← Book details Mijin Marigayiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 59

Sashe 50

Mijin Marigayiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta mike kamar wadda aka tsikara ta nufi gaban wardrobe, ta sauke akwati ta fara zuba kayanta. Ba zata iya cigaba da wannan rayuwar ba, gara kawai ayi ta ta kare.

A hankali ya turo kofar dakin ya shigo da sallama, fuskarta fayau kamar ma farinciki take. Ta dubeshi ta amsa sallamarsa ta cigaba da jera kayanta a cikin akwatin. Ya dubeta da mamaki yace ‘Ya naga kina hada kaya, ko wardrobe din kike gyarawa?’
PAGE 208
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ta dan tsaya da zuba kayan ta kalleshi tace ‘No ba gyarawa zan yi ba, gidan mu zan tafi.’

Mamakinsa ya karu, ya karsa matsawa kusa da ita ‘Ban gane gidanku zaki tafi ba bayan yanzu zamu tafi, shigowa ma nayi na gaya miki ki fito kuyi sallam da Naja zamu wuce.’

Ta rufe akwatin ta zuge sannan ta juya cikin wardrobe din ta dauko jakarta ta sake ajiyewa a kan gadon. Ta kalleshi tace ‘Ka bani minti biyar na karasa hada kayana na fita sai ka rufe gidan gaba daya don nima gidanmu zan tafi.’

Ya dan fara fusata ya matsa ya sha gabanta yana cewa ‘Bana son wulakanci Khadeeja, wai ke me yasa ne duk lokacin da mutum yake cikin uzuri yake so kiyi masa wani abu sai kin yi fitna ne? an gama magana dake amma yanzu saboda kina so ki sa muyi missing flight zaki fara maganar zaki tafi gida.’

Tayi murmushi ta daga kai ta kalleshi tana cewa ‘In sha Allahu wannan itace fitna ta karshe da zan yi maka Mustapha, daga ita ba zan sake ba. Gidanmu zan tafi Mustapha saboda na gaji da aurenka, kuma na gama aurenka daga yau. Zaka iya sakina yanzu ko kuma duk lokacin da ka sami natsuwa ka rubuta min takardar sakin ka aiko gida; amma ba zan sake zama a matsayin matarka ba.’

Gaba daya yawun bakinsa kafewa yayi saboda bai taba zaton Khadeeja zata iya fada masa haka ba, ya saketa! Kuma a wannan lokacin; ya kalleta ya sunkuyar da kai, jimawa kadan ya sake kallonta sannan yace ‘Saboda kujerar Makka kike so ki kashe aurenki Khadeeja? Kujerar da na gaya miki next year dake za a tafi. Tukunna ma kin san hukuncin matar da ta nemi saki a wajen maigidanta ba tare da wani dalili ba?’

Ta jijjiga kai tana murmushi a daidai lokacin da kwalla ta fado daga idonta, ta share kwallar sannan tace ‘Ko daya, kujerarka ba ta kai ta daga min hankali ba tunda dai kasar Makka ta Alla ce ba taka ba. Alhamdulillahi ma kace wadda ta nemi saki ba tare da dalili ba; don ni ina da dalili kuma Allan da ya halicceni ya fi ni sanin dalilin. Amma tabbas yau zan bar gidanka da aurenka Mustapha.’

Ya ja baya ya sake kare mata kallo, yace ‘Kin san me kike fada kuwa Khadeeja? Please idan wasa kike ki bari kada ki saka muyi missing flight.’
PAGE 209
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Tayi yar dariya yayinda ta ware hijabinta ta saka tana cewa ‘Ba wasa nake ba, amma dai kana da zabi. Ka sakeni yanzu ko kuma ka tafi idan ka dawo ka rubuta min takardar ka aiko min gida.’

Ta kwayeshi ta bude dauko jakarta daga kan gadon ta nufi gaban mudubi.

