← Book details Matar Dan Birni Part 1 Complete Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 46

Sashe 38

Matar Dan Birni Part 1 Complete Novel · about 7 min read

Wannan dalilin ne yasa suke girmamata da sanyatq a cikin matan da suka yi da ce, dan haka zahida take tsula tsiyarta a cikinsu, ga shi babu wadda ta isa ta yi mata hirar mus ab KO da ambatar sunansa ne,to kuwa yanzu zata fita hayyacinta ta yi ta faɗe faɗe marasa kan gado da maganganun da suke nuni da kamar tana musu izgili, haka rayuwar zahida take sam bata yin abu ta fuskar addini tunda bata dashi ɗan wanda take dashi kuma tuni ta yi watsi dashi,a halin yanzu jinta take bata da wata damuwa tunda an kawar da damuwarta daga inda take kuma bata jin mus ab zai taba zuwa inda aminatu take ko da a mafarki ne kuwa,dan shekarun da ta yi da aminatu jinta take duk a daure zuciyarta a kuntace take da zafin kishi da wutar bala in tsanar aminatu da hassadarta da take hanata sukuni cikin rayuwarta, ko a can asibitinsu ji suke yi inama ta koma zahidar baya me cike da damuwar da idan tazo asibitin bayan aiki babu abinda take iya taɓukawa bare har ta samu damar cin kashin na ƙasanta.

Cike da takunta na ƙasaita take kokarin shiga bangaren mus ab,sai hura hanci take jinta take tamkar wata sarauniya a duk sa ilin da ta tuna ita din wacece da kuma matsayinta da take amsawa na babbar likitar mata da kuma ɓangaren fiɗa da babu kamarta acikin jaharsu,gata yar me kudi ita me kudi mijinta me kudi surukinta me kuɗi,wani irin murmushi ne ya kufce saman fuskarta lokacin da ta hango gwarzan maza mus ab Jamil zaune ƙasan tattausan cafet din da yayiwa falon ƙawanya,sai da ta dan yi jim tana kallon kyawu da tsarinsa da ko a wane hali yake sai ka gansa cikin wannan yanayin na nutsuwa da kamewa irin ta mutanen da suka san kansu, wanda ilimin addini da na zamani suka cika kansu da rayuwarsu ma ana irin mutanen da suke amfani da ilimin su acikin zamantakewar rayuwarsu, yaji a jikinsa ana kallonsa yanayin kamshin turarenta da ya ɗan hautsine da nasa da ya kama komai nasa yasa shi fahimtar ita ɗince,bai dago ba bai kuma motsa ba yana nan cikin zamansa na kalmashe ƙafa daya karkashin dayar da take a miƙe laptop ɗinsa a gabansa, ga dukkan alamu dai aikin da yake yana da dan muhimmancin da yake bukatar nutsuwa.

Wannan halin na mus ab shine babban kalubalenta acikin rayuwar aurensu,dan zahida bata son Shariya da wulakaci, Shi kuma mus ab wannan ce babbar ɗabi arsa a ganinta shima girman kai ne da shi da ɗagawa saboda yana ganin yana da duk qualities ɗin da ya kamata a ce yayi hakan,ita a kan kanta tana jin da ita ce da baiwar da yake da ita da sai ta yi fiye da haka,to amma ai ita matarsa ce a ganinta ita ce ta cancanta ya saukarwa da kai ba wasu ba,don idan tayi duba ta wani ɓangaren sai taga cewa kamar ma ya fi mata wannan wulakancin akan jama ar da suke tare da shi, wanda ako da yaushe bata jin suna kusheshi kamar yadda ake kushe nata halin da yi mata Allah wadai,to amma ta danganta wannan da kwadayin mutane, suna yabonsa ne kawai dan kyautatawar da yake musu da rashin ƙyamar da yake nuna musu,ita ko wannan bai dameta ba in dai har sai ta basu ne ko kuma ta kulasu ne zasu yabeta to su bar yabonsu bata bukata.

Da wannan tunanin ta daure ta ƙaraso inda yake, zama tayi tana ci gaba da kallonsa kamar zata haɗiyesa dan so, amma idan ta sake ta nuna masa shike nan ta kashe kanta, a hakan ma ya ta cika da wulakancinsa bare ta sakar masa jiki da zuciyarta,yatsina fuska ta yi kafin ta ce, "mus'ab kana ji na fa amma babu wani reaction a tare da Kai da zai nuna cewa kasan nazo", sai da ta fidda ran tankawarsa. kana kuma kamar ana matsa shi dole ta tsinkayi dakakkiyar muryasa can ƙasan maƙoshi yana cewa, "taya zan tanka Miki zahida?bayan baki cika sharaɗin musulunci ba,da kika zo kin yi sallama ne?"ya tambayeta tare da ɗagowa yana watsa mata rikitattun idanunsa da take matuƙar shakkar kallarsu a duk lokacin da tasan ta yi masa ba daidai ba,kawar da fuskarta ta yi, cikin takaici ta ce", to Ni da dakin mijina har sai nayi wata sallama zan shigo?kai babu dama a zauna zaman mutunci na mintuna da kai ba tare da ka kawo batun musulunci ya ce addini ya ce Allah ya ce annabi ya ce an rawaito daga abu kaza ba,haba dan Allah mus ab ni fa matarka ce, yanzu ba zaka iya bani lokacinka ka tarairayeni ka lallaɓa Ni ba sai dai kullum faɗa dan dai Ni ce na kawo rashin daidai duniya",cikin motsa laɓansa ya karanci auziya dan jin kalamanta yake tamkar saɓo saboda rashin dadinsu, daga haka ya tattare komai nasa ya tashi ya barta a wajen sake da baki da ta kaicinsa,ƙwafa ta yi tare da ficewa daga falon a fusace.

