← Book details Matar Dan Birni Part 1 Complete Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 46

Sashe 39

Matar Dan Birni Part 1 Complete Novel · about 7 min read

Cikin bacci aminatu ta dinga jin numfashin mutum a kusa da ita,kafin ta tantance abinda ke shirin faruwa ta ji an fara shafa jikinta wanda hakan yasa ta zabura tana kiran sunan Allah,kasancewar fitila a kashe hakan ya bawa Alhaji Garba damar bin aminatu yana ƙoƙarin kamata, kuka.tasa tana taresa da fadin waye wannan na shiga uku kashe Ni za kayi? Aminatu bata samu amsa ba take suka fara kokowa da mutumin da har yanzu bata tantance waye ba kuma tunaninta bai harsasho mata cewa daddy zai iya biyota a cikin gidansa ba.ihu ta fara yi sosai da neman ɗauki, jin ta fara ihun da zai sa a jita ne yasa daddy ya fara kokarin guduwa sai dai cikin wani irin al'ajabi suka.ga wutar dakin ta kawo hatta da karar kunnawar sai da duk suka jisa a cikin kunnuwansu,take wannan hasken ya bawa aminatu damar ganin fuskar Alhaji Garba a daidai lokacin da yake ta kokarin ficewa daga dakin ya kasa, tamkar wanda aka riƙesa, EY Shi Kam zai iya cewa rike san a kayi dan sosai yaji an riƙe ƙafafunsa wanda ba a bashi damar fita ba har sai da AMINATU ta ga fuskarsa fes a cikin idanunta,yana fita suka ci karo da Hajiya zubaida tare da azumi kai har da Hajara me zuwan yau,cikin tashin hankali Hajiya zubaida ta taresa tana tambayarsa me ya faru?kafin ya bude bakinsa aminatu ta fito daga dakin da gudu tana kuka da faɗin wayyo kwarto ne ya shigo wallahi kwarto ne fyade zai yi min ya cuce ni ya cuci dan birni",cikin in ina da daddyn ya ce ,"na rasa shi na bisa amma ban gansa ba,ku koma ku kwanta zan je na bincika",azumi ta ce ",garin yaya kwarto zai Iya shigowa ko dai a cikin securities ne?" Hajiya zubaida ta ce,"ko securities ba za su iya shigowa cikin falon nan ba bare dakin aminatu gaskiya abin da mamaki,aminatu ko zaki gane wanda ya shigo Miki a cikin securities din gidannan?"Hajiya zubaida ta juyo tana tabayar aminatu,aminatu ta bude baki zata yi magana daddy ya tare ta cikin kame kame dan ya hanata magana,amma ina aminatun ba zata hanu ba,dan kuwa baki ta bude cikin daga murya ta ce,"hajiya wallahi ni dad......."ke ke Aminatu baki da lafiya kin manta je ki kwanta,"daddy ya katseta cikin tashin hankali goshinsa babu abinda yake sai zubar da zufa kamar wanda aka saka cikin tandun gurasa,da zarar aminatu ta dauko magana sai ya katseta cikin rawar baki da karkarwar jiki,da aminatu taga haka sai abin ya zamar mata abin tsokana dan kuwa cikin kara rudashi ta kuma.daga baki ta ce shine ya sh......caraf ta ji hannun daddy saman fatar bakinta ya rufe mata baki cikin tashin hankali yana cewa ",yanzu haka ma jemage ne baki lura ba",take azumi da Hajara da ta canja sunanta zuwa karema suka kalli juna cike da mamaki dan tuni sun dago jirgin aminatu na son tonawa daddy asiri dan babu kokonto sun fahimci shine kwarton. Hajiya zahida kuwa cike ds fusata ta ce "a'a uban jemage,haba daddyn zahida ya za a yi ka hana yarinya magana kiri kiri bayan ta san wanda ya shigo mata daki",janyewa ya yi daga kusa da aminatu yana cewa "to to to ba jemage ba ne karan gidan busert ne kin san shi da jaraba idan bai samu karya ba yaran mutane yake nema",caraf aminatu ta ce au daddy kai ne karen?"take azumi da karema(Hajara)suka tuntsure da dariya dan kuwa sun kasa jurewa hajara a rayuwarta bata taba tunanin zata iya yin irin wannan dariya ba tare da ta samu aldalci ba, amma sai gashi yau daya da ta zo gidan nan aminatu ta girgiza 'yan hanjinta da dariya, ƙarar ƙugin cikin daddy da ƙarar zawon da ya saki ne yasa gaba daya suka fara karon barin wajen dan kuwa ba zasu iya rike dariyar su ba kuma hakan na iya jawo musu kora ta har abada, Hajiya zubaida kuwa wani mugun kallo ta watsa masa tare da barin wajen tana toshe hancinta da warin zawonsa ya game wajen,aminatu dariya tasa tana nuna jallabiyarsa da ƙafarsa da zawon ya zuraro tana cewa "subhanallah kwarto ya bige da zawo azumi ku kawo dauki",jin ta kira su azumi ai baisan sanda ya taka da wani uban gudu ba, ya fada ɗakinsa cike da borin kunya da mozanta da yayi a gaban ma aikatansa.aminatu kuwa ƙin komawa ɗakinta tayi, sai Hajara tabi zuwa dakinta.

