Sashe 44
Matar Dan Birni Part 1 Complete Novel · about 8 min read
Da sauri mus' ab dake shigowa falon ya ɗan lumshe idanunsa tare da fitar da huci ta bakinsa,dan kuwa karar aminatu tamkar a cikin kunnensa haka ya ji ta,kai tsaye ya nufi inda yake da tabbacin daga nan yake jigo sautin kukanta,
Sautinsa ne kawai ya fi na sallamar da yayi shima ba dan tsananin laƙantar motsinsa da aminatu ta yi ba da ba zata ji ko tasan cewa yayi sallama ba,duk da ta ji shi a jikinta ta kuma ji shi a motsinsa hakan baisa ta dago kanta daga durkushen da tayi tana faman murza ƙafarta hade da kukanta da ya yi kasa sosai ba.a hankali ya tako gabanta haɗi da dukawa daf da ita har tana iya shaƙar numfashinsa tare da ƙayataccen ƙamshinsa da yake matukar tafiya da ita tun bata san kanta ba,hannun sa me taushi ya sa ya kama yatsun kafar yana ɗan murzawa kadan kafin cikin deep voice ɗinsa da ba kowa ne ya cika jinta ba,ya ce",baby crayin me ne ya samu kafar kuma?"dago kanta ta yi ta zuba masa oily eyes dinta tana kara kebe bakinta irin na jikakkun yara kana ta ce,"wani mugune wai shi isma ya take min kafa ya wuce kamar ya taka dabba wallahi kuma ba zan yafe ba duniya da lahira wutabalbalin acibalbal din innawuro ta ruga aradun Allah sai na rama",zuba mata ido yayi cike da mamakin sakarcinta duba fa tayi Allah ya isa kuma tana cewa sai ta rama,duk da cewa Allah ya isar ma tata ce ta daban dan bai taba jin irinta ba.bakinsa ya bude a hankali, kana kallonsa kasan ba karamin takura kansa yake yi wajen yin magana ba,ya ce, "to ba kin yi Allah ya isa ba ki bari Allah ya isar Miki idan kuma baya sane sai ki yafe masa",murguɗa karamin bakinta tayi tana mai farfara fararen kwayar idonta kana ta ce, "aradun Allah yana sane,dan kawai saboda dan uwanka ne shine zaka ce na yafe?to bani yafewa mugu me sh....karar faduwar abu ne yasa ta hadiye maganarta tare da juyawa dan ganin abinda ya fadi,ido hudu su kayi da isma yana watsa mata kallon gargaɗi a fakaice ba tare da ya bari mus ab ya gani ba.kana cikin sauri ya tsugunna yana daukar cup din da ya fadi tare da cewa "oh sorry Hamman mu mantuwa nayi na shigo ba tare da sallama ba"ya dauki cup din yana duban aminatu cikin tausayawa kana ya ce, sorry sis har yanzu bai da na ciwo ba ko? ki yi hakuri ban kula ba ne", daga haka ya fice daga kiching din yana aiyana irin cin uban aminatu da zai yi muddin ba ta daina kokarin tona masa a siri ba.
"Kin gani ko ya kuma baki hakuri",ya fada yana dan dage girarshi guda tare da ɗan matsa yatsan da karfi har sai da ta dan yi karamin ihu tana mai rike tsintsiyar hannunsa da wasu gashi suke a kwance tamkar sun kwanta a ƙorama,dan dakatawa yayi tare da kallon hannun nata da yake rike da nasa,wanda hakan ya sa ta yi saurin janye nata hannun tana dan yar far dashi kamar ta taɓa garwashin wuta,buɗe idanunsa yayi tare da lumshe su a lokaci guda kafin kuma ya mike tsaye da hannunta da ya janyo, babu shiri ta ganta a tsaye, kafin ta fara mitar tayar da Itan da yayi, ya kuma jan hannuta da karfi wanda yasa dole ta fara takawa tana binsa cikin yanayin tafiyarsa me ƙarfi wanda nutsuwa tasa ba a fahimtar karfinta da saurinsa a lokaci guda, sai dai ka gane hakan ta nisan kilomitarsa.
A can bangaren Anne kuwa ta saba kullum da an gama abinci za a kai mata ko mai a hada mata a ƙaramin dinning dinta, amma yau tun tana zuba ido har dai ta zo ta fara ji yunwa shiru kake ji babu abinci babu me kawo abinci, ga shi ita kuma Anne irin dattijann nan ne da girma bai hanasu cin abinci ba, dan kuwa Anne Masha Allah tana yiwa cikinta zubi shi yasa gata nan kullum kamar ana hurata dan irin matan nan ne masu jiki, sosai Anne ta yi fushi har ta sawa ranta yau bazata ci abinci ba idan ya so idan yunwan ta kasheta sa fidda gawarta,dan ma rashin mutunci ita da gidan ɗanta amma ace abincin da zata ci ma ya gagareta,(dan adan me manta baya duk yadda ka kai ga kyautata masa rana daya idan aka samu akasi to fa duk ya manta da wanda ka yi masa a baya),dan haka ta yi shirin kwanciyarta haka duk kuwa da yunwar da ke sakadar yan hanjinta.
