← Book details Matar Dan Birni Part 1 Complete Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 46

Sashe 35

Matar Dan Birni Part 1 Complete Novel · about 8 min read

Da sauri Nana ta kama innawuro ta maida ta kan kujerar da take kai, sannan ta fara magana cikin tsananin tausayin innawuro da ganin wani irin kimarta da darajar ta da suka karu a idanunta, ta ce, innawuro dama wannan ranar nake jira ranar da zaki magntu akan abinda ke faruwa, to alhamdulillahi anzo gabar kuma naji dadi matuka da ya kasance na haɗa wata babbar alaka da ku saboda ku din mutane da kowa zai so ace ya haɗa alaka dasu idan fa har yasan me ye mutunci da karamci, innawuro ki kwantar da hankalinki kisa a ranki cewa AMINATU tana rayuwa tare da mijinta ne," da sauri innawuro ta kalli Nana kafin cikin rawar baki ta ce,a'a kar muyi haka dake AMINATU tun tana kankanuwarta ubanta ya daura mata igiyar aure wannan ita ce ƙaddarar AMINATU saboda Allah ya jarrabeta da son abinda bata taɓa gani ba abinda jinsa kawai tayi a bakin baffanta, wanda tun daga nan sunan MATAR ƊAN BIRNI ya bita kuma shine silar shigowarmu birni dan kwai mu nemesa, har zuwa yau aminatu bata manta da dan birnin da bata sanshi ba yana nan a ranta duk da cewa yanzu bata yawan yi min maganar nemosa kamar yadda take yi a baya", murmushi Nana saki kana tajefowa innawuro tambayar da ta dan jefa ta Cikin dogon tunani,shin kin san dalilin da yasa ta daina tambayar wancan dan birnin ta kuma daina shiga damuwa a duk lokacin da ta tuna shi?Nana bata saurari amsar innawuro ba tunda tasan bata da amsar ta ɗora da cewa,saboda ta sameshi ne, yana kusa da ita idanun ta ne basu sanshi ba amma zuciyarta ta sanshi kuruciya ce ta hanata ganoshi amma da sannu zata ganesa da kanga ba tare da wami ya nuna mata shi ba, innawuro ina mainsanar dake cewa shi wancan dan birnin da kuka bawa auren aminati sabida yadda da kauna wadda bata da iyaka SHINE MUS'AB dina yaro daya tamkar da dubu, yadda da amincin da danki yayi hasashe a tare da shi ina mai tabbatar Miki da cewa dan ki dan baiwame kamar yadda jikar ki ta zama yar baiwa dan kuwa hasshensa daidai yake ya bada AMINATU a hannun da ya dace, ko ke baki ga haka ba?".

Wata irin ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya innawuro ta sauke kafin ta ce," bani wata shaida da zai tabbatar min da abinda kika faɗa ", murmushi Nana tayi kana ba tare da bata lokaci ba ta bawa innawuro labarin abinda tasan cewa babu wanda ya sani daga ita sai baffan AMINATU da kuma uban gayya dan birni mijin AMINATU,a take innawuro ta yi sujud shukur har da kukanta,anan Nana ta kuma sanar da ita dalilin da yasa baizo nemansu ba da kuma niyar neman a daidai ganar da Allah ya sauƙaƙe masa wahala ya kawosu har inda yake ta wani sanadi daban da su dukansu basu sanshi ba.

Hankalin innawuro kwance ta koma dakinta ta yi alwala ta fara sallolin nafila dan godewa Ubangiji me iko da aiwatarwa a duk sanda yaso.

