Sashe 46
Matar Dan Birni Part 1 Complete Novel · about 2 min read
Suna zuwa kasa Nana ta saki hannunta tana zabga mata harara kafin ta ce,"ke kam aminatu yaushe zaki hankali?yaushe zaki daina wannan sakarcin da sakin baki haka a gaban kowa eye?"tura baki aminatun ta yi tare da cewa,"to Nana haka kawai sai na barsa ya dinga lalube Ni bayan shi b mijina bane duba fa kiga bakina duk sanda ya samu dama sai ya ci min idan na barsa ai sai dai wata rana na tashi na ga bani da baki,Ni wallahi ki hanasa ko na kai kararsa wajen ab.....bige bakinta nana ta yi tana mai rasa abin cewa ga kunyar da ta lullubeta saboda zantukan aminatun,dan Kore zancan sai Nana ta yi saurin sako mata zancan Anne, "aminatu me yasa jiya baki kaiwa Anne abinci ba?"zaro ido aminatu ta yi tare da cewa "kai kai tab wallahi yau na kuma tabbatar da cewa matar nan bata kaunata kaji wata karya"harara nana ta kuma jefawa aminatun tana cewa "annen ce take karya?"da sauri ta rufe bakinta tare da cewa "a a ba ita ba ce subtar baki nayi amma dai nasan na kai mata abinci ta koro ni wai bani na saba kai mata ba dan haka na mayar ba zata ci ba,kuma da nace mata zan mayar larai ta kawo mata shima cewa ta yi bata so dan yau tunda har na taba abincinta bazata ci ba,bayan ma bata san kusan kullum ma Ni nake girkin ba",dan jim nana ta yi kafin ta ce ai shi kenan amma dai ki kiyaye nan gaba idan hakan ta faru ki fara gaya min",yes ma aminatu ta fada tana mai daga hannunta da kamewa a tsaye irin yadda sojoji suke yi,girgiza kai kawai Nana tayi ta wuce bangarenta a ranta kuwa ta gasgata aminatu dan tasan irin tsanar da anne ta yi mata tsaf zata yi hakan,dan haka take ta share maganar a nan wajen.