Alhaji Kabir Alhaji Garba Alhaji Jamil,zaune a gidan gonarsu in da suka haɗu dan tattauna batun innawuro, wani ruwan magani a cikin kwalba daddy zahida ya miƙawa Abby tare da cewa, karɓi wannan shi za a zuba mata cikin ruwan da zata sha, Dr Shazam ya ce bashi da banbanci da ruwa dan haka babu wanda zai gane an sa wani abu a cikin ruwan shanta,wannan maganin shi zai tayar mata da ciwon cikin da dole sai an dangana ga asibiti,kuma dai kun san cewa tunda yar balaja'un ta ta bata kusa da ita dole GJK za a kaita,shike nan daga nan aiki ya kammala dan mu din masu nasara ne ako da yaushe shi yasa bama kawo rashin nasara cikin lissafinmu",ya kammala maganar da sakin wani shu'umin murmushi.

Su ɗin ma dariya su kayi,yayinda da Abby yake juya ruwan maganin a hannunsa zuciyarsa fes, saboda nasarar da suke hawa mataki mataki ba tare da ta taɓa kwaɓe musu ba,to ko da ta kwaɓe ɗin ma nasararsu ce take sawa su yi saurin Ankara su yi maganin matsalar, Alhaji Garba ya dube su daya bayan daya fuskarsa cike da annashuwa kana ya ce,"na samo mana wani sabon kasuwancin",gaba daya suka zuba masa ido suna jiran karashen zancan,muskutawa ya ɗan yi sannan ya basu labarin sabuwar me aikin da suka samu har gida tare matsalarta,dariya suka.sheke da ita Alhaji Kabir cikin nuna daddyn zahida da hannu yake cewa "gaskiya garba da kai da jamil ban san wanda yafi wani iya salon neman kudi ba,kaji fa wata dabara", murmushin bosawa Abby yayi kana ya ɗauki laptop dinsa ya fara ƴan danne danne, cikin sakanni sai gashi ya yi hadakar kira da shi da duk wani customers dinsu na nan gida da na can kasashen waje,ko wanne da fuskarsa wajen su hamsin, take Abby ya sanar da su sabon kasuwancin da suke dashi a yanzu koda ko zuciya ta yaro dan shekara goma, dan haka me so a yi ciniki yanzu tare da yin buking,take kowannensu ya fara saka farashi kamar dai yadda ake saka farashin hannun jari ko siyan Company,daga karshe dai mutum biyu sun yi nasara me koda da me zuciya sun saka farashin da babu wanda ya kuma sakawa dan haka ciniki ya fada, take su kayi rubutu da saka rabin kudi aka tsaida date din karba, kamar yadda suka saba.tafawa su kayi suna mai shiga tsananin farinciki dan bayan zuciyar innawuro da ta aminatu wannan yaron ne mafi tsadar farashi da suka samu,tabbas dole Mutanen nan su riki kasuwancinsu da muhimmanci dan ba karamin kudi suke samu ba, kai me karatu idan kaji farashin zuciya ƙwaya daya sai numfashinka ya kusa ɗaukewa, dan talaka futuk idan ya samesu to babu shi babu talauci har zuwa kan tattaba kunnensa.da wannan suka rufe zamansu na yau.

Daddyn zahida ba shi ya shigo gidan ba sai misalin ƙarfe ɗaya, dan sai da ya biya yayi sharholiyarsa da ya daina ta a baya, amma zuwan aminatu cikin rayuwarsa sai da ta tada masa da tsohon miki,duk da cewa ba wai yana samun gamsuwa ba ne,dan duk macen da zai kusanta sai ya fara aiyana aminatu a ransa tukuna yake jin dama dama,jin gidan shiru yasa ya wuce ɗakinsa kai tsaye,wanka ya yi kafin ya zura kayan baccinsa ya haye saman gadonsa yana maida numfashi,sai kuma ya kasa baccin ya fada duniyar tunanin aminatu kamar yadda ya zame masa jiki tun ranar da ya fara sata cikin idanunsa,dan acikin wannan shekaru babu ranar da baya mafarkinta,yau ma atepting din shiga dakinta ya fara yi kamar kullum sai dai Yana tsoron tijarar yarinyar shi kuma baya son yayi mu amala da mace ba acikin hayyacinta ba,har zuwa karfe biyu na dare ya kasa bacci kuma ya kasa tsaida matsaya dan da yayi kamar zai je sai kuma ya tuna wacece aminatu, daga karshe dai shi ya rinjayi zuciyar da take sagar masa da gwiwa ya zura silafas dinsa ya fice daga dakin yana aiyanawa ransa cewa babu abinda zai faru, wannan ne ya bashi kwarin gwiwar shiga dakin aminatu idanunsa rufe da son biyan buƙatar kansa.
Chapter 38 · 0% Book details