*******

Kuka AMINATU tasa saboda ta kasa ƙwatar kanta ji take kamar zai cire mata fatar baki,ga hannunsa da yake ta kokarin kaiwa ga inda take ganin idan ta bari ya taba shi ke nan ta gama taɓewa babu ita babu samun Rahma,kukan da ta saka me ƙarfi shi ya dakatar dashi daga abinda yake yi, zame bakinsa yayi daga nata, ba tare da ya kula da kukan da take ta masa ba ya kama hannunta ya gasa mata,yana ji tana ta maganganunta da ba wani fahimtarsu yake ba,da haka ya gama ya naɗota cikin towel kamar wata jaririya ya kaita har saman gadon, sannan ya kawo kayan bacci masu taushi ya saka mata, wanda dakyar ta bari ya saka matan dan turasa ta dinga yi tana kare ƙirjinta da bata san cewa ya fi ta son kiyaye kallon wannan guraren ba,bai barta ta yi bacci ba sai da ya tabbatar ta sha furar da ya ɗauko mata dan yasan da yunwa a tare da ita, ita kuma ba wani jure yunwa take yi ba, dan kuwa kafin kaga abinda zai hana aminatu cin abinci zaka jima.

Tun daga wannan ranar innawuro ta samu nutsuwa,sai dai ta bangaren zahida da Abby babu wannan nutsuwar Allah Allah suke aminatu ta warke su tattarata ta koma gidan daddyn zahidan kamar yadda suka tsara,sun san cewa ko ma meye aminatu ta sani game dasu basu nada wani amfani tunda gaba daya rayuwarta su suke juyata bata da wani karfi ko wayan yin wani abu akan duk ma me ta sani ɗin wannan tunanin yasa suka watsar da shakkun da suke da fargabarsu akan aminatun.

Ta bangaren aminatu kuwa tun daga wannan ranar bata kuma bari ta kusanci inda mus ab yake ba,saboda ita kanta duk da rashin hankalin ta tasan cewa abinda yake faruwa tsakaninsu haramunne, dan haka ta dauki damarar yin yaki da zuciyarta,a haka har ta samu sauki tayi garau da ita,wanda dama burin Abby da zahida kenan.

Yau suna gama karyawa ,Abby ya umarci Nana da ta kira innawuro yana so zasu yi magana da ita,Nana ba ta kawo komai a ranta ba ta kira innawuro, ko da innawuro ta zo shi ya fara gaidata kamar yadda ya saba a duk sanda suka haɗu wannan halayyar tasa tana daya da daga cikin abinda ya kuma siya masa girma da yarda a wajen innawuro, dan gyaran murya ya yi kafin cikin nutsuwa ya fuskanci innawuro ya fara da cewa, "innawuro wata alfarma nake nema a wajenki ina kuma fatan zan samu?"ya karasa maganar ta sigar tambaya idanunsa kuma akan innawuro,cikin nuna girman da yake dashi a gunta ta ce,"in sha Allah in dai har bata fi ƙarfina ba zan iya yi maka", jinjina kai yayi cike da gansuwa kana ya ɗora da cewa, so nake ki amince aminatu ta koma gidan daddyn zahida wajen mahaifiyar zahida kenan, na dan wani lokaci ne kawai zata dawo nan daga baya", kamar ya ban fajimceka ba akan me aminatu zata koma gidansu zahida? a wane dalilin?"Nana ta faɗa cike da nuna rashin yarda da kuma mamakin bijurowar wannan sabon al'amarin lokaci ɗaya?"ɗaga mata hannu Abby yayi fuskarsa a haɗe tare da cewa "babu ruwanki ba da ke nake magana ba kuma ba umarninki nake nema ba,"dubansa ya maida kan innawuro yana cewa innawuro wannan ce alfarmar da nake nema a wajenki ina har zan samu",gaba ɗayansu innawuro suka zubawa ido har aminatun da tunda suka fara magana take bin bakunansu da ido kamar wadda ta tashi a makanta,a hankali innawuro ta sunkuyar da kanta ƙasa kana cikin ladabi irin na hadimi ga ubangidansa ta ce,"Ni yanzu bani da iko da aminatu dan haka ka yi magana da wanda yake iko da ita idan har ya amince Nima na amince".