Yana tsaye mamaki ya hanashi magana. Yana daga kai idonsa ya sauka a kan agogon bangon yake kafe a saman dakin; 12:52pm agogon ya nuna; shi da aka cewa su zama suna cikin airport kafin azahar.

‘Mteww!’ ya ja dan gajeran tsaki sannan ya fesar da iska daga bakinsa. ‘Khadeeja yanzu ya kike so nayi da yaran bayan mun gama magana dake? Kuma me nayi miki da har zaki rike a matsayin hujjar da ta saka zaki ce na sake ki?’

‘Yara kam ai yanzu ba matsalata bane, duk yanda kayi da su daidai ne. Ni dai zan tafi, yanzu in sah Allah.’

Ta sauke akwatinta ta fara ja tana nufin koafr dakin.

Ya bi bayanta da kallo; to me yayi mata da har zata ce ya saketa a wannan lokacin? Anya kuwa ta san menene zawarci? Kawai saboda bakin cikin ba da ita zai fara tafiya aikin Hajji ba? Ko ma me take nufi ya kamata ya cika mata burinta, watakila kafin ya dawo ta dawo hayyacinta kuma ta gane mahimmancin aure a rayuwarta. In ya so idan ya dawo da ita sai ta hakura ta zauna tunda dai shi bai ga wani abu da yayi mata ba.

Tana daf da karasawa bakin kofar yace ‘Khadeeja.’

Ta juyo ta dan tsaya ‘Ki je na sakeki saki daya.’

Ta yi sauri ta juya fuskarta saboda kaucewa hada ido da shi; duk da ita nema kuma da yakinin zai aikata haka amma sai da fitar kalmar tayi mata ciwo. Ta sake juyowa cikin murya kasa-kasa tace ‘Nagode.’

‘Zaki yi nadamar rabuwa da ni Khadeeja.’ Ya fada a gajarce.

Ta kalleshi tayi murmushi sannan ta kawar da kanta ta faki idonsa ta goge kwallar da ta taru a kwarmin idonta.

Bugun kofa ne ya klatsesu da Shukra tana cewa ‘Abba Anti tace zaku makara fa.’

‘Um, gani nan zuwa.’ Ya amsa daga cikin dakin.

Ya wuce Khadeejan ya bude kofar ya fice. Ta bi bayansa janye da akwatinta. Shukra ta tsaya a gefenta tace ‘Anti kema harda ke za a tafi?’

Ta kama hannunta tace ‘A’a ni gidanmu zan tafi ba da ni za a tafi ba.’
PAGE 210
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

‘Gidan Mommy? To damu zaki tafi?’ ta tambaya da mamaki.

‘Eh, gidan Mommy zan tafi amma ba daku zan tafi ba. Abbanku zai gaya muku wadda zata zauna da ku.’
Gaba daya yaran suka zuba mata ido suna kokarin gani me take fada. Ta kwalawa Hafsa kira ta bata umarni ta hada kayanta su tafi gida. Ba tare da bata lokaci ba ta juya.

Ta dubi Naja wadda take zaune tana binsu da kallon mamaki tace ‘Maman Rukayya sai kun dawo, Alah ya amsa ibada Alah ya maimaita mana.’

‘Amin.’ Ta amsa a gajarce sannan ta dubi Mustapha tace ‘Ban fa gane ba, me yake faruwa ne?’

Kafin ya bata amsa tuni Khadeeja ta ja akwatinta ta fice daga parlor din. Shukra wadda ta karasa ta fada jikin Abbanta ta rushe da kuka; saboda ta kasa fahimtar me yake faruwa su da aka ce za ayi tafiya har Abbansu a barsu da Anti kuma Antin ta fara tafiya.

Ya dubi naja yace ‘Cewa tayi na saketa kuma na saketa, tunda ita ta nema.’

Ta dan firgita ta dafe kirji, bata san lokacin da yawun da yake bakinta ya wuce ba tace ‘Saboda me? Kai kuma ka biye mata?’

