← Book details Matar Dan Birni Part 1 Complete Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 46

Sashe 34

Matar Dan Birni Part 1 Complete Novel · about 7 min read

Sai da nana ta tabbatar da innawuro ta shige ɗakinta sannan ta dawo da dubanta kan zahida tare da cewa "dan Allah zahida ki dinga kama girmanki kinga gashi nan ta yi miki rainin da bata yiwa wani a gidan nan ba",zama Abby ya yi cike da tunanin kalaman aminatu na yanzun, gaba daya ta kulle shi ta saka shi cikin sarkakiya, me take nufi da kar su yi mata abinda suke yi me ye abinda suke yi din? Zahida ma wucewa ta yi tana juya kalaman a ranta tare da son fassarasu da gano ma'anarsu amma hakan ya ci tura,Anne ma cikin mitarta da ta ƙi dainawa ta koma dakinta, Nana kuwa tana tsaye akan Abby tana kallon yadda ya lula duniyar tunani duk maganar da take yi masa bai san tana yi ba,da dan sauti me amo ta ta kuma kiran sunansa har da dan buga kujerar da yake zaune akai, firgigit yayi kamar wanda ya farka daga bacci ke nauyi, zuma masa ido Nana tayi cike da tuhuma wanda hakan yasa shi ƴan kame_kamen da ya kuma jefa zuciyar nana cikin zargi,bata ce masa komai ba ta juya ta barsa da kame_kamensa,cike da fargaba da tashin hankalin da aminatu ta haifar masa shima ya koma bangarensa.

Kai tsaye ABM hospital mus ab ya wuce da aminatu, suna zuwa aka karbeta cike da kulawa,bangaren kashi aka kaita take likitoci kusan uku suka hadu akanta dan gyara targaden da ta samu a hannu,ana farawa aminatu ta cika wod din da ihu, idan ta yi salatin sai kuma ta koma jawa zahida Allah ya isa daga karshe dai ta yiwa kanta fada ta hanyar ci gaba da kiran sunan Allah a haka har aka samu aka gama kafa gyaran,amma su kansu likitocin sun ji a jikinsu dan babu wanda aminatu bata ciza ba duk fuskarsu shatin hannun aminatu ne na yakushi,lokacin da suka fito mus ab ya kalle su takaici ya sa shi harararta kafin kuma ya basu hakuri, duk cikinau babu wanda ya damu sai ma dariya da nishaɗin da aminatun ta sakasu duk kuwa da cewa sun ji a jikinsu,daga nan ya kamata suka tafi gida tana ci gaba da rakinta.

Lokacin da suka karasa gidan tuni aminatu ta yi bacci, basu samu kowa a falon ba,ko ina yayi tsit kamar babu wani abu me numfashi a gidan,ko daga can wajen babu motsin kowa sai na securities din da suke on duty da suke ta kai komo tsakanin harabar gidan zuwa wajen gidan,kai tsaye bangarensa ya wuce da ita dan ita ya kwantar da ita yana kallon fuskarta da duk ta ɓaci da da shatin hawayen rigima,samun kansa yayi da dan jan dogon hancinta a saman labbansa yana fadin rigimammiya a ko wane hali take sai take bakinta baya rissina,bayi ya wuce ya haɗa mata ruwa me dumi, kana ya dawo daukarta yayi kamar yadda ya saba ya kaita har cikin bathtub ɗin,ajiyar zuciya ta saki tare da far da idanunta,da sauri ta maida ta kulle ta kuma budewa sai sannan ta yadda da inda take,turbune fuska ta yi kamar zata sa kuka,ɗan yatsansa ya ɗora kan jajayen labbanta yayi mata alamar ta yi shuru,hakan yasa ta haɗiye kukanta sai dai ba ta daina kwaɓe fuskar ba,janye rigarta yake kokarin yi ta yi saurin dafewa tana kallonsa da odnaunta sa suka cika da ƙwalla ga kuma maiƙon cikinsu da yake wani irin sheki hakan yasa kallonnata ya bada wani irin yanayi, wanda ya saukarwa da mus ab wata irin kasala da mutuwar jiki tsigogin jikinsa suka dinga mikewa tare da wani irin sanyi na musamman da ya dinga ratsa duk.wata tsoka da ɓargon jikinsa,lumshe idanunsa yayi yana son saita kansa da kuma tuhumar kansa a kan yanayin da yake shiga a duk sanda ya kasance da aminatu, yanayin da baya jinsa akan ko wace irin mace duk kyanta da ajinta kuwa,aminatu kuwa takaicin kanta da haushin kanta ne ya kamata, saboda tasan cewa abinda take bari yana faruwa tsakaninta da mus ab ba daidai ba ne, to amma ta rasa dalilin da yasa take kasa sarrafa kanta da yaƙar sheɗan a duk sanda kusancinsu ya wuce na alaƙar uban gida da da hadimarsa,ta kan rasa masarrafin a ko wace kafa ta jiki ta da zuciyarta, to me yasa hakan ke faruwa bayan kuma idan wanin mus'ab dinne bata yadda ko yatsanta ya riƙe?saukar tattausan labbansa me wani irjn ƙamshin da bata iya tantance na wani abin ƙamshi ne yasa ta dawo daga duniyar tunanin da ta tafi,buɗe bakin ta yi zata yi tsiwar tata da ta saba, amma hakan bata samu ba sai ma amfani da yayi da wannan damar ya ƙarasa zura gaba ɗayan harshensa cikin bakinta......

