← Book details Matar Dan Birni Part 1 Complete Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 46

Sashe 42

Matar Dan Birni Part 1 Complete Novel · about 7 min read

Bashi ya saki bakinta ba har sai da suka shiga ɗakinsa ya zaunar da ita saman gadonsa tare da janyo laptop dinsa gabanta ya kunna,aminatu tana so ta yi kuka kuma tana son ganin abinda mus ab yake kokarin yi, dan haka ta dake zuciyarta da take ji tamkar zata faso kirjinta ta fito ta zubawa laptop din ido tana kallon abinda zai bayyana a ciki,ware manyan idanunta tayi cike da mamakin abinda take gani tar saman screen ɗin laptop,bakinta har rawa yake wajen ambatar sunan innawuro kafin wasu zafafan hawaye su sauko mata sai kawai ta rungume laptop ɗin tana wani irin kuka da yake fitowa tare da dariyar farinciki, ajiye laptop din tayi tana kallon innawuro kafin ta buɗe baki ta ce, "innawuro na aka ce an sa ce ki?yanzu kina ina?a ina kike? murmushin dariya innawuro ta yi saboda ganin farincikin aminatunta kafin ta ce ", boɗɗo na ki kwantar da hankalinki ina cikin aminci tare da mutane masu karamci, amma hakan bata samu ba sai da taimakon wata mata da ta ce sunanta Hajara tare da mus abu wanda shine yayi komai, amma ba zaki fahimci ko mai ba a yanzu sai nan gaba, kuma muma har yanzu bamu fahimta ba sai nan gaban idan bincike ya tabbatar, aminatu gaba dayan mu nan muna cikin duhu saboda matar har muka rabu da ita bata bayyana mana komai game da dalilinta na bada gudummawa wajen sace Ni ba",dafe kirji aminatu ta yi tana cewa , innawuro da gaske dai sace kin aka yi ko?"jinjina kai innawuro ta yi kana ta ce,a wajen wasu sata ce amma a wajen mu taimako ne kamar yadda ta fada mana kuma ta ce in dai har muna son sanin gaskiyar abinda yake faruwa to kar na bayyana a idanun duniya,kema saboda kina da hakkin sani ne bana so kuma hankalinki ya tashi shi yasa muka sanar da ke,ita ta shirya abin amma mus ab shi ya gabatar da shirin,gashi nan a gabanki amma bana so ki tambaye shi dan shima a duhun yake lokaci ne zai nuna komai,"to innawuro tunda dai kina nan lafiya alhamdl da zan ga wannan matar da na rungumeta na mata godiya,amma dan Allah innawuro shi na rungumesa runguma daya da sumbata ɗaya ta nuna godiyata innawuro na Miki alkawari ba zan wuce haka ba",kasa magana innawuro ta yi saboda kunya sai kawai ta rufe laptop din gabanta tana yiwa boddonta addu'ar shiriya.

Aminatu kuwa bata saurari amincewar innawuro ba dan bata ma san ta rufe laptop din ba, saboda tana gama magana ta rungume mus ab tare da Kai bakinta saitin nasa ta sumbaci labbansa tana shirin dauke bakinta taji ya sa hannunsa gaba daya biyun ya tallafi bayanta tare da manne ƙirjinsa da nata bata yi aune ba taji tattausan harshensa yana ratsa ko wace kusfa da kofa da loko da ke cikin bakinta, shan bakinta yake tamkar ya samu alewar lollipop, hankalinsa kwance, runtse idanunta ta yi tana dan mutsu_mutsu da jikinta dan son kwacewa, idanunsa a lumshe ya dan dauke bakinsa da ga kan nata kana cikin wata irin murya me ratsa kashi da jijiya yace,"tunda kika fara sai kin ƙarasa,da kin sani ma baki yiwa innawuro alkawarin cewa daga haka babu kari ba",daga haka ya birkitata zuwa kan gadon tare da kwanciya saman cikinta ya ɗan sakar mata nauyinsa kadan yana kallon cikin idanun ta da take ta ƙif_kifta su kamar munafuka,jin nauyinsa yasa ta ɗan yi kara tare da tura ƙaramin bakinta tana cewa "wannan fa iskanci ne ka daina babu kyau Allah yayi....bata samu karasawa ba saboda ruf ya rufe bakinta da nasa ya ci gaba da bata wani irin fashionally Kisess masu taɓa zuciya da war gaza tunanin lafiyayyar mace,juya ta kawai yake yana shanye miyan bakinta,sai dai bai yarda ya taba ko inan ta ba dan ba wannan ne a ransa ba duk da cewa ba ƙaramin juriya yake yi ba, yana jin wani irin feelings akan aminatu me ƙarfi sai dai hakan ba shi yake nuna zai so kansa ya tauyeta ba, dan ya yiwa kansa alkwarin cewa idan komai ya kammala zai bawa aminatu yancinta na zabar mijin da take so,shi yasa duk abinda zai yi yake kokarin kawo adalci cikin lamarin, wannan din ma wasu lokuta da dama baya sanin hakan tana faruwa,some times yana kasa riƙe kansa ne da fita hayyacin da har take kaishi ga aikata hakan.

