← Book details Matar Dan Birni Part 1 Complete Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 46

Sashe 29

Matar Dan Birni Part 1 Complete Novel · about 8 min read

Kamar a mafarki yaji karar zahida a cikin kunnensa, cikin nutsuwa ya buɗe idanunsa da suke cike da bacci da gajiyar hanya, sai da ya ɗan dauki sakanni a zaune yana addu'a kana a hankali ya zuro ƙafafunsa da kamar baya taka ƙasa da su ya zurasu cikin silipas ɗinsa masu taushi,kana ya miƙe tare da ɗan yin miƙa ya nufi hanyar fita, yayin da duk takun da zai yi sai yaji ihun zahida na ƙaruwa a cikin kunnensa haka ne yasa shi ƙara sauri wajen barin ɗakin.

Aminatu na jin ihun zahida ta fasa sauka ta tsaya daga bakin barendar da ya raba tsakanin dakin zahida da bangaren mus ab,da gudu Nana da innawuro suma suka fito suna tambayar lafiya suke jin kamar ihu,taɓe baki aminatu ta yi tare da basu hanya tana cewa "Nima abinda na ji kenan na fito", dai-dai lokacin mus ab ya fito daga bagarensa yana duban aminatu kafin ya kaida jallinsa kan nana da innawuro da suke hayowa upstairs ɗin,cikin muryarsa dake nuna tsantsar takurar da yake ciki akan yawan magana ya ce,Nana lafiya dai?"Nana da ta wucewa ta gefan aminatu ta ce to ni ma dai ban san abinda kefaruwa ba hawowata kenan",ihun zahida da suka kuma ji ne yasa duk suka zabura suka nufi ɗakinta, turus duk suka yi suna kallon ɗan ladi da yake ta yiwa zahida magiya cikin kuka akan ta tausaya masa ta soshi ta kaunace shi idan ba haka ba mutuwa zai yi".

Nana da mamaki ya isheta ta ce,"kai dan ladi dama baka da hankali yaushe ka fara shaye_shaye matar auren kake cewa taso ka zaka mutu?to ka mutun mana fita daga ɗakinnan ko yanzu nasa security su fiddaka", innawuro ta ce to Ni wannan wace irin masifa ce kai yanzu har ka yi tsaurin idon biyo uwar dakinka har cikin daki saboda hauka"?caraf aminatu ta yi ta ce,"aa fa innawuro ku daina ganin laifinsa ita da kanta ta jawowa kanta masifa dan haka ku rabu da ita ta je can ta ƙarata mu dai zamu sha kallon show a wagga gida", ta fada tana mai ƙyalƙyalewa da dariya,haɗa idon da su kayi da oga mus ab yasa ta haɗiye ragowar dariyarta tana faman kif_kifta manyan idanunta.

Tsare aminatu yayi da lumsassun idanunsa kafin cikin kamewarsa ya ce."me yake faruwa a nan?" Tura ƙaramin bakinta ta yi kafin cikin ƙunkuni ta ce," kawai ku lallabasa ya fita tunda ba yin kansa ba ne idan kuma kuka ce ta karfi zaku fiddashi to wallahi sai dai ku rufesu shi da ita a dakin dan ba zai taɓa fita ba", shotup tambayar ki fa nayi amma kike ce min a bar matata tare da wani ƙato a ɗaki aminatu Are U out of sense?"ba ƙaramin tsorata aminatu ta yi da tsawar mus ab ba hakan yasa ta fashe da matsanancin kuka,Nana kuwa shawarar aminatu suka bi ita da innawuro dan dukkansu sun san wacece aminatu, da kyar suka lallaba dan ladi ya tafi amma da sharaɗin zai dawo da sassafe,ta gaban mus ab yazo ya wuce, yana yi yana waigen zagida da ta yi tsuru_,tsuru har ta rame a cikin ƙanƙanin lokaci.