Azumi ita ka dai ta dinga babbaka dariya, ko da ta yi shiru da zarar ta tuna,karkarwar me gidan da batun jemage da kare da zawo sai ta ji ba zata iya jurewa ba, haka a can bangaren aminatu da hajara suma dariyar suka dinga yi karma hajara ta ji labari, dan ita dariya biyu take yi har lokacin bata manta da miyan AMINATU da security yasha ba wannan ne ya ke karawa dariyarta armashi.....
[4/12, 5:30 PM] yushauadamfatima: *Typing*

💕
*MATAR ƊAN BIRNI ** 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

``` Page28``*

Alhaji Garba yana shiga ɗaki kai tsaye bayi ya nufa ya wanke jikinsa, ko wanka bai tsaya yi ba ya fito cikin gaggawa ya dauki waya ya dannawa Abby kira, sai da ya kira sau wajen biyar sannan Abby ya daga bayan ya lallaɓa ya baro dakin da suke tare da Nana,dayan dakin ya shiga tare da rufowa sannan ya fara magana, "haba Garba me ya faru kake min irin wannan kiran cikin dare bayan kasan ina tare da Nana tun da ba mu yi da kai zamu yi waya ba bare na shirya?",cikin azalzala alhaji garba ya tafi kan maganarsa ba tare da ya biyewa tuhumar Abby din ba,"ina fata dai ka bawa innawuro wannan maganin?" Na bata me ya faru?"Abby ya tambaya cike da kaguwa,ba tare da ya bawa Abby amsa ba ya ci gaba da cewa to ya sakamako ya fito?"a takaice Abby ya kuma bashi amsa da cewa ina nan ina jira dai nasan zuwa asuba zata kasa jurewa ta kira nana shi yasa nake tare da nanan",Alhaji Garba ya kuma cewa "to Jamil ka tabbatar da cewa kun fita tare da zahida dan ina mai tabbatar maka da cewa aminatu zata iya dawowa gidan nan cikin ko wane irin lokaci kuma kasan cewa muddin zahida taga aminatu ta dawo gidan nan bazata samu nutsuwar yin aikin nan ba zata iya jawo mana asarar biliyoyin kudaden da muka ci fiye da rabi idan aka ce zamu biya ba ƙaramin jinjga zamu yi ba,dan haka ka yi yadda zaka yi ka tabbatar bata haɗu da aminatu ba", Abby ya ce. "to me kuka yiwa aminatu da har zata iya dawowa gidan nan bayan kuma da amincewarta na kawota?"hannu yasa ya goge zufar da ta ke ta tsatstsafowa a goshinsa kana ya ce."jamilu kasan halin wannan sheɗaniyar yarinyar me kama da aljanu dai ba sai na yi maka karin bayani ba, dan haka kayi abinda na ce maka ka ceci nasararmu daga faduwa,"shike nan ko mai zai tafi daidai gashi can ma naji motsin Nana yanzu haka ciwon innawuron ne ya fito da ita", daga haka suka.kashe wayar Abby kuwa yana fita ya tarar da Nana cikin tashin hankali tana sanar dashi innawuro ce bata da lafiya sosai,wucewa yayi suka nufi dakin innawuro a ransa yana cewa "anzo wajen".

A cikin daren suka fita da innawuro zuwa asibiti,hatta da mus ab bai zauna ba sai da ya bisu,ko a can asibitin shi ya dinga kaiwa yana kawowa dan ganin innawuro ta samu kulawar likitoci,sai da aka kira sallah sannan Abby ya jashi suka tafi masallaci wanda dama wannan damar kawai yake jira saboda hankalin sa ya ɗan tashi ganin mus ab din ya ki matsawa daga dakin da aka kai innawuron.

Lissafin Alhaji Garba yayi daidai, dan kuwa aminatu na idar da Sallah asuba ta dauki abin da ta zo dashi ta fito dan barin gidan,da Hajiya Amina suka ci karo, bata tambayi aminatun dalilin ganinta da haka ba dan tasan dama hakan zata faru,waya kawai ta mikawa aminatun tare da cewa "Nana ce take son magana da ke",cikin sauri aminatu ta karbi wayar lokaci daya tqna sakawa nana kukan taɓara, sai da nanan ta rarrasheta sannan ta snaar da ita cewa suna asibiti innawuro ce tq kwana da ciwon ciki daga karshe da takwantar mata da hankali da cewa amma ta ju sauki har tana magana dan haka aminatun ta taho a nutse.

Tana mikawa Hajiya zubaida wayar ta ja akwatin ta tana shirin fita,kasa dakatar da ita mom zahida ta yi sai kalli da ta bita dashi dan har yanzu shock ɗin da ta shiga jiya bai saketa ba, duk da cewa tasan halin mijin nata,to amma bata yi zaton akuyancin nasa ya kai ya farma yarinya ƙarama marainiya ba.
Chapter 39 · 0% Book details