← Book details Mijin Marigayiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 59

Sashe 48

Mijin Marigayiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

‘Amin ya Allah.’ Ta amsa sannan ta mike tayi musu sallama ta fice.

Har taje gida abun yana yi mata ciwo a rai; wato harma ya gayawa ‘yan uwansa da Naja zai tafi Hajji kenan an fara zuwar mata murna ta kuma ana yi mata Allah ya kaow na ‘yan baya. Kuma wannan ganin da ta yiwa Naja ya kara tabbatar mata da cewa Najan tana dauke da ciki domin yawu ne a bakinta irin wanda masu ciki suke tarawa.

Tun da ta shiga gidan Mommy ta san da matsala, amma dai bata tambayeta ba saboda bata son ganin kukanta. Ta san yanzu da ta tambayeta damuwarta sai tayi kuka mai isarta sannan zata gaya mata damuwar.

Sun zaune a parlor din Mommy bayan sun gama cin abincin rana suna hira yayinda Hammad yake ta kaiwa da kawowarsa, Mommy ta dubeta tace ‘Ki bar min Hammad a nan ya kwana biyu ki samu ki dan huta, naga duk kin yi wani zuru-zuru.’

Tayi gajeran murmushi tace ‘Gashi nan Mommy an bar miki, idan na shirya sai Ahmad ya mayar da ni gida ya karbo masa kayansa.’
PAGE 200
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Tayi dariya ‘Dama neman kai ake da shi.’

Jimawa kadan tace ‘Momy wai Abbansu ne zai tafi Hajji shi da Naja.’

Nan da nan fara’arta ta karu, tace ‘Kai ma sha Allahu, Allah ya amsa ibada.’ Ta kalli Khadijan suka hadu kuma kamar wadda aka tunawa wni abu tace ‘Ah, to ke me yasa ba za a hada dake ba ko kuma a fara kaiki, ko kinyi halin naki ne ya bata miki rai kin ce ba kya son kujerar?’

Ta sa yatsanta ta goge kwallar da ta fado a kwarmin idonta, ta kawar da kai sannan tace ‘Haka ya zaba ya fara tafiya da ita.’

Da mamaki ta zaro ido tana tambaya ‘To ke me kika yi masa, tunda dai ai kece babba ke ya kamata ya fara tafiya dake ko kuma ya tafi daku dukanku a lokaci guda.’

‘Yace wai ciki ne da ni don haka ba zai tafi da ni ba sai dai ko wata shekarar zuwa lokacin na haihu.’

Ta kalli cikinta sannan ta kalli fuskarta ‘Ciki? To ai karami ne kuma naga har yanzu ana zuwa da masu ciki sai dai idan basu da lafiya. Ni ban ma san kina da cikin ba ai.’

‘Nima bai fi last week na gane ba, ban ma sa rai da shi ba kawai na ganshi.’
Mommy ta dafa hannunta tace ‘To ai shikenan tunda ya zo sai muce Allah ya raya, amma dai masu ciki suna zuwa aikin Hajji har yanzu. Ana ta dai cewa za a hana amma ba a hana din ba tukunna. Kawai da yace bai so zuwa dake ba.’

Ta sake share kwalla tace ‘Tabbas Mommy bai so ba, don itama Najan ai ciki ne da ita. Kawai dai ya zata ban san tana da cikin bane shi yasa yake so ya raina min hankali kamar yanda ya saba.’

‘Ikon Allah.’

Suka yi shiru na dan lokaci; itama Mommy abun ya daure mata kai. Duk gidajen da ta sani na mata biyu ko sama to idan irin wannan damar ta samu babba ake fara kaiwa. Tabbas abun ya sosa mata rai to amma babu yanda zata yi. Ta dafa hannun Khadeejan wadda itama tayi nisa a nata tunanin tace ‘Kuma baki gaya masa Najan ma ciki ne da ita ba?’
PAGE 201
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

‘Ban gaya masa ba Mommy, kuma ba zan gaya masa ba. Yana sane da abinda yake yi Mommy, tsaf ya san tana da ciki. Ita da take tara yawu idan tana laulayi, kuma ko yau ma da na shiga wajenta da yawuna bakinta. Kawai dai da ita yayi niyyar zuwa, ko na gaya masa kuma ba canzawa zai yi ba sai dai kawai yayi ta kawo hujjoji.’

‘Uhm, to ai shikenan. Kin ga dama shi Hajji kiran Allah ne, kema in sha Allahu Allah zai kirawoki nan ba da dadewa ba ta hanyar da ya so. Kada ki sa wata damuwa a ranki balle ki illata dan da yake cikinki.’

Suka yi sshiru na dan lokaci, jimawa kadan ta gyara zama tace ‘Wallahi ni Mommy na ma gaji da auren nasa gaba daya. Tabbas ko shekara nawa zan yi da Mustapha ba zai taba canzawa ba, ba zai iya yi min adalci ba. Watakila ya daina so na, watakila kuma iya son da yake min kenan. Amma dai gaskiya na gaji Mommy.’

Ta dafa hannunta cike da kulawa tace ‘To ai hakuri zaki yi, dama shi aure ya gaji haka kuma ribar aure ta me hakuri ce. Baki sani ba ko ita abokiyar zaman naki wani abun take yi na biye-biyen malamai, ai duka ana yi.’

