Sashe 40
Matar Dan Birni Part 1 Complete Novel · about 8 min read
A harabar gidan suka hadu da hajar tana share farfajiyar wajen,kallon aminatun ta yi cikin damuwar tafiyar da zata yi dan ɗan zaman da suka yi har sun saba,"yanzu tafiya zaki yi kenan"?hajar ta tambayi aminatu cikin damuwar da ta bayyana kan saman fuskarta,kama hannunta aminatu ta yi tare da cewa ,"hajar ai yanzu tafiya ta zamar min dole tunda kakata na asibiti ba lafiya ƙarin damuwata ma shine an kaita asibitin da bana so, asibitin da na yiwa tsanar da ban san dalilinta ba,shi yasa yanzu dole can zan tafi kai tsaye ", wane asibiti ne"?hajar tayi tambayar zuciyarta cike da fargaba,jan akwatin aminatu ta yi kana cikin rashin bawa tambayar hajar din muhimmanci ta ce,"GJK hospital",da gudu hajar ta bi bayan aminatu tana cewa zan iya rakaki na duba kakar taki dan Allah idan ban takura ki ba", zuba mata ido aminatu ta yi tana kallon cikin idanunta wanda har sai da hajar ta ji tsoron hakan ya shigeta dan sai taga idanun aminatun sun yi wata kala da ban kamar ba nata ba,a hankali kuma sai taga sun koma daidai har aminatun ta buɗe baki ta ce, "babu wata damuwa na gode da kulawa", dai-dai nan suka ƙaraso tsakiyar tafkeken filin gidan da yake barazanar cinye unguwa guda,malam tanko driver su ka gani ya ƙaraso da mota gabansu tare da cewa "Hajiya ku shigo Alhaji ya ce na kaiku asibitin", wani kallon rainin hankali aminatu ta yiwa daddy da yake tsaye daga dan gefansu cikin yanayin rashin gaskiya,kafin ta ce, "bama buƙatar shiga motar jemagu, idan mun fita da sawayen mu su tare mana hanya a ja mu lungu a yi mana fy.....wata irin ƙatuwar atshawa me haɗe da tari Alhaji garba ya saki sarai aminatu ta gansa kuma idanunta akansa take yin maganarta ba tare da shakka ko tsoro ba, da sauri malam tanko ya fita daga motar ya je yana masa sannu tare da bashi ruwan robar da ya ɗauko masa a motar, karɓar ruwan yayi ya kafa kai bai sauke robar ba sai da ruwan suka ƙare tas, sannan ya dire yana maida numfashi tamkar wanda yayi tseren gudu,sosai hajar ta yi dauriyar riƙe dariyar dake cinta tana jinjina wa aminatu da mamakin halinta na rashin tsoro da rashin barin ko ta kwana,jan hannunta da aminatun ta yi shi ya dawo da ita hankalinta, fita suka yi daga gidan sai da suka yi tafiya me ɗan nisa sannan suka samu adedeta sahu suka hau.