Fyadam✍🏾
[4/12, 5:04 PM] yushauadamfatima: *Typing*

💕
*MATAR ƊAN BIRNI ** 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

``` *Page25``*

A dai-dai wannan lokacin ne kuma innawuro a can dakinta ta kasa zaune da tsaye, dan kuwa sosai lamarin gidan ya dameta baran ma mu'amalar boɗɗon ta da MUS'AB, damuwarta ta kai maƙura mafita kawai take nema domin tana ji tana gani ba zata bari a lalata mata rayuwar jika ba,EY lalatawa mana tunda in dai har suna ci gaba da kusantar juna irin haka da mus ab dole wani abu ya faru,ko da kuwa shi mus'ab din bashi da niyar keta mutuncinta ai shi sheɗan yana da kwarin gwiwar sarrafa zuciyoyinsu, wannan tunanin da ta yi yasa ta fita daga dakin zuwa bangaren Nana da tun zamanta a gidan shigar ta ɗaya,tana zuwa ta ƙwanƙwasa ƙofar, jim kaɗan taji muryar Nana na tambayar waye?nice" innawuro ta amsa da muryar damuwa, buɗe kofar Nana tayi tana kallon innawuro da lokaci daya ta karanci damuwar da take ciki, hanya ta bata ta shigo, bayan innawuro ta shigo ta nuna mata kujera da ta zauna,zaman ta yi ba tare da musu ba, itama nanan zama tayi tana fuskantar innawuro da kuma sauraron abinda ya kawota a dai-dai wannan lokaci.

Jin innawuro ta yi shiru tana ƴan kame_kame wanda ke nuni da cewa nauyin maganar da zata yiwa nanan take ji yasa Nana cewa. "karki damu innawuro ki faɗa min damuwarki ki dauke ni matsayin 'yarki da zaki iya faɗawa duk abinda kike son fada", wannan maganar ta nana sosai ta bawa innawuro kwarin gwiwa, hakan yasa innawuro gyara zamanta tana mai fuskantar Nana da dukkan zuciyarta, kana ta fara magana da cewa,ki gafarce ni akan abinda nake son faɗa miki,ki fahimceni fahimta irin ta uwar da ta ke son inganta tarbiyyar ƴarta ta hanyar da ya dace,na kasa barin abin a raina saboda yanzu damun da yake min har ya kai ya hanani runtsawa gashi kuma a matsayin mu na yan aiki wanda aka inganta rayuwarsu ba tare da nuna banbanci ba bani da zarrar yin fito na fito ta hanyar da bata dace ba,shi yasa na dangana na kuma samu kwarin gwiwar fuskantarki ta dalilin halayenki da suke nuni da cewa ke uwa ce ta gari kuma mace me adalci ga wanda yake ƙarƙashinta, numfashi innawuro ta dan ja sannan ta ci gaba da cewa, Nana kin san dai cewa MUS'AB ba muharramin AMINATU ba ne ko? Kuma kin san cewa kusancinsu a addinance harma da al'ada haramunne,to me yasa mun san haka, amma a matsayin mu na iyaye mata wanda tarbiyyar yaranmu suka ta allaka a hannun mu zamu yi saken da zasu lalace ta hanyar basu gudummawarmu?ban yi mamakin yadda duk tarbiya da hankalin mus ab yake yin hakan ba tare da shakka ba, saboda nasan mafi akasarin masu kuɗi ko yan boko basu maida hakan wani babban al'amari ba,ke kanki ina mamakin yadda baki iya tsawatar da shi babu me magana akan hakan sai Anne wadda sam bana jin haushinta akan abinda take yiwa AMINATU",a hankali innawuro ta zamo kasa ta sa gwiwarta akasa tare da hade hannunta biyu idanunta na zubda ƙwalla ta ce",dan Allah ku rufa min asiri idan har ba zaku iya tsawatar da yaronku akan irin rayuwar da yake kokarin nunawa aminatu ba to ku bari mu tafi mu yi nesa da ku, AMINATU amana ce a wajena duk da cewa na kasance kakarta wadda ta haifi ubanta amma hakan bashi yake nuna cewa zan yi sake da amana da kuma tarbiyarta ba".
Chapter 34 · 0% Book details