Nana ficewa ta yi tana hararar mus ab saboda tsawar da yayiwa aminatu akan wata banzar matarsa da bata san muhimmancinsa ba,har suka fita aminatu bata bar kuka ba har dasu sheshsheƙa kamar wadda ake yankar naman jikinta,a hankali zahida ta ƙarasa inda yake tsaye jikinta a matukar sanyaye sannan ta wani ɓangaren abinda mus ab yayiwa aminatu akanta yasa ta fara zaton ko dai ragowar kwallin yayi aiki akansa, shi yasa ta matso tare dasa hannu ta rungumeshi,tana sakin kukan munafurci,take kukan aminatu ya ƙaru sai ga aminatu na neman shiɗewa, cikin wani irin zafin nama mus ab ya hankaɗe zahida daga jikinsa yayi kan aminatu da take shirin yin kasa ya tarota zuwa jikinsa,kafin yayi wani abu tuni aminatu ta sume a jikinsa, daukarta yayi cancakaras ya fita daga ɗakin zahida kai tsaye ya nufi ɗakinsa da ita,yayin da ya bar zahida tana wani irin kukan neman ɗauki, zuciyarta kuwa kamar zata hudo ta fito, tabbas dole ta ɗauki mummunan mataki a akan aminatu, dole zata fuskanci su daddy idan ba zasu yi aikin da zasu yi akan aminatu ba to ita ta gaji da jira dan wallahi ba zata bari ta kashe ta a banza ba.

A hankali ya kwantar da ita saman lafiyayyan gadonsa, kana ya dauko ruwa a dispenser ya zuba mata kadan akan fuskarta, a hankali taja wata doguwar ajiyar zuciya tare da buɗe idanunta tana bin dakin da kallo, kafin kuma cikin sauri ta miƙe zata fice daga ɗakin zuciyarta na yi mata ƙuna da zafin da ta rasa akan meye?riƙo hannunta yayi yana cewa "common ina zaki baki bani labarin abinda yake faruwa da matata ba?"wani shaƙurarran kuka ta saki tana son fizgar hannunta da ya riƙe kam,amma ta kasa ƙarshe ma janyota yayi ya zaunar bisa cinyoyinsa yana mai kamo fuskarta dan kallon cikin idanunta, so yake kawai ya tabbatar da abinda yake zato kuma yake gani a cikin idanunnata shi yasa yake kuma tunzurata da kalaman da ya fuskanci sune damuwarta......kasa ƙwatar kanta da ta yi yasa ta yi sarunder tare da shigewa cikin jikinsa tana ci gaba da kukan da bata san dalilinsa ba,",nifa yanzu na girma nasan hukuncin taɓa jikin da ba halalina ba dan haka ki daina tumurmushewa zahida jikin mijinta" ya fada dan guntun murmushi na subcewa daga kan kyakkyawar fuskarsa......

Fyadam✍🏾

8064537048 opay Fatima yushau adam.