Aminatu bata taɓa tunanin haka jikin innawuro yayi ba, dan lokacin da suka ƙarasa asibitin har an fito da ita za a shiga da ita dakin tiyata, riƙe gadon aminatu ta yi tana wani irin kukan da tunda tayi wayo bata taɓa yinsa ba,saboda innawuro ita ce komai nata bata san kowa ba sai ita shi yasa bata son ko ciwo innawuro ta ji ajikinta, cikin kuka take cewa "yanzu da tafiya zaku yi da innawuro na ban ganta ba?me za kuyi mata?ina zaku kaita me ye ya sameta da har za a yi mata aiki?Nana da sauran likitocinne suke ta ƙoƙarin kamata,amma ta riƙe gadon katamau tamkar wadda ake ƙarawa ƙarfi,da karfi ta doke hannun wata likita da ta kama ƙafadarta tana cewa, "ni ku rabu da ni bana bukatar wannan asibitin ban sonsa ku bani ita na kaita wani asibitin bana so na rasa innawuro ita ka dai ce da Ni a duniya, ita ce kawai me sona",da sauri Abby ya ɗan matsa gefe tare da sa kiran mus ab, dan kuwa tabbas idan suka ƙyale aminatu ta ci gaba da wannan zantukan zata jawo musu babbar asarar da suke gudu,mus ab din Yana ɗagawa ya ce,maza mus ab ka dawo idan ka gama sa hannun dan ga amimatu nan duk ta birkice mana kowa ya kasa control ɗinta ta hana a shiga da innawuro dakin tiyata kuma hakan kan iya jawo babbar matsala",ko rufe bakinsa bai yi ba ya hango mus ab din cikin nutsuwa yana tunkarosu,sauke wayar yayi daga kunnesa yana sakin ajiyar zuciya,tare da goge gumin fuskarsa,a ransa yana cewa "wannan wace irin yarinya ce haka? Me yasa take son bamu matsala cikin rayuwarmu?me yasa muke tsoronta duk da mun san cewa babu wani abu da zata iya ko da kuwa tasan wani abu daga cikin sorrinmu?"bai da wannan amsar dan haka yayi kokarin saita kansa,a hankali cikin makewarsa ya karasa inda aminatun take ƙankame da gadon innawuro ta hana kowa taɓawa bare aja ta zuwa dakin tiyatar, dogayen hannayensa yasa ya ɗagota daga durƙusan da tayi gaban gadon tare da ɓanɓare hannunta daga jikin gadon,kafin cikin taushin muryarsa da ko wane harafi yake fita daddaya ya ce,aminaaaaaatu," da sauri ta buɗe idanunta da su kayi wani irin ja saboda kuka tana cin karo da fuskarsa kuwa ta wani irin rungumesa irin rungumar nan dake tabbatar da cewa ta samu inda za a share mata kukanta, dogayen hannayensa yasa yayi mata zobe yana mai tafa bayanta cikin wata irin lallaɓa da kulawar da duk wata mace zata so ace ita ake yiwa, goga fuskarta ta shuga yi a kirjinta tana ɗan bugunsa cikin kuka tana cewa "ƊAN BIRNI kar ka bari su tafi min da innawuro na ita kadai gareni idan na rasata bani da kowa tinda har yanzu Ban samu ƊAN BIRNI na ba bani da me kulawa dani bani da me jure shiriritata, idan na tsokano faɗa babu me tsayawa gabana na boye a bayansa dan Allah su dawo min da innawuro na kaji Ɗan BIRNI".
Duk wanda yake sauraron aminatu gurin nan sai da kalamanta suka soke shi, dan ita Nana ma kuka take yi haka hajar da sauran mutane masu taguwar zuciyar dake reception ɗin,cikin wannan halin likitocin suka samu suka janye gadon da innawuro take kai suka wuce ɗakin tiyata.
Abby dai ya samu wancan baragabar ta sake shi yanzu kuma fargabar da yake shine na kar zahida ta fito taga mus ab da aminatu a cikin wannan halin,dan muddin zahida ta gansu a haka zata iya birkice musu rasa kanta, wanda shima hakan babbar matsala ce, tunda saboda buƙatar nutsuwar ta ta ne ma har suka nesan ta ta da aminatun, wannan tunanin da yayi ne yasa shi zabura ya nufi ofishin zahidar dan ya dan dauke mata hankali har mus ab yabar wajen da AMINATU.
