← Book details Mijin Marigayiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 59

Sashe 33

Mijin Marigayiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan ya kai ‘yan makaranta ya dawo suka zauna tare a parlor din sama suna cin abinci yayinda Hammad yake hannun Rashida. Shiru suke cin abincin babu wanda yake magana, kamar ma dai basa cikin walwala.
PAGE 135
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ya ajiye cokalin dake hannunsa yace ‘Kin ce babu wani abu da kuke bukata saboda taryar baki ko?’

Ba tare da ta daina cin abncinta ba tace ‘Eh. Ni kam mai ai don dai ka hana ne da sai nayi tafiyata wajen Mommy idan aka kawota aka tafi sai na dawo da daddare ko ma da safe.’

‘No, don Allah ki bar wannan maganar. Ai ya kamata dai ace a samu a karbi bakin nan cikin mutunci.’

‘Um.’

Suka cigaba da cin abincinsu, jimawa kadan yace ‘Hajia ma tace a nan zasu zo suyi biki ranar lahadin, in ya so sai su tsaya su karbi amarya sannan su tafi.’

Ta kalleshi suka hada ido sannan ta kawar da kanta, wani malolo ya zo ya toare mata makogoro; su Hajia zasuyi biki a nan? Saboda suna murna za ayi mata kishiya ko me? Ta dauki kofin shayinia mai zafi ta kurba da fatan zafin shayin zai tafiyar mata da abinda ya tokare mata makogoro amma hakan bai samu ba. Ta kalleshi a jigace tace ‘Ka ga shikenan sai na tafi gidan Mommy ko? Tunda ka ga masu karbar amarya zasu zo.’

Ya dan zaro ido yana cewa ‘Haba dai! Hakan kuma ai bai yi tsari ba, kina matar gida kuma azo biki gidan ba kya nan. Ko ba haka ba ma kin san Hajia zata ga kamar kin rainata ne shi yasa zaki tafi ki barsu su kadai suyi bikin. Please kiyi hakuri kawai saboda kada abun ya zama wata fitna kuma. Kin ji?’

Ta daga kai tana cewa ‘Uh.’

‘Yauwa, please kiyi hakuri a gama taron nan ba tare da wata matsala ba.’

Tayi gajeran murmushi tace ‘In sha Allah.’

Ya ture kwanon bayan ya kurbe dan ragowar shayinsa sannan yace ‘Zan saka miki kudi a account dinki saboda na san zaki iya bukatar wani abun ko don baki. Akwai ruwa da lemo wanda zan kawo, abincin kuma dama tunda kika ce ba zaki yi a nan ba na bayar da kudin don haka su Hajia zasu taho da shi.’

‘Ok.’

‘Idan kuma da bukata zaki iya yin wani abincin a nan ko da kadan ne.’

‘Ok, babu damuwa.’

Ya mike ya shige dakin domin ya karasa shiryawa. Nan take itama ta ture kwanon indomie din ta mike ta haye sama. Kuka take son tayi ko zata ji sanyi a ranta, amma bata so ta bata lokaci musamman da yake yana jiranta kuma tare zasu fita.
PAGE 136
MIJIN MARIGAYIYA
A Huasa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Haka tayi sauri ta shirya suka sauko tare, ta karbi Hammad a wajen Anti Binta suka fice suka bar Anti Binta Hafsu wadda kanwar Rashida ce aka kawo mata bayan an yi auren Rashidan tun kafin ta haifi Hammad.

Haka suka zauna a mota babu wanda yake magana da dan uwansa; ya riga ya kula da yanda take nema ta tayar masa da fitna a wajen bikin nan amma ba zai barta ba. Sosai ya ji dadi da Hajia tace zasu zo nan suyi biki don baya so ta bayar da matsala idan an kawo amarya, amma ya san tunda Hajia tana nan babu wata matsala da zata basu. Haka yaje ya ajiyeta a gidansu sannan ya wuce.
………

Tana shiga gidan ta sami Ahmad a parlor yana shan shayi; nan da nan ya mike ya karbi Hammad daga hannunta.

‘Ina Mommy?’ ta tambaya bayan ta amsa gaisuwar da yake mata.

‘Tana dakin Baffa.’

Ba tare da ta bashi amsa ba ta bar masa Hammad ta wuce ta nufi dakin.

A zaune ta hango Mommy a kan dadduma ta mike kafa da waya a hannunta, ta jefar da mayafinta ta karasa gaba daya ta fada jikin Mommy ta rushe da kuka.

‘Inna lillahi wa Inna ilaihi raji’un! Khadeeja me ya faru? Ina Hammad din?’ Mommy ta tambaya cikin tashin hankali.

Da kyar ta bude baki tace ‘Yana hannun Ahmad.’

Ita kanta saida taji ajiyar zuciyar da Mommy din tayi, sanna ta cigaba ‘To me ya faru kike wannan kukan haka? Ko Mustaphan sakinki yayi ne?’

Ta jijjiga kai alamar a’a ba tare da ta dago ba, ta cigaba da kukanta. Kawai sai Mommy ta hakura da tambayar ta zuba mata ido, a hankali ta daga hannunta tana shafa kanta; ta dai san da maganar saura kwana uku a daurawa Mustapha aure don haka watakila wani abun yayi mata wanda ya sosa mata rai shine ta taho nan tazo tana wannan kukan. Saida ta dauki loakci tana wannan kukan sannan ta dan numfasa ta dago ta kalli Mommy, suna hada ido kuma sai ta sake fashewa da kuka.