Aminatu dai bata san lokacin da bacci ya dauke ta ba,mus ab ya jima a zaune yana kallon fuskar aminatu tare da tuna batun mata me suna Hajara.

Abinda ya faru bayan gama wayarsa da Abby akan yazo ga aminatu ta hana a shiga da innawuro dakin tiyata,sai kawai yaga mata a gabansa ba kuma tare da ta ce masa komai ba ta mika masa wata doguwar takarda ta bar wajen,buɗe takardar yayi yana karantawa cike da daurewar kai,idan kana son farincikin aminatu to tabbas sai ka kubutar da kakarta daga shirin barin duniya idan kana bukatar taimakona ka kira Ni a wannan layin, kar kuma ka yi min ko wace irin tambaya saboda ba zan sanar da kai komai ba, dan kuwa babu yardar farad daya tsakanina da duk wani kwayar halitta a cikin duniyar nan,yana gama karantawa ya dago kansa yana laluben inda matar ta yi sai dai kuma bat babu ita babu dalilinta,har zai share batun sai kuma yaji ya kasa yin hakan baran ma da ya haɗa da ta riyo lafuzan aminatu na baya da na yanzu,to idan haka ne kenan akwai kamshin gaskiya akan zargin da mutane suke yiwa wannan asibitin? sannan kuma hakan na nufin aminatu ta san wani abu akan wannan asibitin tunda har take gudunsa,dole fa sai nabi maganar wannan baiwar Allah sannan duk zan samu amshoshina daga baya. ya bawa kansa amsa yana mai yaga takardar kuci kuci,kafin ya shiga inda su Aminatu suke sai da ya fara kiran daya daga cikin likitocin da zasu yiwa innawuro aiki me suna Dr halima,kudi kawai ya cikata da shi ta amince zata fito masa da innawuro,cike da yakinin cewa Allah zai kubutar da me gaskiya ya shiga wajen aminatu yana rarrashi,ya bar Dr halima da matar me suna Hajara, Dr halima ita ce ta shigar da Hajara ta wata kofa da ba kowa ne ya san da ita ba idan ba isu isu amintattun likitocin ba,ko su fa basu san cewa duk wata zuciya ko koda da ake cirewa ba ana cireta ne dan lalura ko dasheba, saboda lokuta da dama ana kawo matacciyar zuciya ko kodar da bata da amfani a ce dashe za a yi wa mara lafiya, dan haka suma duk a duhu suke amfani kawai ake dasu dan su masu sanin basu wuce mutum biyu ba.

Dan haka da wannan damar Dr halima da Hajara suka samu suka fidda innawuro, wajen fita da ita daga asibitin ma mus ab Shi ya kwatanta musu hanyar da zasu fita ba tare da securities sun gansu ba,hanyar da ko ita hakima bata sani ba,hara na fita ta samu motar da mus ab ya aiko suka shiga suka bar asibitin ba tare da kowa ya kula dasu ba bare a yi zarginsu,halima kuma dama bata fita ba bare yan uwansa su yi zarginta dan suna tare take aiwatar da shirinta cikin taka tsantsan.

Koda suka kai innawuro gidan da mus'ab ya bawa driver umarni Hajara bata shiga ba, fita ta yi ta koma gidan Alhaji Garba saboda kar ta bashi kofar da tunaninsa zai juyo kanta.wannan shine dalilin kubutar innawuro daga hannun su Abby.

Numfashi yaja me huci tare da kwanciya kusa da ita yana fuskantarta idanunsa akan fuskarta,zuciyarsa cike da bincike da zargin da ya fara darsuwa akan asibitin iyayen nasa wanda a halin yanzu yake hatta da mahaifinsa ba zai tsira daga binciken da zai fara dan nemo gaskiya ba,duk da cewa yana kan binciken nemo mutanen can na baffan AMINATU to amma hakan ba zai hanasa haɗawa da binciken asibitinnasu ba,don shima abu me me matukar muhimmanci.
[4/12, 6:23 PM] yushauadamfatima: *Typing*

💕
*MATAR ƊAN BIRNI ** 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

``` *Page30``*

A can bangaren zahida kuwa itama can gidan gonar ta su ta bisu kamar yadda suka bukaci da tazo,idan na ce muku tashin hankali to na rage muku armashin tashin hankalin da su Abby ɗin suke ciki, domin kuwa har Mr alfa ya fara danno musu kira jin su shiru babu su babu sako babu dan aike,daga karshe dai su ɗan turƙyi suka sa ya nemo musu wadda zasu yi amfani da ita a matsayin innawuro,basu bar gidan gonar ba har sai da dan turkyi ya tabbatar musu da cewa aiki ya kammala dan a halin yanzu matar tana cikin asibitin tana jiran zuwan dr Zahida,hakan yasa kai tsaye Zahida ta koma asibiti su kuma kowa ya nufi gida da fatan kar ta kuma kwaɓe musu kwabar da tunda suka fara kasuwancinsu ba su taba yin makamanciyarta ba.
Chapter 42 · 0% Book details