ganinka sun fara fito da kaya. Kayan nasu ma fa wasu suna wajen wanki.’
'Wallahi kuwa, ai babu komai daga baya sai na zo na karbar musu sauran, kuma ma ai zasu dinga zuwa in Sha Allah.' Ya bata amsa.
Haka aka gama fitar da kayan aka zuba masa a mota ya kwashe su suka kama hanya, suna ta murna zasu je wajen Anti Khadija.
…….
Tunda ta gama tuwo tayi Sallah sai ta yi wanka ta shirya cikin bum short dinta da wata figalalliyar riga, ta sha turare sai kamshi takeyi ga gidan ma tayi fes da ko ina ta kunna turaren wuta kamshi sai tashi yake a hankali.
Tana kwance a kan three-seater tana danna waya ta jiyo motarsa ya bude gate yana shigowa, ta tashi zaune ta dan gyaggyara tana jiran ya shigo ta taro shi daga bakin kofa.
Mintuna kadan ta fara jiyo motsinsu a kofar shigowa parlor, ya zura mukullin yana kokarin budewa yana cewa ‘Afaf rike hannun Shukra na bude kofar.’
Ta dan yamutsa fuska tana kokarin ta gane shi da su waye; tas ta jiyo muryarsu gaba daya. Ta dan rikice kadan tana mamakin dalilin da yasa ya taho da su bayan ya amince sai next week.
Ta jiyoshi yana zare mukullin daga jikin kofar; ta kalli jikinta yanda take kusan tsirara. Ta yi wuf ta zaga bayan kujera daidai lokacin da yake sako kai cikin parlor din, ta dauki jilbab dinta wanda yake ajiye a saman kujera ta saka.
Tana karasa saka jilbab din suka shigo da gudu bayan ya shigo, suka hada baki gaba daya ‘Anti Khadija, Anti Khadija.' Suka karasa da gudu suka rungumeta suna murna.
Haka ta yashe baki tana amsa gaisuwarsu, ta dauki Shukra tana cewa ‘Shukra baby, ya Mama? Kin barota tana kuka ko?’
Cikin muryarta ta gwaranci tace ‘Ba kuka take ba, ta ce ma na gaisheki.’
'Ina amsawa.’
Ta ajiyeta ta kama hannun Habib tace ‘Ya Habib, welcome.’
Ta kalli Mustapha suka hada ido, yayi sauri yace ‘Sun ki barina na taho sai da suka biyo ni, ga kayansu nan sai ku shigar.’
'Uhm, bari mu gani.’ Ta amsa murya kasa-kasa.
Ta dauki babban akwatin nasu ta ja ta nufi dakin yaran tana cewa ‘Afaf dauko wannan jakar mu iai daki.’
Afaf ta kama jakar tana kokarin dagawa Abbansu yace ‘Ke ajiye jakar nan ba zaki iya dauka ba.’
Suna tsaye a dakin a gaban wardrobe tana tambayar Afaf ina jakar Abbansu ya shiga dakin dauke da jakar, yace ‘Ga ta nan, gani nayi ba zata iya daukowa ba na dauko mata.’
Ta yi ‘yar dariya tace ‘Haba dai, Yaya Afaf ai ba raguwa bace, jakar ma da babu nauyi.’
Sukayi dariya gaba daya, ya ja yaran suka fice daga dakin suka barta ita kadai tana kokarin samarwa akwatin kayansu waje. Bayan ta ajiye akwatin a kusa da mudubi ta dan ja baya ta kare wa dakin kallo; komai tsaf yake tunda an share lokacin da ana kafi sai dai ba a shimfida zanin gado ba a kan babban gadon nasu. Bata san a ya suke kwana ba kafin a aurota amma dai tana jin a kan gadon suke kwana duka. Ta fito ta samesu a parlor sun baje suna kallo suna ta yiwa Abbanau surutu.
Ta dubesu tace ‘Bari na ciro hijabin nan Afaf sai ki tayani mu gyara dakin.’
Abbansu yace ‘Wannan ce za tayi wani gyaran daki? Babu abinda ta iya fa.’
Tayi ‘yar dariya tace ‘Bari ka gani.’
Ta shige dakinta; tana shiga ta cire hijabin ta jefa kan gado, ta karasa gaban wardrobe ta bude tana duban babban rigar da zata saka.
Wani malolo ya tokare mata makogoro saboda takaici; to ta ina zata soma? Haka kawai ya kwaso mata yara a wannan daren. Da ya gaya mata ma ai da tuni ta gyara dakin. Ta ja gajeren tsaki a Fili.