‘Saboda bakin cikin zan tafi dake Hajji ban tafi da ita ba.’ Ya fada cike da adcin rai.

Ya karasa ya zauna a kan kujera a jigace kamar wanda aka tura.

Sukayi cirko cirko suna kallonshi.

Habib ya shigo a guje ko sallama bai yi ba, yana cewa ‘Abba na ga Anti tafi. Me yake faruwa ne? waye zai zauna damu?’

Ya mike a jigace yana cewa ‘Maza kowa ya debo kaya ko kala daya ne mu wuce, sai na ajiyeku gidan Hajia. In ya so ko gobe sai ku dawo da Yaya Jidda ku debi kaya. Antin ta tafi.’

Ya fice batare da ya sauraresu ba Naja ta rufa masa baya.

Nasreen ta kalli Habibi ta kare gefeb bakinta kamar me rada tace ‘Ya saketa.’

Ya zaro ido zai yi magana suka jiyo muryar babansu daga kafar bene yana cewa ‘Maza fa ku sauko.’

Suka mike gaba daya suka shirya suka fice.
PAGE 211
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ba karamin mamaki Hajia da Alhaji suka yi ba da Mustapha ya gaya musu ya saki Khadeeja.

Shi kadai ya shiga da yaran don ita Naja ma cewa yayi ta zauna a mota saboda kada ta bata musu lokaci. Suna shiga yaran suka wuce cikin gida shi da Hajia da Alhaji suka tsaya a parlor yana musu bayanin abinda ya faru.

Alhaji yace ‘To kai wane irin rashin hankali ne wannan? Ai don mace tace a saketa ba a sakin nata. Zuciya ce ta kwasheta kuma sai daga baya zata zo tana nadama. Da ka sani ka barta da aurenta idan ma tafiyar zata yi ta tafi idan ka dawo kalau zaka ga ta dawo.’
A fusace yace ‘Alhaji yarinyar ce ta kureni, ita kullum sai dai ay mata yanda take so amma ita ba zata yi yanda ake so ba? Taje idan mutuwar aure dadi ne ai ta samu sai ta dana ta fi shiga hankalinta.’

Hajiya tace ‘Ai shikenan tunda haka ta zaba. To yanzu in Hammad din da Rukayya? Ban gansu tare da ‘yan uwansu ba.’

‘Shi Hammad dama yana gidansu, ita kuma Rukayya gidansu ta kaita.’

‘Ai shikenan, Allah ya sauwake. Idan ka dawo a san yanda za ayi domin dai aure bai kamata ya mutu saboda kujerar hajji ba.’ Alhaji ya fada cike da nadama.

Mustapha ya dubi Hajia yace ‘Mukullin gida yana hannun Habib in an jima Baba Sani abokina zai zo ya kaisu shi da Afaf su debo kayansu su rufo gidan. Idan sun dawo sai ya bawa Alhaji mukullin gidan ya ajiye min. akwai ATM card din a hannun Afaf idan ana bukatar wani abu na kudi sai taje ta ciro ta bayar.’

Yayi musu sallama ya fice zuciyarsa cike da damuwa.

……….
Zuciyarta fayau ta fito daga gidan tana addu’ar Allah ya sa iyakar zamanta kenan da Mustapha tunda ta san saki daya yayi mata. Sun tsaye a bakin titi ita da Hafsa suna jiran mota ya zo ya wucesu a guje a tashi motar. Ta bi bayan motar da kallo tana murmushi; ta tuna lokutan da yake zuwa ya wuceta a titi zata tafi makaranta amma ba zai iya rage mata hanya ba. Tayi murmushi ta kawar da kai. Jimawa kadan da wucewarsu ta sami mota, suka hau suka nufi gidan Mommy.

Tana tura gate din gidan Baffa ne a tsaye yake rufe motarsa, da alama dawowarsa kenan.
PAGE 212
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Chapter 50 · 0% Book details