← Book details Mijin Marigayiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 59

Sashe 5

Mijin Marigayiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yace ‘Shi na fara cinyewa Abba.'

Nasreen tace ‘Abba ni ina son dankali, Anti tace ba za a dinga soya dankali ba sai weekend.’ Ta langabe kai kamar abun tausayi.

Ba tare da ya kalli Khadeejan ba yace ‘No, za a dinga soyawa kada ki damu, maza ki ci abinci mu tafi.’

Tana jinsu ta kawar da kanta, don sai dai idan shi zai dinga tashi ya soya ita bazata iya soya dankali da sassafe ba. Nan da nan suka gama; Habib ne ya fara mikewa har ya juya tace ‘Dauke plate dinka da cup din ka kai kitchen.’

Ya dauke plate din ya tafi da shi, suma ‘yan uwan da suka ga haka kowa idan ta mike sai ta dauke plate dinta ta wuce da shi.
Suma ‘yan uwan da suka ga haka kowa idan ta mike sai ta dauke plate dinta ta wuce da shi. Suka karasa shiryawa suka fice tare da Abbansu.

Kafin ya dawo ta soya dankali da kwai ta jera a dining table sannan ta wuce daki; wanka zata shiga sai kuma ta tuna ko da ta yi wankan dai kitchen zata shiga tayi wanke-wanke ga shara, don haka taga gara ta bari idan ta gama aikin ta yi wankan.

Sai da yayi wanka ya shirya sannan ya fito a shirye, kai tsaye ta riga ta shirya abincin a dining table don haka suka zauna. Yana bude kwanon yace ‘Sai da suka tafi kuma kika soya dankali? Sun fi son soyayyen abinci idan zasu tafi school.’

Ta dan langabe kai ‘To ai Babe ba zan iya soya wani abu before 7am ba, da ace ma dai ina da mai aiki ne. Amma hakan ma weekend zan soya musu in sha Allah.’

‘To ai da kin bari sai weekend din ma ci gaba daya, yanzu idan sun dawo ai zasu ga bawon ba dadi ai kuma ma Shukra zata gaya musu tunda ita taci. Mai aikin ma kuma za a dauka.’

'Uhm.'

Suka cigaba da cin abincin ba tare da kowa ya ce komai ba.

Gaba daya ma abincin sai ya fice daga ranta; kenan duk abinda ba zata bawa yaransa ba baya so ita ta ci. Haka tunani kala-kala suka yi ta yawo a kanta.

Ya gama cin abincin ya fice ya barsu ita da Shukra.

Sai wajen 10am ya kirawota a waya, bayan ta dauka yace ‘Mantawa nayi ban gaya miki ba idan 1pm tayi sai ki je ki dauko yara daga school.’

Ta dan yi shiru don ta zata shi zai daukosu, tace ‘Ohk, but zan iya zuwa a kasa?’

'No, kin san school din ai ba nisa sosai amma dai ku hau a dai-daita sahu sai ki tafi da Shukra.’

'Ok.'

Suna gama wayar ta mike ta dora abincin rana don ta gama da wuri. Lokaci yana yi ta dauki Shukra suka tafi suka dauko yan makarantar. Suna dawowa bayan sun huta ta shiryasu suka tafi islamiyya.

Dab da magriba ya dawo. Bayan ya huta yana zaune a parlor shi da yaran tana jiyoshi yana tambayar Afaf abinda aka yi da baya nan, an dauko su da wuri daga school? Sun ci abincin rana? Me suka ci? Sun makara a islamiyya? Haka dai ya cigaba da tambayoyinsa tana kitchen tana jiyosu, kamar ta fito tayi magana sai kuma ta share ta cigaba da abinda takeyi.
PAGE 20
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

A haka suka karasa satin nan tana bakin kokarinta wajen kula da yaran nan gaba dayansu.

Ranar Juma'a suna gida da yake yara babu islamiyya; ranar ne kuma suke gyara gashin yaran mai kitso zata zo. Tun da wuri Afafa ta tsefe nata kan, ita kuma Shukra da yake tun suna makaranta Khadeejan ta tsefe mata babu wanda ya ji kansu. Tun da suka gama cin abincin rana take faman lallaba Nasreen ta bari a tsefe mata amma har aka kusa kiran la'asar guda biyu suka tsefe. Bata son a taba gashinta kwata-kwata don haka taki ma zama a tsefe.

Khadeeja ta kamo hannunta tace ‘Zo kin ji Nas, kin ga fa Shukra zata fi ki kwalliya tunda ta tsaya an gyara mata nata.’

Ta zauna, har an fara tsifar ta zame kanta ta matsa tana zumbura baki. Afaf tace ‘Anti wallahi idan baki zare mata ido ba haka za kiyi ta fama da ita, sai ayi sati ana tsefe kanta a gidan Mama.'

Ta cigaba da lallabata amma sam ta ki tsayawa; don haka ta kama hannunta ta zaunar da ita tana cewa ‘Idan kika sake tashi sai na zaneki Nasreen, ko na sa almakashi na aske gashin kan ya koma kamar na Yaya Habib.' Ta dubi Afaf tace ‘Yaya Afaf dauko min slippers mai zafi idan bata tsaya an tsefe ba zaneta zan yi.’

Da sauri Afaf ta dauki slippers ta zo ta ajiye a gaba Nasreeen wadda ta fara shesshekar kuka tana fizge-fizge. Khadeeja ta dan rike gashin tace zan dake ki fa Nasreen, ki rufe min baki bana son jin kukanki.’

Nan da nan ta hadiye kukanta tana shessheka aka cigaba da tsifa Shukra tana mata dariya.
……….