Yan nijer

80416252
Amanata
[4/11, 7:53 AM] yushauadamfatima: https://chat.whatsapp.com/KjZ4tAsifjTHdEEUdPWRXD

*Typing*

💕
*MATAR ƊAN BIRNI ** 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

``` *Page 22``*

Ƙananun Duka ta shiga kai masa wanda da ƙyar ya samu ya riƙe hannunta, kana a hankali ya haɗe tazarar dake tsakanin fuskarsa da tata,cikin kuka aminatu ta buɗe bakinta zata yi magana sai dai kafin ta furta abinda ke ranta, sanyi da kamshin harshen mus ab yayiwa bakinta tsinke,wani abu me kamar mayan ƙarfe ya shiga jansa duk da yadda yake son rinjayar zuciyarsa na barin aikata abinda yake aikatawar,hannunsa ya zura ta cikin rigarta yana shafa shafaffen cikinta da kamar ba a zuba masa abinci har zuwa cikin ramin cibinta,wani irin sheshsheƙa aminatu tayi tamkar zata shiɗe saboda yadda tsigar jikinta suka mimmiƙe, yawo yake da hannunsa a jikinta cikin wani irin salo me tafiya da imanin ma'aboci bege, bakinsa kuwa a hankali yake sauko dashi har zuwa wuyanta yana shaƙar sassanyan ƙamshinta da ya ke neman ruguza masa duk wani tunani yana mai goga gemunsa a duk inda ya samu,hannunsa da ya kai kan brz ɗinta yasa ta ja wani ƙaƙƙarfan numfashi tamkar zata sume duk da cewa ba wai ya taɓa fatar jikinta ba ne.cikin sauri ta zame daga jikinsa ta haye saman gadon ta dukunkune kanta tana maida numfashin tashin hankali da wani irin yanayi da ta tsinci kanta a ciki wanda ita kanta bata san na meye ba.

Shima noƙewa yayi cikin fuskewa da shanye yanayin da yake ciki ya wuce bayi,bai jima ba ya fito ya samu har ta yi bacci dan haka sai kawai ya kwanta a gefenta wanda da a baya ba haka yake yi ba,amma yau sai yaji ba zai iya nesa da ƙamshin da aminatu take yi ba,can gefe ya kwnata bayan ya tofa musu addu'a,a hankali ya lumshe idanunsa yana son ya manta da abinda ya faru yanzun, sai dai ina duk juyin da zai yi taushin fatar jikin aminatu yake ji a cijin hannunsa,haka kuma duk numfashin da zai yi tare da ƙamshinta yake maidashi, a nutse ya bude idanunsa da suka sauya launi ya watsasu kan fuskarta da ta ke ta sheƙi tana baccinta cikin nutsuwa, kallonta yake yana jin abinda yake ji yana ƙaruwa a tare dashi, kasa jurewa da yayi ne yasa shi matsawa kusa da ita tare da janyota jikinsa, cusa fuskarsa yayi a cikin wuyanta yana mai shaƙar ƙamshinta me sanyi, wanda hakan ya samu baccin da yake nema ya daukesa ba tare da ya shirya ba.

Da misalin ƙarfe biyu mus ab ya tashi aminatu,yasha mamakin ganin aminatu ta tashi ba tare da ta yi ƙunƙuni ba kamar yadda ta ke yi a baya, lafiya ƙalau tayo alwala suka fara sallah (kar ku manta a yadda aminatu take rayuwarta a yanzu bata san komai a cikin rayuwarba,bata san cewa akwai wani kalubale da yake lulluɓe a cikin duniyarta ba,bata da wata damuwa da zata sa tayi tunanin neman taimako gurin Allah ko yin addu'a dan Allah ya kareta ba,to amma duk da tasan da wannan hakan bai hanata bin tafarkin da nana da innawuro da kuma hamma mus ab dinta suka dorata ba,kar kice sai kina da damuwa ko bukata zaki nemi taimakon Allah tashin dare da yawanta addu'ar neman tsari, baki da matsala a yanzu bashi yake nufin iya kaddararki kenan ba baki da damuwa bashi yake nufin bazaki miƙa kukanki wajen Allah ba,karki manta da cewa kina da babbar damuwa damuwar da tafi kowace damuwa a duniya damuwar kuwa ita ce mutuwa, tashin alƙima, me zaki tarar, me kika aikata, wuta, aljanna,duk wannan sune babbar damuwar muminin kwarai,dan haka ba sai Allah ya jarrabeki da kalubalen rayuwa ba ne zaki fuskancesa,a'a neman lahirarki shine babban kalubalenki, wannan shine abinda magabatan aminatu suka koyar da ita suka nuna mata lallai ba sai tana da damuwar duniya ne zata tashi ta nemi lahirarta ba, wallahi mu farka duniya bata da tabbas mu nemi lahirarmu kafin lokaci ya ƙure mana, koda zaki yi sharholiyarki karki bari kimanta da Allah da kuma mutuwa domin tuna sune kadai yake dawo damu kan hanya, Allah ya shirya mu yasa mu cika da imani)
Chapter 29 · 0% Book details