Tayi murmushin yake tace ‘Ai wallahi babu wani biye-biye Mommy, a hayyacinsa yake yi. Kawai dai idan hidima za ayi masa to ya fi so ni ya saka ni aiki, idan kuma morewa zai yi da harkar soyayya to wannan ita ta iya. Amma babu wani asiri haka ya tsarawa kansa.’

Ta sake kama hannunta tarike tana kallon fuskarta tace ‘Ki dai yi hakurin, in sha Allahu zaki ga ribarsa. Kuma idan dai Hajji ne da izinin Allah kema zai kirawoki.’

‘Uhm.’

Nan suka dauki lokaci Mommy tana bata baki. Can zuwa yamma ta shirya Ahmad ya mayar da ita gida ta barwa Mommy Hammad.

--------
Shirye-shiryen tafiya aikin Hajji sun kankama domin ana maganar saura sati uku alhazai su fara tashi. Duk wani abu da suke bukata na kula da gida Mustapha ya tanada ya kawo musu, kuma yayi mata bayanin abokinsa wanda dama ta san shi; shine zai kawo musu raguna kuma ya tsaya a yanka.

Yanzu kullum sai yamma tayi sai ya dauki Najan a mota su fice wai sun tafi bita, haka ta zuba musu ido tana ta bawa kanta hakuri.
PAGE 202
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Gaba daya maganar tafiyar ta fita daga ran Khadeeja, kuma Mustaphan ma gaba daya ya fice mata daga rai; ji take yi kamar matsayinta a wajensa bai wuce na mai aiki ba. Zuwa yanzu ta san wanda ma bai san halin da suke ciki ba ya san Naja tana da ciki domin tara yawunta ya karu kuma tayi fari tas irin na masu ciki. Sai dai har yanzu ita Khadeejan bata sanar da Mustapha cewa ta san Najan tana da ciki ba. Sai shirye-shiryensa yake yi yana zuwa sallama da mutane domin Hajia ta gama gayawa kaf dangi Mustapha zai tafi Hajji da matarsa. Danginsa da na Naja sai zuwa suke sallama, duk wanda ya zo sai ya cewa Khadeeja Alah ya kirawo ‘yan baya. Wannan kalmar ba karamin bata mata rai take yi ba, amma haka ta share ta kawar da kai.

Tun jiya bata jin dadi sai dai bata gane me yake damunta ba, haka take ta fama. Da yake ba itace da aiki ba kuma Hammad baya nan haka ta wuni a kwance. Daf da magriba ta fara gane abinda yake damunta; marata ce take ciwo ga wani amai da yake taso mata amma ya ki fitowa. Haka ta sha panadol ta shige dakinta ta kwanta. Wajen 9pm Mustaphan ya shigo dakin domin sanar da ita ya dawo kamar yanda ya saba. Har ya juya zai fita ya dan tsaya yace ‘Wai ya na ganki a kwance ne? kamar baki da lafiya.’

‘Uhm, mara tace take dan ciwo.’ Ta amsa a gajiye.

‘Ok, Allah ya sauwake. Ko kina bukatar wani abu?’

Tace ‘No ina jin zai daina don na ma sha panadol.’

Ya sake yi mata sannu sannan ya juya ya fice.

Can wajen 10:30pm ciwon ya matsa mata, tun tana daurewa har ta kasa. Ta lalubi wayarta ta kirawoshi, ba tare da bata lokaci ba ya shigo dakin nata. Kafin ya shigo ma ta riga ta shige bandaki saboda yanda take jin kamar zata yi kashi, kafin ta karasa toilet din abinda yake shirin fitowa daga jikinta ya riga ya fito sai jini da ya biyo baya gaba daya da aman da ya tokare mata kirji.

A tsugune ya sameta a bandakin, ya karasa da sauri ya duba halin da take ciki. Ya kamata ta mike sannan ta karasa ta zauna a kan toilet. Tace ya jirata ta wanke jikinta sai suje asibiti.
PAGE 203
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Nan da nan ta wanke jiki ta gyara sannan ta tattare zanin nata da bainda ya fita daga cikin nata gaba daya ta saka a leda sannan ta fito ta shirya suka kama hanyar asibiti. Babu wanda yayi magana sai shi da yake mata sannu lokaci zuwa lokaci; a haka har suka isa asibitin.

Ba tare da bata lokaci ba likita ya dubata kuma ya tabbatar da cewa cikin jikinta ya fice gaba daya, don ko wankin ciki ma ba sai an yi mata saboda komai ya fice. Aka rubuta mata magunguna aka sallamesu.

Tun a mota ta gane Mustapha bai ji dadin zubewar cikin ba, duk da ita ta fi shishiga damuwa da zubewar cikin; amma dai ta kula ba haka yayi ba wancan lokacin da tayi bari. Har yanzu tana jin ciwon mara don haka ba zata iya surutu ba.

Bayan sun dawo gida ta haye samanta ta sake yin wanka sannan ta sha magungunanta ta saka Hafsa ta hada mata indomie da shayi mai kauri ta zauna taci. Sai da taci ta koshi sannan ta kirawo Mommy da Yaya Mama ta sanar da su. A daren Momy ta so zuwa sai da Khadeejan ta hanata ta sanar da ita cewa ta sami lafiya su bari da safe sa zo; don haka suka hakura.

Can wajen daya saura ya sameta a dakin; tana kwance a gefen gado tana shirin yin bacci. Ya zauna a gefenta yace ‘Sannu.’

‘Yauwa.’ Ta amsa tana daga kwance.
Chapter 48 · 0% Book details