Motsin shigowarsa ne ya katse mata tunanin, ya nufota yana cewa ‘Na zata a nan dakinki zasu kwana ai.’
Ta dan goge idonta ta juyo tana cewa ‘No, gara kawai na gyara musu dakinsu tunda babu wata kura da yawa a dakin sai su kwanta a can.’
Ya dan tabe baki ‘Ok, ammma dai za ki dinga zuwa kina dubasu ko?’
'Eh mana wannan ai dolene.’ Ta amsa tana dan juya jikinta.
Ya juya ya fita ba tare da ya ko kalli jikin nata ba. Ta kalle jikinta ta dan murgude baki; yau dai kwalliyarta ta tashi a aikin banza kenan.
Ta janyo babbar riga a wardrobe din ta saka, ta sa hula ta rufe gashinta sannan ta fito. Kai tsaye ta wuce kitchen ta dauki tsintsiya da parker, ta fito parlor din ta dubesu tace ‘Taso Afaf, maza mu gyara dakinku ku sami wajen kwanciya.’
Ta wuce ta barsu, a tunaninta yarinyar zata biyo bayanta. Sai dai har ta shiga dakin ta fara kokarin sharewa babu motsin tahowarta, ta dan dakata da sharar da takeyi ta kwala mata kira. A maimakon yarinyar ta amsa sai Abbansu yace ‘Abinci muke ci.’
Ba tare da ta amsa ba ta sunkuya ta cigaba da sharar, har ta dan yi nisa a sharar sai kuma ta tuna cewa yayi abinci suke ci fa; to wanne abincin? Tuwon da ta tuka da shinkafa gwangwani 1 da Rabi din ya tasa yaransa a gaba suke cinyewa? Bayan ta gaya masa zata jirashi ya dawo su ci abincin dare tare? Tuwon ma da gaba dayansa malmala uku ne ta tuka saboda ta san miyar ba zata isa su ci dumame ba.
Har ta ajiye sharar ta nufo parlor din sai kuma ta tuna idan ta zo me zata yi a kai, don haka sai kawai ta cigaba da sharar ta tana fatan Allah ya sa su rage mata tuwon.
Ta share dakin ta karkade ko ina sannan ta shimfida zanen gadon da ta dauko daga dakinta. Ta kalli dakin taga ko ina yayi tsaf, sannan ta dauko sharar da ta kwashe ta fito.
Suna zaune a kan dining table suna ta cin tuwo shi da ‘yayansa, kafin tayi magana Abbansu ya dubeta yace ‘Yauwa dan karo mana tuwon nan Habib bai koshi ba, ga Shukra ma kamar zata kara.’
Ta dan zaro ido tace ‘Wai kun ciye na flask din?’
'To nawa yake, ai bashi da yawa.’
Kafin ta bada amsa Nasreen tace ‘Kuma miyar tayi dadi Anti.'
Ta yi murmushin yake tace ‘Shikenan dama na dafa, ko nima ban ci ba.’
Habib yace ‘Abba nifa ban koshi ba, dama bamu ci abincin dare ba lokacin da muka taho gashi mun manta bamu karbo kazar mu ba a wajen Mama.’
Abbansu ya dubeta yace ‘Yanzu ya zakiyi da Habib? Yunwa yake ji.’
‘Akwai ragowar bread sai mu raba ni da shi mu sha da tea, don gaskiya yanzu ba zan so dora tukunya ba.’ ba tare da ta saurari amsarsu ba ta wuce kitchen da sharar a hannunta.
So take ta sami waje tayi kuka ko taji sanyi a ranta, don haka ba tare da ta kalli wajen ba ta jefa sharar ta juya sink ta fara wanke hannunta. Abbansu ta jiyo a bayanta yace ‘Khadeeja, daurewa fa zakiyi ki dafawa Habib Indomie don shi baya cin bread kuma kinga ai ba ya kwana da yunwa ba.’
Ta kalleshi suka hada ido tace ‘Babe na gaji ne wallahi, nima ina son tuwon amma na hakura zan ci bread.’
Ta dan saurara tana kallon yanda yake kara hade rai, sai kuma cinkin sanyin murya tace ‘Amma Afaf ta zo na kunna mata cooker ta dafa musu Indomie din.’
Ya kalleta shekeke yace ‘Wai ke me kika dauki Afaf ne she's only eleven babu abinda ta iya na aikin gida. Idan ta girma dai ta koya but ki daure kawai ki dafa masa.’
Ta juya ta bashi baya saboda hawaye ne yake Shirin kwace mata, ya juya ya fice ya bar mata kitchen din.