← Book details Matar Dan Birni Part 1 Complete Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 46

Sashe 41

Matar Dan Birni Part 1 Complete Novel · about 7 min read

💕
*MATAR ƊAN BIRNI ** 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

``` *Page29``*

Turus su kayi gaba dayansu suna kallon gadon wayam,babu innawuro babu alamunta,cikin daga murya da hargowa zahida ta ke tambayar likitocin da suke kula da innawuro,"me ye hakan tayaya duk kuna dakin za a sace mutum guda ba tare da kun sani ba?"cikin in ina nas halima ta ce", wallahi Dr bamu san komai ba, saboda nas ahlam ne ya shigo ya ce in jiki kin ce ya maida ita dayan dakin me kallon wannan,shine mu ka bari yaja gadon ya fita har da ce mana mu tsaya mu haɗo kayan aikin sai mu biyosa,to a garin tsayuwar ne har haka ta faru ba tare da mun Ankara ba sai daga baya ne ma muka fuskanci cewa ba nas ahlam din ba ne ya shigo yaudararsa aka yi aka sumar dashi aka yi amfani da kayansa dan ancimma a manufa",wata irin zufa ce ta shiga ketowa Abby da ya kasa cewa komai bayan zare idanunsa da yake zuwa loko da saƙon ɗakin kamar zai ga innawuro anan,cikin tsawa da hargowar da ke nuna tsananin tashin hankali zahida ta ce "ina nas ahlam din yake?"Dr yana cikin dakin canja kaya a sume",cewar dr salomon da ya fi kowa tsorota dan shi gani yake yi aljanu ne kawai suka yi wannan aikin ba mutum ba, domin kuwa lissafin ya kai lissafi,tabbas wanda yayi wannan aikin ba ƙaramin me lissafi da wayo ba ne",

Da gudu Zahida ta da Abby tare da sauran nas din suka fice zuwa ɗakin canjin kaya, a ƙasan ɗakin suka samu nas ahlam kwance daga shi sai gajeren wando wanda hakan ya kuma tabbatarwa da Zahida da Abby cewa amfani a kayi da kayansa na aikin tiyata aka ɗauki innawuro,Dr zahida ce ta durƙusa a gabansa tasa hannunta a kofofin hancinsa sannan ta dago kanta tana kallon ragowar likitocin kafin ta ce "ku ɗaukesa zuwa emagency ku tabbatar da cewa ya farfaɗo cikin mintinan da basu gaza talatin ba"Sannan ta maida kallonta kan securities da likitocin da suke dakin, kafin cikin kaushin muryar da take nuna tsantsar gargaɗi ta ce ", daga iya mu dun nan bama bukatar kowa ya san wannan bangare idan ma wani yaji to a tabbatar an toshe maganar ta tdaya iya nan,domin kuwa fitar wannan maganar daidai take da rusa wannan asibitin, kun san dai cewa mutane suna jiran kiris ne akanmu dan haka mu bar maganar ,mu kuma zamu yi duk abinda ya dace dan ganin mun binciko wanda yayi wannan aikin,cikin ruwa fun asiri ba tare da kowa ya ji ya gani ba,muddin na samu maganar nan ta fita to wallahi dukkanku nan baku tsira daga karbar mummunan hukucin mu ba",daga karshe ta nuna musu hanya tare da ceqa kuje ku yi abinda na umarce ku", gaba daya fita suka yi daga dakin suka bar zahidan da Abby da yake ji tamkar zai yi hauka.

Suna fita Abby ya zabura yana cewa Zahida ya zamu yi me ye abinyi ta ina zamu fara?"ɗan jim Zahida ta yi kafin ta kalli Abby ɗin da lokaci daya duk ya wani firgice,kana ta ce"Abby yanzu Bama da wani abinyi baya ga mu nemo wata zuciyar da tayi daidai da waccan mu yi aiki kanta idan ba haka ba muna cikin matsala kun dai fini sanin halin Mr alfa Romeo bashi da daga kafa akan harkar kudi komai kankantarta, in yaso idan muka gaba da matsalarsa sai mu fara binciken wannan shu umin me aiki tamkad da jinnun, tabbas Abby wannan kwamushen yana da alaƙa da wanda yasan sirrinmu ko kuma yake zarginmu",jinjina kai Abby yayi kafin ya ɗan dafe kansa na sakanni can kuma ya ɗan zaburo tare da cewa",anya kywa babu sa hannun AMINATU?"girgiza kai zahida ta yi kafin ta ce, "a'a Abby aminatu ba zata iya ba, ka manta aminatu ko zuwa asibitin nan ba ta yi ba kai bana tunanin ma tasan ankwao innawuro nan kaga kenan babu ita a cikin zarginmu ",ey haka ne fa amma duk da haka ba zamu kasa bincikarta ba kin san yarinyar nan tamkar aljana take komai aka ce miki zata yi kar ki musa", Abby muje kar shurun mu ya kuma dasa zargin da mitane zasu yi mana binciken kwakwaf akan wannan al'amarin".