Har su Nana suka fito su kayi dinner tare da zaman hirarsu da duk wanda ya samu ,bata shiga kiching taga halin da yake ciki ba. bare ta ga kulolin abincin Anne,ita ma larai Allah bai sa ta lura ba har ta kammala gyaranta ta wanke ko mai ta fice daga kiching din,aminatu kuma tana sane amma ta yi biris dan a cewarta daga rana irin ta yau Anne ta shiga komarta bazata rabu da ita ba har sai randa ta koma ga Allah.
[4/12, 7:00 PM] yushauadamfatima: *Typing*
💕
*MATAR ƊAN BIRNI ** 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
``` *Page31``*
Har misalin ƙarfe ɗaya Anne ta kasa runtsawa saboda yunwa ga kuma bakar zuciya ta ki yiwa kowa magana, har fitowa tayi lokacin basu jima da cin abinci ba ta yi shawagi wai ko Nana zata ganta ta tuna bata kawo mata abinci,ba amma shiru kake ji, dan ita Nana bata ma kawo wannan tunanin a ranta ba sam,aminatu kuwa dauke kai take tana dariya a a fakaice dan sarai ta fahimci shawagin Anne ba akan komai ba ne sai akan adda'am,a ranta cewa take ai tsohuwa tunda kika sake na gane kaunarki da abinci to kuwa kin shiga tara tsohuwar kawai.
Haka ta gama shawaginta ta koma daki tana faman zuba ƙwafa cikinta kuwa banda kugin yunwa babu abinda yake, duban agogo Nana ta yi kafin ta dawo da dubanta kan Khalid dake kwance kan cinyar aminatu, sannan ta ce,"aminatu ku je ku kwanta kunga dare yayi kar ki kasa tashin dare",shafa tattausar sumar khalid aminatu ta yi tana cewa ,nana wane dare kuma?ai dare ya riga ya gama yi shi yasa ba zan kwanta ba sai nayi sallolina dan kar na kasa tashi karfe biyu"mikewa Nana tayi tana cewa "to hakan yayi Nima bari na yi amfani da dabarar ki na fara yin sallar kafin na kwanta"to Nana Allah ya tashe mu lafiya yau tare da Khalid zamu kwanta kwana biyu na yi kewarsa saboda tafiyar da yayi gidan adda suhaima",to shike nan Amin"nana ta fad tana taka matakalar step biyar da zai kaita bangaren dakinta.
Sai da aminatu ta tabbatar da cewa Nana ta yi balance a dakinta, sannan ta kwantar da Khalid a hankali, tashi ta yi ta nufi kiching, tana shiga ta dauki kayan abincin Anne ta fita da shi ta baya ko tsoro ba ta ji ba ta kaiwa security da yake gadin main kofar da zata sadaka da cikin gidan baki daya,tana dawowa ta kwanta a kujera tana ci gaba da kallon tashar aljazira da suke karanta Alkur'ani me girma,a hankali take bi cikin daddan sautinta tana yi tana kallon gefen hanyar dakin Anne, Dan ta tabbatar sai ta fito neman abinci a yadda dai ta fahimci zaryar da take.
Hasashen aminatu ya tabbata dan kuwa Anne ta hango cikin sanda kamar wata ɓarauniya,ta fito daga dakinta,da sauri aminatu ta rufe idonta kamar me bacci,sai dai tana kallon Annen.
Hanyar kiching Anne ta yi cikin sanda kamar ɓarauniya dan yasa a ranta ko da zata ci abincin nan to bata son wani ya sani bare idan ta ce bata ci ba a ƙaryata ko kuma idan ta kwanta jinya,sai da aminatu ta tabbatar da shigar anne kiching ɗin sannan ta yi sauri ta miƙe tare da nufar kiching ɗin,bata bari ta yi takun da Anne zata Ankara da shigar ta ba, shi yasa ganin aminatun ya matukar razana ta dan bayan kunyar da ta ke gudu har da tsananin tsoro, take ta diririce, cikin in ina take cewa,"en dama bera ne na gani nake son neman madoki na bigesa dan kin san Ni fa a rayuwata bana son bera, da na ga bera gwara na ga maciji ina matukar jin tsoron bera, shi yasa idan naji motsinsa bana iya zama a wajen"rike kugu aminatu ta yi kafin cikin son boye dariyarta ta ce,"duk tsoron da kike masa shine kuma zaki iya kasheshi?to ma wai ta ina bera ya shigo gidan nan ne?gaskiya dai anne kin iya zubota sai dai idan da abinda ya kawo ki daban amma ba dai batun bera ba",kallonta anne ta yi cike da tsarguwa da masifa taf baki ta ce,"to dan ubanki me nazo nema? idan ma wani abun na zo nema ai gidan dana ne ba na ubanki ba ko?" Tura baki aminatu ta yi cikin gunguni take cewa "uban aminatu bawan Allah ne dan haka a daina zagar munshi",har Anne zata daga murya sai kuma ta tuna hakan yana nufin fallasa halin da take ciki ne,dan haka ta rufe bakinta tare da barin kiching ɗin a fusace cikinta kuma na karar yunwa fadin rai kuma ya hanata ta tambaya.
A wannan dare dai haka Anne ta kwana da yunwa,ba dan taso ba karshe akan aminatu ta huce duk da cewa bata san cewa ita ce me shiryawa da bada umarni ba,haka ta kwana tana tsinewa aminatu da ahlinta.