Sashe 4
Mijin Marigayiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta share hawayenta ta sauko da tukunya karama ta zuba Indomie din da ruwa da komai ta kunna wuta ta dora. Ta koma ta jingina da sink ta tsaya ta kafa tagumi; yanzu shikenan har ta gama amarcin, ko awa biyu yaran nan basu yi da zuwa ba amma sun gundireta, anya kuwa zata iya wannan rayuwar. Ko da yake dai yanzu suka zo ta san basu fahimceta ba itama kuma bata fahimcesu ba; amma dai zata dorasu a saiti kwanan nan.
Tana cikin juye Indomie din suka shigo kitchen din suka wanke hannuwansu, sai dai abinda ya bata mamaki babu wanda ya dauko plate din da yaci abincin ya kawo kitchen din; duk a dining table din suka baro mata. Ta gama juye Indomie din ta mikawa Habib bayan ya gama wanke hannu.
haka ta fito ta kwashe kwanukan daga dining su kuma suna zaune suna kallon TV. Ta hado shayi ta dauki guntun bread dinta ta wuce daki.
Bayan ta gama shan shayin ta dauko kofin ta fito, tana isa gaban sink din zata ajiye kofin ta ga Indomie din da ta dafawa Habib ko rabi bai ci ba kuma ga dukkan alamu ya koshi kenan.
'mtsewww' ta ja tsaki a Fili.
Ta wanke hannunta ta fito daga kitchen din. Har zata wuce daki Abbansu yace ‘Kizo ki shiryasu sun fara jin bacci kinga 10 har ta gota.’
Ta juyo ta dawo, ta dauki Shukra wadda ta riga ta fara gyangyadi Afaf, Habib da Nasreen suka bi bayanta. Sune suka nuna mata kayan baccinsu ta taimaka musu duk suka yi brush sannan suka shirya, ‘yan matan gaba daya suka haye gadon. Ta kalli gadon taga ma ba zai ishesu ba don haka ta koma dakinta ta dauko katifar da aka kawo mata saboda baki ta shimfidawa Habib a kasa. Ta gama tsaf zata kashe musu fitula Nasreen yace ‘Anti ba a kashe mana fitila sai mun yi barci.’
Ta mayar da fitilar ta kunna musu sannan ta fice daga dakin, ta wuce Abbansu a parlor ta shige dakinta. Ta riga ta gaji sosai don haka itama kayan bacci kawai ta saka ta rufe dakin nata ta wuce dakinsa, ta kwanta ta rufe idonta.
……..
Lokacin da Khadeeja ta fito daga dakinsa ya zata dakinsu Afaf zata koma don su kwana tare, amma sai ya ga ta shige dakinsa. Ya tashi ya shiga dakin yaran inda ya tarar dukansu sunyi bacci, don haka ya kashe musu fitilar ya fito daga dakin.
Ya kashe fitilun falon ya shige daki.
Tana kwance a kan gado kamar ma bacci takeyi, don haka ya kyaleta.
Bayan ya gama shirinsa ya kwanta, ya mika hannu ya tabata, ta juyo ta bude ido tace ‘Babe, ka shigo?’
'Um.' Ya amsa a gajarce.
Ta fara kokarin matsowa jikinsa, ya tashi zaune yana cewa ‘Kin baro yara su kadai, kin ga daga nan ma ai ba lallai ki jiyo motsinsu ba. Ni da na zata ma tare zaki kwana da Shukra a dakinki fa, she's just 3 bata saba kwana ita kadai ba.’
Ta dan matsa ta koma inda ta baro tana cewa ‘No, they will be fine fa, ba kaga a tsakiyar yayunta na sata ba kuma duk fa sun yi bacci. Ka ga na ma saka alarm wajen biyun dare zan je na dubasu sai kuma da asuba.’
'Uhm, amma dai da kin daure kin kwana da su din.’
'Kada ka damu ina jinsu.’ Ta fada sannan ta gyara kwanciyarta ta juya masa baya ta rufe ido. Haka kawai zai ce taje ta kwana a cikin yara; to ai ko ‘yar da ta haifa ce shekara uku ai raba wajen kwana zasu yi. Ba zama ta fara wannan aikin ba balle ya sallamawa yaran ita.
Har barci ya fara daukanta suka ji an murda kofar, ya riga ya murda mukullin da ya shiga don haka sai kofar bata bude ba. Aka kwankwasa a hankali, suka tashi zaune tare shi da Khadeejan. Kafin suce wani abu Nasreen tace ‘Abba Shukra ce ta tashi zata sha shayi.’
Ya kalli Khadeeja yace ‘Oh, na manta ban gaya miki ba tana farkawa shan tea da daddare, tunda aka yaye ta ta saba. Kije ki hada mata shayi, da ga ta sha zata koma bacci.’
'Shayi? A wannan daren? Ko fa 4 hours basu yi ba da cin tuwo, ikon Allah.'
‘Idan baki bata ba haka zata yi ta yiwa mutane kuka har sai an bata, kije ki hado mata gobe sai ki hada ki sa a flask kafin ta kwanta.’ Ya fada yana sake bata rai.
Ta daura zaninta a kirji ta sauka daga kan gadon ta fice daga dakin cike da takaici.
A tsakiyar gadon ta sami Shukra tana kuka, duk yanda zuciyarta ta kai ga kuna a wannan lokacin dole ta danne fushinta. Ta mika mata hannu tana dan murmushi tana cewa ‘Ahh! Sorry Shukra, ya aka yi? Kukan me kike yi?’
Cikin shesshekar kuka da gwarancinta tace ‘Tea.’
Ta zauna a gefen gadon ta rungumeta tana shafa bayanta tana mata magana cikin lallashi ‘Ya Isa, ya isa. Da safe ke zan fara hadawa shayi kinji Baby Shukra, kinga dare yayi ko? Muyi bacci da safe sai mu sha tea ko, harda bread ma da kwai ko?’
