Sashe 36
Matar Dan Birni Part 1 Complete Novel · about 8 min read
Innawuro kuwa nasiha ta yiwa aminatu akan a ta ajiye wannan sakarcinnata dan kar ta dauko rigimar da zata sa a kulle so ko a koresu da ga gidan,dan ba kowa ne Zidane zasu iya hakurin da su Nana suke da ita aminatun ba,da haka suka rabu ba tare da aminatu ta wani nuna mata taji nasihartar ta ba.
Aminatu na so ta yiwa nana da Khalid da Shi kadai take jin kewarsa sallama amma Abby ya hana, haka ya tasata gaba suka fice daga gidan.....
Fyadam✍🏾
8064537048
Fatima yushau adam opay
[4/12, 5:04 PM] yushauadamfatima: *Typing*
💕
*MATAR ƊAN BIRNI ** 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
``` *Page26``*
Har motarsu ta fice daga gidan mus'ab da yake ta can saman barendarsa idanunsa yana kansu,wani zazzafan huci ya fesar yana mai ƙara buɗe idanunsa da kuma lumshesu a lokaci guda, ba zai iya cewa ga yanayin da yake ciki ba shi kansa bare kuma wani ya fahimta, komai nasa a nutse yake dan haka babu me gane ainahinsa ta ciki da waje,motsin da ya ji ne yasa shi buɗe idanunsa da suke a lumshe, Nana ce a tsaye bakin ƙofar tana yi masa kallon jin ƙai da tausayi, ba dan ko mai ba sai dan tasan ɗanta ba mai son hayaniya da magana ba ne, shi komai ma in dai har akan yayi doguwar magana ne to gara ya haƙura dashi, tasan cewa yana da abin cewa akan tafiyar aminatu amma tsananin miskilanci ba zai barsa ba, ya gwammace ya rabu da Abbyn na shi yayi duk yadda yake so da abinda yake ikonsa, duk da tasan cewa har da biyayyar da kuma yasan cewa abinda Abby ya faɗa gaskiya ne na cewa koda ikonsa ce amimatu shi kuma shi yake iko da me iko da AMINATU dan haka dukansu ikonsa ne,a hankali ta karasa tare da dafa kwantacciyar sumarsa baka siɗik, kana ta fara magana cikin kwantar da murya da cewa,"mus ab na san cewa ba da son ranka haka ta faru ba kuma dole idan muka tsananta da son dakatar da shi, sai fa idan mun fada masa matsayin aminatu a wajensa wanda kuma hakan ba mai yiwuwa ba ne a yanzu,ko ba dan ko ba dan waccan binciken naka ba dole mu rufe maganar saboda zahida,dan kuwa muddin zahida tasan matdayin aminati a wajenka zata iya aikata komai akan aminatu,amma kayi hakuri na san aminatu ba zata dore a gidan nan ba muna zaune zaka ganta da sawayenta ta dawo",ta karasa maganar da ɗan bubbuga kafaɗarsa,a hankali ya bude idanunsa da suka dan sauya launi akan nana kana cikin taushin muryar da tsintsinka kalmomin ya ce,"kar ki damu Nana bani da damuwa da hakan ko mai lafiya daga gareni", murmushi ta yi ba tare da ta kuma cewa komai ba ta fita daga barendar.shima ta shi yayi ya koma can wani kebantaccen ɗakinsa da yake gudanar da ayyukansa na sirri dan yana da wata shari'a da zai gudanar abcikin kwanakin wanda hakanne yasa a kwanakin bashi da lokacin kansa.
Gidan sak irin na Abby Dan haka aminatu ba ta damu da kalle gidan ba kamar yadda ta saba bawa idanunta abinci akan duk abinda yake sabo a wajenta,yadda securities suke zagaye da gidan Abby haka nan ma suke ta faman sunturi tamkar sojan da suke fareti,kai tsaye suka shiga falon gidan wanda ba da ban canjin launin kayan falon da kujerun dakin ba da tabbas cewa zata yi a gidan su ƊAN BIRNI take, daddyn zahida da Shi da macen da take tdamannin mahaifiyar zahida ce suna zaune a falon kujera ɗaya, kallo daya zaka.yi mata kasanbcewa wayayyiyar macece ta nunawa sa a ko daga yanayin zaman da su kayi zaka tabbatar da hakan,hannu su kayi da shi da Abby suna gaisawa amma idanunsa suna kan aminatu tamkar zai cinyeta ɗanya, "ko kunya baya ji tsohon banza" aminatu ta faɗa cikin mulmula bakinta,matar da ta ji Abby ya kirata da hajiya zubaida ce ta kamo hannunta tana cewa,"zo ki zauna ɗiyata ai ni ba 'yar tayin zama kuka kawo min ba ɗiya kukawo min, aminatu saki jikinki ki dauka nan ma gida ne kin ji",aminatu dai binsu da kallo kawai take yi amma ko ihum bata ce ba bare su sa ran zata gaidasu,to su ɗin ma basu damu da gaisuwarta ba abinda ya damesu shine a gabansu,
Bayan ɗan tattaunawa na wasu mintinan da basu gaza ashirin ba, Abby ya yi musu sallama ya tafi yana mai haddadawa aminatu ta saki jikinta na zuwa lokacin da zata koma can gidan,shima bata tanka masa ba dan gaba daya cike take da kallon iskancin da daddy yake yi mata, Abby Yana tafiya ta mike zunbur tana me tura ɗan karamin bakinta kana ta dubi Hajiya zubaida ta ce,",yunwa nake ji",dariya dadyn zahida yayi yana cewa to hajiya aiki fa ya sameki dan ɗiyar taki bata wasa da cikinta"ƙwafa aminatu ta yi a ranta tana cewa ba dai kasa an kawo ni gidanka ba ai.ka shiga uku da kai da wanda babu tsakinsa ma dan wallahi sai na gallabeku sai na hanaku baccin kirki daga kai har watsatsiyar matar taka kafin na koma.