Har yanzu aminatu kuka take, wanda haka yasa mus ab ya yi kasa da murya dai-dai saitin kunnenta ya fara mata magana cikin lallashi, so sorry angel innawuro zata fito lafiya, ga Nana tana sonki ga suhaima da Khalid duk suna sonki ki daina cewa baki da kowa",dago kanta tayi da kan ƙirjinsa tana mai kallon idanunsa da bata iya kallar cikin su ta ce,kai baka so na?"sosai tambayar ta buge da amma dake jarumi ne ba komai zaka fuskanta daga garesa ba, sai ya ɗan furzar da hucin bakinsa kafin cikin wani irin yanayi me sanyi da lumshe kwayar idanunsa da suke tamkar na mai jin bacci ya ce,"SONSO me zurfeen da bashi da iyaka da ƘAUNA irin wadda babu irinta a duniya",shi kansa mus ab baya ce ga da ga inda kalaman nan suka fito ba shi dai kawai ya tsinci zuciyarsa da bakinsa suna rera kalaman tamkar wani waƙe,aminatu kuwa wani irin zazzaɓi ta ji yana shirin kamata saboda yadda kalaman suka shigeta shigar bazata, duk da cewa bata cikin hayyacin da zata iya fahimtar kalaman nasa dalla,jin yanayin jikinnata yasa shi duban Nana ba tare da ya ce komai ba,jinjina kai Nana tayi dan ita tuni ta gama laƙantar gane yaren kuramen dannata,shi yasa ko motsi yayi tana iya fuskantar abinda yake nufi,kamar dai yanzu da ta gane yana mata nuni da zasu tafi gida da aminatun ne dan ta samu nutsuwa,da kansa yasa ta amota sannan ya shiga yaja suka bar harabar asibitin.
A can bangaren zahida da Abby kuwa, tare ta yayi da wasu bayanan da bata wani ganesu,wanda bai kyaleta ba har sai da ya fito ya tabbatar da cewa mus ba ya tafi da aminatu,yana shirin komawa ta fito sanye cikin kayan aiki hannunta sanye da hand gloves da wata nas a gefanta rike da wasu TARKACE acikin faranti,ajiyar zuciya Abby ya sauke wadda ke nuni da fara dan samun nutsuwar da yayi tunda bayajin mutuwarsa zata kammala har sai an fito da zuciyar innawuro da ƙodarta lafiya.
Zahida na dora hannunta saman saman hadle din kofar da zata sasanta da dogon corridon da dakunan tiyatar suke a jere reras kamar dakin hotel,taji an riga ta buɗewa ta ciki ba kuma buɗewa ce da ke nuna lafiya ba,dan hatta da farantan karkace kayan operation din dake hannun nas ɗin nan sai da suka tarwatse, kasa, securities din dake gadin kofar tuni suka yi kan likitan da yayi wannan barnar dan kuwa su kullum a shirye suke cikin shrin ko a mutu ko ayi rai.
Sai da suka tabbatar likita ne sannan suka janye daga dabaibayin da suka yi masa da bindigun su hagu da dama,cikin tashin hankali Abby da ya kasa fita da ga wajen ya matso yana cewa kai lafiya me ya faru?" Zahida ma kallon Dr Salomon take cike da fusata da tambaya,cikin rawar baki da na hannu yake nuna musu hanyar dakin tiyatar ba tare da ya iya cewa komai ba,cikin tsawa zahida ta ce "dalla malam ka bude baki ka gata mana me ye yake faruwa?"dakyar Dr Salomon ya iya bude bakinsa dake matukar rawa cike da rashin hankali ya ce,babu shi babu majinyaci ya bace bamu gane sa ba", da sauri Abby ya shaƙi wuyan Salomon Yana cewa me kake nufi wane majinyacin kake fada yi mana bayani mu fahimta,?"cikin tsananin walahalar shaƙar da salonmon ya ji yake cewa Hajiya innuwurr shine baya nan ya bace", da wani irin gudu zahida da Abby Kai har ma da securities din suka bangaje Salomon suka shige dakin dan ganewa idanunsu abinda take shirin faruwa.....
Tofa wai ya haka ne?
Me ke shirin faruwa?
Da gaske innawuro aka sace?
Idan ita ce wa ye ya sace ta?
Ta yaya kuma hakan ta faru bayan duk likitocin da zasu yi aikin sun kasance a dakin?
Uhhhhhh bana cewa komai yanzu....
Fyadam ✍🏾
,8064537048
Opay Fatima yushau adam
Amount 500
[4/12, 5:49 PM] yushauadamfatima: *Typing*