Ta gyada kai alamar eh, amma fa hawayenta ya ki daina zuba harda shesshekar. Ta cigaba da shafa bayana tana lallabata yayinda Nasreen ta koma ta kwanta har bacci ya fara daukanta. Abbansu ya ya turo kofa ya shigo dakin, Shukra ta leko ta kafaradar Khadija cikin shessheka tace ‘Abba tea zan sha.’
Ta kwace daga jikin Khadijan ta sauko ta taho wajensa, ya rage tsawo ya dauketa ya rungumeta yana cewa ‘Ya isa, Anti bata baki shayin ba?’
'Tace sai da safe.’ ta fada tana shessheka.
Ta mike ta rungume hannuwanta a kirjinta ta kalleshi da fuskar tausayi tace ‘Babe, ka barni da ita zata koma bacci kuma a hankali zaka ga ta ma daina farkawan shan shayi da daddaren. Ka barni na lallabata idan tayi bacci zan taho.’
Kallonta yake da mamaki a fuskarsa, sai da ta gama sannan yace ‘Yunwa fa take ji, haka zata kwana da yunwa. She's only 3, idan ta girma da kanta zata daina duk yayyenta ma haka barsu take raininsu.’
Cikin kosawa tace ‘Kai dai ka barni da ita mana, I promise you she will be just fine.’
Ta karaso kusa da shi, ta mika hannu ya dafa kafadarta yana cewa ‘Kin ga, ki yi hakuri ki hado mata shayi kada ki sakata kwana da yunwa tunda bata saba ba. A hankali zaki ga da kanta zata daina.’
Murya kasa-kasa tace ‘Ohkk!’
Ta wuce ta barshi a nan ta nufi kitchen; tea at 1pm, wannan wane irin tashin hankali ne? Idan da ya kyalesu ta san tabbas zata rabata da wannan shan tea din amma har wani cewa yakeyi kada ta barta da yunwa. Ta karasa kitchen din ta hado mata tea a kofi ta daukonta fito.
Tana zuwa ta sameshi zaune a gefen gadon ragowar yaran duk suna ta baccinsu yayin da yake zaune rungume da Shukra; har bacci ya fara dibanta amma tana shiga ya dagata yace ‘Yauwa Baby tashi ga shayinki.’
Ta tashi tana muttsike ido, ya mike tsaye ya nunawa Khadijan wajen ta yana cewa ‘Zauna sai na ajiye miki ita idan kin gama bata tayi bacci kya taho.’
Ya ajiye mata ita a kan cinyarta ta fara bata shayin sannan ya fice ya barsu.
Bayan ta gama bata shayin ta sakata tayi fitsari sannan ta kwantar da ita ta dan jijjigata bacci ya fara kwasarta sannan ta wuce dakin. Ko da ta shiga dakin ya riga yayi bacci, don haka ba tare da ta kunna fitila ba ta lalubi waje ta kwanta a gefen gadon. Motsin kwanciyarta ne ya farkar da shi, ya dan matso ya rungumota ta baya yana sumbatar bayan wuyanta. Ta dan motsa tace ‘Mmmm!’
Yace ‘Kin San gobe yara zasu school ko? Sai ki tashi da wuri don ki shirya su.’
A take jikinta yayi sanyi; gaba daya ma ta manta da wannan tunda ita ta riga ta sanar da kawarta su yi mata attendance ba zata koma ba sai tayi sati.
Ya cigaba da lalubenta tana kokarin zamewa, saboda ita gaba daya ma komai ya fita daga ranta; a halin yanzu ma kuka take son yi. Sai dai haka ta hakura ta barshi yayi yanda ya so sannan ta kwanta tana fargabar yanda zata tashi nan da awowi kadan ta cigaba da hidima.
Ana fara kiran assalatu ya tasheta daga bacci, sai da tayi da gaske sannan ta iya saukowa daga kan gadon. Tayi alwala ta wuce kitchen tunda da dan sauran lokaci kafin a tada Sallah. Ta tsaya a tsakiyar kitchen din tana tunanin inda zata fara; a hankali dabara ta fado mata; macaroni da sauce zata dafa musu in ya so sai ta dafa indomie da kwai suyi breakfast. Nan da nan ta dora sannan ta debo tsofaffin flasks dinsu da ta gani a store ta wanke sannan taje tayi Sallah.
Ta zata idan ya dawo daga masallaci zai tsaya ya tayata shiryasu amma ga mamakinta sai ya wucesu a parlor ya koma daki ya kwanta ya cigaba da baccinsa.
7:15 am ta gama komai duk ta yi musu wanka sun shirya, suka zauna a dining table ta kawo musu abinci ta zubawa kowa Indomie da dafaffen kwai guda daya. Daga fuskokinsu ta san ba indomie suka so ci ba, suna cikin cin abincin yayinda ita kuma take zaune a table din tana bawa Shukra a baki Nasreen ta kalleta tace ‘Anti da ma dankali da kwai kika soya mana.’
Ta kalleta tana murmushi tace ‘Saboda kar ku makara shi yasa nayi sauri na dafa Indomie, but in sha Allah weekend idan babu makaranta sai a soya muku dankali kin ji. Yanzu maza ki cinye kafin Abba ya fito ya kai ku school.’
Suka cigaba da cin abincinsu. Jimawa kadan Abbansu ya fito yana rike da mukullin mota, suka hada baki gaba daya suka gaisheshi. Bayan ya amsa yace ‘Maza ku gama mu wuce a school kada ku makara.’
Ya kula da ragowar kwai a plate din kowa banda Habib, ya dubeshi yace ‘Kai ina naka kwan.'