Daga masallacin Juma'a ya wuce gida don ya gaida Hajia, da ya gaisheta sai ya wuce gida don Khadeeja tace idan ya dawo zai kaisu saloon ita da yara a wanke musu kai da yamma kuma akwai mai kitso a makota dama ita take musu.

Yana shiga gidan ya sami Yaya Jidda da yaranta biyu ‘yan mata Naja da Farida, bayan sun gaisa gaba daya Yaya Jidda ta dubeshi tace ‘Gidanka fa zamu tafi yanzu ni da yara, Hajia tace muje mu dubo su Afaf.'

Yace ‘To ai sai ku tsaya mu tafi, don nima gaisawa kawai zamu yi na wuce.’

Kafin minti goma sun gama, suka shiga mota ya ja su suka kama hanya, suna tafe suna hira.

'To ya yaran? Ana kula da su dai ko?’
PAGE 21

MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ta tambayeshi.

'Ah Alhamdulillah, gaskiya tana kokari.’ Ya fada cike da fara'a.

'To ai haka ake so, Allah ya sa ta dore.’

Tun a bakin gate yayi honk, gaba daya yaran suka fito banda Nasreen. Habib ya tayashi bude gate, bayan ya shigo da motar gaba dayansu suka yi masa sannu da zuwa.

A nan suka fara gaida Yaya Jidda, bayan ta amsa tace ‘Ina Nasreena?’

Afaf tace ‘Tana ciki tsifa Anti Khadeeja take mata.’

Suka wuce gaba daya suka shiga gidan; kafin Khadeeja ta amsa sallamarsu Nasreen ta fizge kanta wanda saura daya a gama tsefeshi ta tashi tana share hawaye tace ‘Abbaaa.’ ta fada tana zumbura baki.

Da sauri ya rungumeta ‘Ya haka na ganki wujiga-wujiga? Wa ya taba ki?’

Shukra ta tintsire ta dariya ta daga slippers din da aka ajiye tace ‘Kukan tsifa take Abba shine Anti zata zaneta da slippers, kaga nawa Anti yalash din ko kuka ban yi ba har aka tsefe yanzu za mu je saloon smma banda ita. Anti tace tunda bata so a taba kanta askeshi zata yi kamar na Yaya Habib.'

'Sannu da zuwa Yaya.’ Khadija ta fada tana karkade jikinta.

'Yauwa.' ta amsa ba yabo babu fallasa.

Ta kare musu kallo tana kokarin zama tana cewa ‘To yanzu Kuma tsifar ce sai an yi zaniya ni ‘ya su?’

Kafin Khadeeja tace wani abu Afaf tace ‘Anti wallahi idan aka biye mata sai an yi sati ana wannan tsifar, kullum haka ake fama da ita.’

Khadeeja tace ‘Ai ba a ma yi zaniyar ba ta bari an tsefe.’

Ta tsuguna ta gaida ita yayinda shi kuma ya ja hannun Nasreen din suka shige ciki.

Sai da ta kawowa Yaya Jidda ruwa sannan ta bi shi dakin. Tana shiga ta sameshi a tsaye yana cire kaya yayinda Nasreen take kwance a kan kujerar dakin, kafin tace wani abu yace ‘Wai me yasa ne sai an yi duka sannan za a yi tsifar? naga tun tuni dama ana mata kitson ban taba ji an doketa ba.’

Tace ‘Yanzun ma ba a doketa ba, ko Nasreen? Ta dai ki tsayawa a tsefe ne na takurata na tsefe mata, amma ba ayi duka ba.’

Ya kawar da kai ‘Ni dai bana son dukan yara, don Allah duk abinda yaro yayi kada a dokar min shi. Uwarsu ma bata dukansu, bana bari gaskiya.’

Ta sunkuyar da kai cikin kosawa tace ‘In sha Allah za a kiyaye.’
PAGE 22

MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ta ajiye masa ruwan da ta kai masa tana cewa ‘Lunch dinka yana nan a table.’ sannan ta fito ta barshi a dakin.

Bayan ta dawo parlor din ta tarar Yaya Jidda tana ta yiwa Afaf tambayoyi, ta wucesu ta shige kitchen.

Ta tsaya a tsakiyar kitchen din gaba daya kanta ya kulle; daga shigowarsu suna nema suce ta doki Nasreen, to yanzu haka suke so a bar Nasreen din ta dinga yawo da kanta? Gashi Afaf tace makarantarsu ana duba kitso duk ranar Monday. Ta jijjiga kai ta karasa ta dauki saucer ta zuba cake da cin-cin ta debo lemo a fridge ta jera a tray ta kawowa Yaya Jidda da yaranta, bayan ta ajiye a gabanta tace ‘Ya wajen su Hajiya?’

'Lafiya kalau.’ Ta amsa ba yabo babu fallasa.

Sukayi shiru sai surutun Afaf da take ta bawa Naja labari. Shukra ta matso ta kwanta a jikin Khadeeja tace ‘Anti nima lemon.’

Ta shafa kanta ta dubi Afaf tace ‘Yaya ki dauko mata lemon wanda babu sanyi.’

Ta mike, har ta kama hanyar kitchen din Yaya Jidda tace ‘Ku ba zaku sha lemon ba?’

Afaf tace ‘Ai da shi muka je school.’

Shukra tace ‘Anti tace idan an kawowa baki abinci mutum ya daina cewa zai ci, ni ma dai kawai lemon zan sha.’

Khadeeja tace ‘Ki dauko muku lemon idan kuna so.’

Jimawa kadan Abbansu ya fito daga dakin ya wuce dining ya zauna ya fara cin abinci; yana cikin cin abincin ya juyo yace ‘Kai Habib kun ci abinci ne?’

Yace ‘Tun dazu Abba, acici har tayi round 2.’ Ya fada yana zungurar Nasreen.
Chapter 5 · 0% Book details