Cikin sheshekar kuka tace ‘Mommy ba zan iya ba, ba zan iya ba Mommy.’
Ta dago fuskarta tana share mata hawayen tace ‘Menene ba zaki iya ba Khadeeja?’
PAGE 137
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ta tsagaita da kukan sai dai hawayenta ya kasa daina fita; ta sa bayan hannunta ta goge hawayen ta kalli Mommy suka hada ido na dan lokaci. Ta kawar da kanta tace ‘Mommy ban san me Mustapha yake so da ni ba. Bayan ya gama raina min hankali lokacin da yana neman aure yanzu kuma duk da ban bashi matsala ba amma ba zai barni na zauna lafiya ba.’

Ta share mata hawaye tana cewa ‘Me yayi miki kuma.’

‘Mommy nace masa ina so ranar da za akawo amarya na taho nan idan sun gama kaita sai na koma ya hana ni, na hakura nace zan zauna amma ba zan yi taro ba; su kawo amaryarsu kawai su tafi. Da farko har ya yarda amma yau yake gaya min wai babarsa tace zata zo a nan gidan namu zata yi biki, kuma yace ba zan tafi na barsu ba. Mommy so suke bakin ciki ya kasheni? Dansu zai yi min kishiya kuma suzo suna celabrating a gaba na?’

Da mamaki Mommy tace ‘Ikon Allah, ita mahaifiyar tasa ce zata yi biki saboda zai kara aure?’

Ta sa hannu ta goge ragowar hawayen da yake kan fuskarta sannan tace ‘Eh Mommy, wai zasu zo suyi biki. Kin ga kenan nace ba zan karbi amarya ba amma zasu yi min dole.’

Mommy ta kama hannunta ta kalleta sannan tace ‘Kiyi hakuri kin ji, zaki iya. Kishiya bata kashe kowa ba in sha Allahu kema ba zata kashe ki ba. Ki bi su a hankali, dare daya ne ayi ya wuce. Da an kwana biyu itama zata zama kamar ke kuma yanda yayi miki haka zai yi mata.

Ta jijjiga kai tana murmushi mai dauke da ma’anoni tana cewa ‘Hmm! Mommy ba zai taba yi mana adalci ba. Kina ganin yanda tum kafin ta shigo shi da yaransa da ‘yanuwansa suka karkata wajenta. Gaskiya ban saka rai Mustapha zai iya yi min adalci ni da matarsa, sai dai kawai nace Allah ya bani hakuri ko kuma ya kawo min mafita mafi alkhairi.’

‘kada ki damu, ai ba shi yayi kansa ba, in sha Allahu Allah ba zai bari ya cutar dake ba daga shi har ‘yanuwan nasa gaba daya.’

‘Hmmm!’ ta sunkuyar da kai tana kallon yatsinta da take wasa da su.

Jimawa kadan tace ‘Mommy bana son ayi min biki a gida, bana son a akwo min maryarsa ace za a bani amanarta ko ayi mana fada tare. Amma kinga duk sun shirya hakan zasu yi.’
PAGE 138
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Mommy ta sake kamo hannuwanta duka biyun ta kalleta suka hada ido sannan tace ‘Kada ki damu, kamar yanda na gaya miki na ranar ne kawai. Kuma kema ‘yan uwanki zasu zo, duk da kince kada azo da yawa toh yayayrki zasu zo da kamar mutum hudu haka. Nabila kuma tace gobe zata taho ta tayaki kwana zuwa lokacin da zasu gama bikin. Kada ki damu in sha Allahu omai zai wuce.’

Haka suka zauna Mommy tayi ta bata baki har zuwa yamma. Ta samu zuciyarta tayi sanyi amma dai bata da tabbacin ko zata iya dauka, ta dai hakura taga yanda zata kaya kamar yanda Mommy tace.

Sai da yamma sanna ta shirya ta koma gidan zuciyarta cike da wasi-wasi.

Washegari ‘yan uwan amarya suka zo suka yi kafi. Basu ja fitna ba don haka lafiya aka rabu, ta sa Hafsa ta mika musu kuloloin abincin da ta bayar aka dafa musu; don ita tunda suka shigo gidan ta haye sama kuma har suka gama bata sauko sun hadu ba. Sun tura Hafsa taje ta kirawota sau ba iyaka amma haka hafsan take dawowa tace musu saman a rufe yake. Haka suka gama kafinsu suna ta rangada guda, ga turare da suka bade gidan dashi. Sai da suka kusan gamaw sannan yara suka dawo daga makaranta, nan da nan suka shige cikinsu da yake sun saba da kannenta saboda yawan zuwa gidansu da suke yi.

……….
Dawowarsu daga gidan kafi yayi daidai da dawowarta daga wajen lalle, a zaune ta samesu a farfajiyar gidan ana ta hirarraki. Ta dubi yayarta Ummi tace ‘Yaya har kun dawo daga kafin?’

Ta tabe baki tace ‘Hmmm! Mun dawo’

Ta dan kalleta da alamar tambaya tace ‘Ya naga kina yatsina fuska? Komai dai ya tafi dai-dai ko?’

Salma wadda cousin dinta ce tace ‘Um babu laifi. Amma fa mu a kasa Mustaphan ya nuna mana daki guda daya da parlor yace nan ne naki kuma a nan mukayi kafi. Saman gidan nan ma dai ‘yar mulkin uwargidan taki bata ko bari mun hau ba ta ja kofa ta rufe don bamu ko isa ta sauko mu gaisa ba ta aiko mana da kulolin abinci kamar wasu mayunwata.’

Ta zmburi baki ‘Ban gane a kasa ya baku daki ba? Ai ni sama mukayi da shi kuma ya amsa min a kan haka.’
Chapter 33 · 0% Book details