"Waye me iko da AMINATU a gidan nan sama da ni da na kawo ku gidan?"Abby ya tambaya idanunsa akan innawuro yana jiran jin amsarta,kafin wani daga cikinsu ya ƙara yunƙurin yin magana,dakakkiyar muryarsa me cike da ginshira da wani salo na musamman ta karaɗe kunnuwansu, "Abby nine nake da iko da AMINATU dan haka sai da izinina za a zartar da hukunci a kanta",cike da wani irin mamaki Abby yake kallon MUS'AB da yake neman wajen zama fuskar nan babu annuri ko kaɗan,da ƙyar Abby ya iya haɗiye kakkauran miyan da ya tokare maƙoshinsa kana ya iya cewa,"mus ab me ye haɗinka da aminatu da har ikon ta zai koma hannunka?"nana ta ce,"ni a ganina shine magajin gidan kuma tun ranar da ka kawo aminatu gidan nan ka saki hannunta mus ab ya kama dan haka dole shine me iko da ita",wani mugun kallo ya watsa mata kafin cikin tsananin fusata ya ce," Nana ni kike faɗawa wannan maganar? to bari ki ji na gaya miki ko kun so ko kun ƙi sai na yi iko da AMINATU tunda shima me ikon da ita nine ubansa me iko da shi idan kuma ban isa ba ku fada min?" Shiru suka yi babu wanda ya tanka masa, juyawa yayi ya fuskanci aminatu tare da cewa aminatu kin amince zaki je inda na buƙaci kije?"kai tsaye ta ɗaga kanta kana ta amsa masa da cewa "zanje",yauwa yar albarka"Abby ya faɗa fuskarsa cike da fara,a,da sauri ta kawar da kanta dan kaucewa mugun kallon da mus ab yake auna mata, duk da cewa koda bata kallesa ba tana jin kaifin idanun nasa a jikinta,a ranta tana jin cewa mafita ce Allah ya kawo mata ta kaucewa daga saɓcon Allah,to amma can ɗin ma ai baki tsira ba,kai tsaye ta bawa zuciyar da take mata wannan tambayar amsa da cewa, shi wancan tsohon najadun zan iya dakatar dashi koda ace bai sauya ba, shi kuma wannan bana iya sarrafa kaina a duk lokacin da ya kusanceni dan haka can ɗin yafi min, zanje na ɗan lokaci tun da ba zama zan yi na har abada ba, wannan tunanin da ta yi tun fara muhawarar tasu ne yasa da Abby ya tambayeta ta amince ba tare da wani ja in ja ba.

Tana jin karfin takunsa lokacin da ya mike ya nufi upstairs,ta kasan idanunta take kallon ƙafafunsa da yake takasu akan mables din falon a haka kamar ba takun yake yi ba, amma kuma duk takun da yayi sai kaji sautinsa har cikin ranka,da haka ta daina hango shi, Muryar Abby ta ji yana cewa tashi kije ki shiya kizo mu tafi",sai da aminatu ta bar falon sannan ya dawo da dubansa kan innawuro cikin rarrashi da son kwantar mata da hankali ya ce,"innawuro aminatu ba nisa za tai da ke ba,tunda duk a cikin Layin nan muke,nisan mu da gidan Alhaji Garba bashi da yawa dan haka duk sanda kika so ganin AMINATU zaki ganta,"jikin innawuro a sanyaye ta amsa kana ta mike ta bi bayan aminatu.

Saboda takaici Nana barin wajen ta yi zuciyarta cike da wasi_wasi da zargi akan wannan sabon al'amarin,zuciyarta babu abinda ta raya illa cewa yayi haka ne kawai saboda farin cikin zahida, tunda yanzu duk wanda yake tare da su yasan abinda zahida ta ƙi jini a rayuwarta aminatu ce,shi yasa ranta ya ɓaci matuka da irin wannan hukunci.
Chapter 35 · 0% Book details