Fita su kayi daga dakin suna mai tunanin ta yadda zasu fuskanci aminatu Nana Mus ab da wannan maganar me girma wadda tafi ace mutuwa suka bayyana.

Da sauri Nana ta ƙaraso gaban Abby idanunta cike da ƙwalla tana cewa,me yake faruwa shin da haskene an rasa innawuro?"jan hannunta Abby yayi amma sai ta dinga kokarin fincikewa tana ci gaba da yi masa tambayoyin da wasu ma bata san tana yin su ba, a haka ya saka ta amota ya figi motar suka bar harabar asibitin.

Abin ya faru akan idanun wasu tsirarun mutane, to amma lokaci ɗaya maganar ta mutu saboda yadda aka nuna cewa innawuro bayi ta shiga ta faɗi a ciki bayi bayan farfadowarta saboda ba ayi mata allurar bacci ba,da wannan maganar suka samu suka rufe batun ɓatan innawuro.

Suna zuwa gidan ya kashe motar ya zagayo da kansa ya kuma buɗe mata tare da kamo hannunta suka wuce cikin gidan, ba tare da ya kula da ƴan ƙananun kukan da ta ci gaba da yi ba,sai da ya kaita har dakinta sannan ya fita zuwa Masallaci bayan ya bawa larai umarnin kula da ita,

Yana fita itama mikewa tayi ta shiga bayi ta dauro alwala tazo ta tada sallah,sai da ta fara yin nafila kafin ta maida farilla, ko da ta idar ta jima a zaune tana karatun Alkur'ani idanunta a lumshe baka jin ko mai sai sassanyan Muryarta da take tashi cikin kamewa da fitar da haruffa tare da tajwidi,a hankali ta dinga jin zuciyarta na sanyaya duk wani datti na korewa,ba ita ta dakata ba har sai da taji shigowarsa dakin kana ta shafa tare da mikeqa tana dan kallonsa kasa kasa.

Cikin dakakkiyar muryasa ta ji yana cewa "innawuro tana lafiya,yaushe zaki koma wancan gidan?"girgiza kanta tayi tare da cewa "a'a Ni ba zan koma ba na dawo gida kusa da innawuro na",me yasa ai na ga ke kika ce za ki je ba wani ya miki dole ba",tura ƙaramin bakinta tayi tana kokarin fita daga dakin ta ce,"to yanzu kuma na canja ra ayi ina nan"daga haka ta fice daga dakin tana mitar sa a ranta,shima fita yayi har zai haye upstairs sai kuma ya dakata tare da canja hanya zuwa falon saboda jiyo muryar nana da yayi.zuba mata ido yayi saboda yanayin da ya ganta a ciki, aminatu na gefenta tana ta zuba mata tambayar yaya jikin innawuro ta farfaɗo? me yasa basu dawo da ita gida ba?"amma Nana ta kasa amsa mata ko tambaya daya,shima mus ab din kasa haɗa ido ta yi da shi saboda ta fahimci irin tambayar AMINATU yake mata ta yanayin kallon da yake mata,da kyar ta iya bude baki ta ce"tana nan lafiya bari na je na yi sallar zuhur na dan huta kafin mu koma hospital ɗin",, daga haka ta zame hannun ta daga na aminatu ta wuce zuwa bangarenta,shi kuwa da ma Abby yana ajiyeta juyawa yayi yabar gidan dan bai ga zama ba a cikin irin wannan lokaci,yana tafe yana kiran su Alhaji Garba akan su haɗu a can gidan gonarsu.

Ganin yadda jikin Nana yake a sanyaye yasa aminatu ta yi kwaƙwal da idanunta zata yi kuka,kama hannunta mus ab yayi yaja ta suka bi bayan Nanan, saidai suna.gab da shiga dakin suka ji yo Muryarta cikin kuka tana waya da suhaima tana sanar da ita halin da suke ciki na batan innawuro,wani irin bugawa zuciyar aminatu ta yi,har mus ab na jin bugun zuciyar saboda kusancin da suka yi,baki ta bude zata yi magana yayi saurin tarar numfashinta ta hanyar sa hannunsa ya rufe bakinnata tare da janta suka koma da baya,kuka take son yi da magana amma ya hanata wannan damar.
Chapter 41 · 0% Book details