Me aikinta me suna azumi hajiya zubaida ta kwalawa kira,cikin minti ɗaya sai ga azumi ta zube gaban Hajiya zubaida tana cewa "gani ranki shi daɗe"kallon AMINATU ta yi tare da cewa me zaki ci baby?",kut kaji wani iskanci gandamemiyar budurwa dani za a cewa baby,aradun Allah baby na bayan uwarta",azumi bata san lokacin da ta ɗago kanta ba saboda tsananin mamakin ƙarfin halin wannan yarinya,ita ma Hajiya zubaida kasa motsi ta yi da jin wannan katobarar ta Aminatu me kama da zagi zagi,shi kuwa oga Alhaji bai shiga wani shock ba saboda yasan kadan daga cikin halin aminatu fiye da wannan ma zata iya faɗa,kuma hakan ba damuwarsa ba ne in dai har zai samu biyan buƙatarsa,azumi ce ta kasa jurewa ta ce,"ke kuwa ɗiyata wannan kalaman naki ai daidai suke da zagi ko ba komai ai sun haifeki",Ni ki bani abinci yunwa nake ji",aminatu ta faɗa ba tare da ta bi ta kan maganar azumi ba bare ta nuna cewa ta damu da abinda ta faa din,Hajiya zubaida ta maida dubanta kan azumi tare da cewa tashi ki kawo mata abinci kar ki damu kuruciya ce bata san manufar abinda ta faɗa ba", Alhaji Garba ya ce to zauna zata kawo miki abincin,zaman ta yi ba tare da ta tanka ba,ba a dau dogon lokaci ba azumi ta kawo mata abijcine rai da motsi, nan ta zauna ta vi ta koshi ta ruwa da lemo daga nan hajiya zubaida da kanta ta kaita dakin da alhaji garba ya ce a kaita,duk da cewa dakin yayi kusa da nata da nasa amma bata kawo ko kai a ranta ba sai manl daɗi da hakan yayi mata.
A can gidan su mus ab kuwa, lokaci ɗaya kewaye aminatu ta fara tasiri a wajensu baran ma Khalid da bai san cewa aminatu ta yi nisa ba ne, duk shigar da zai yi sai ya tambayi Nana ko larai ina aminatu,daga karshe dai nana ta fada masa gaskiya aminatu sai ta yi kwanaki zata dawo,aiko kuka Khalid yasa rarrashi duniya yaki yin shiru, daidai lokacin kuma Abby suka dawo dashi da isma da ya biya ya dauko daga filin jirgi,to dawowar isma ce ta kwnatar da rigimar Khalid tunda dama isma mutuminsa.
A daddafe dai yau aminatu ta kwana uku a gidan su zahida ba tare da wata matsala ba, sai dai ita da ta kasa sabawa, gashi duk abinda tasan zai bata musu rai shi take yi, amma mutanen kamar mayu basu nuna wata damuwa saima tarayrayarta da suke kuma yi,ita fa aminatu ji take kamar ana saka mata shakkun akan wadannan mutane,ji take kamar ana nuna mata su da wasu abubuwa da suka dangance su a cikin duhu,bata san me yasa ake cusa mata al'amarin waɗannan mutanen cikin tunaninta da ranta ba? sam bata yarda dasu ba hatta da mom zahidar bata yadda da ita ba, haka nan take ji dole akwai wani abu da suke buƙata a gunta, sosai ake nuna mata cewa ta bibiye su wanda ta kasa fahimtar daga ina take jin hakan kuma me yasa take jin hakan?
Yau da ta samu kwana hudu cif a gidan ta farka da wata irin kewar su Nana Khalid da innawuro kai harda Anne abokiyar faɗanta,da dukan mutanen gidan,sai dai a tan gefe guda akwai wanda take ji kewarsa ce ta lulluɓe ta kowa kuma da za ace zata gansa da bazata damu da kewar su ba,so take ta ya kicesa ta manta dashi amma tana ji kamar wannan kewar da take ji ta sa ce,tura bakinta ta yi tamkar yana kallonta kana ta ce,"me zai sai na yi kewarsa? mutum bayan iskanci babu abinda ya iya, Ni kewar su nana kawai nake da innawuro na",a tunaninta maganar da ta yi zata iya sawa ta ji tabbacin hakan a ranta amma sai ta ji tamkar tsokano ciwo ta yi,hakan yasa ta zura tattausan silifas tare da yana mayafin bayar da yake kanta ta fice daga daga dakin,harabar gidan ta fito sai taga nan ma kamar yayi mata kadan hakan yasa kai tsaye ta yi mikakkiyar tafiya har zuwa gate ɗin gidan.